Hausa Novels and Stories

The Virgin Maid 1

Sponsored links

(A.B.U teaching Hospital) .

 

Cike da Azama Nurse Hamdiyya ta fito daga Ɗakin labour ɗin tana nufar Office ɗin ta ,fuskar ta fal cike da annuri bata ko ganin gaban ta saboda tsaban farin ciki . Tsayawa nayi ina ƙare mawa farfajiyar Wannan babban asibitin kallo , wanda duk da kasancewar Dare ne ,Amma haske ta ko ina kaman Safiya ko hantsi saboda Solar dake haske ko ina na wannan Asibiti . Muryar Nurse Hamdiyya naji daga baya na , wanda jin hakan ya sani Saurin juyawa ina mai ƙare mata kallo , wayar hannun ta ta kara a kunnen ta cike da matsanancin Farin ciki ta ke faɗin ” Congratulations Alhaji Abdullah , Madam ta sauka cikin ƙoshin lafiya an samu ɗiya mace “. Eh yanzu haka tana ɗakin hutawa ita da babyn ta . To sai kun iso”. Katse kirar tayi tana nufar Ɗakin da Mai haihuwar take ,wanda ko ba’a faɗa maka ba da’alama matar wani babba ne a ƙasar nan tamu ko daga yanayin yanda aka keɓence ta a ɗaki ita ɗaya ba hayaniya , Sauke Ajiyar zuciya Nurse Hamdiyya Tayi ganin Hajiya Salma Har ta samu barci , Alhmdllh Allah ya cika maku burin ku , tsawon shekaru Ashirin da Auren ku baku taɓa samun ƙaruwa ba sai a wannan shekara , hannun ta Nurse takai zuwa inda Jaririyar ke ƙwance , gaban ta ne ya buga dammm jin Jaririyar bata numfashi , sakin Wayar hannun ta tayi nan take ta ratsatstsake a saman tiles .

 

Ba tare da ta tsaya bi takan Wayar nata ba tasa hannun ta tana girgiza Jaririyar , Hawaye ne ya fara bin kuncin ta , Innalilahi wa’inna ilaihir rajiun shine Kalmar da take maimatawa . Maida Jaririyar tayi ta aje tana ɗurƙusawa tare da ɗaukar Wayar ta da yayi part part a ƙasa . Ganin babu yanda za’a yi tayi kira dashi yasa Ta saurin Fitowa tana nufo ƙasan Down Stairs .

 

 

 

 

 

Eh ta sauka lafiya yanzu mun samu ɗiya mace”. Taji Muryar Wani daga wurin yana faɗa . Cikin sauri ta ƙarisa ga mutumin jikin ta na Rawa haka idanun ta na xubda ƙwallah ta kalle shi tana cewa ” Yallaɓai don Allah ka taimaka mun da Wayar ka nayi kirar Ujila yanzu ya kamani . A fusace ya juyo yana bin Nurse Hamdiyya da wani irin kallo , Itama kallo Ɗaya tayi masa ta gane irin masifaffun matsiyatan talakawan nan ne ,marasa mutunci su burin su su tijara mai arziƙi wanda Allah ya rufa masa.

Cike da Tsawa na talauci da ya ishe sa yace ” Ke bari na gama sanar da ƙauye cewa mata na ta haihu ko , idan zasu taho ko buhun Masara aka kawo mun ai na rage zafin talauci a wannan marran.

 

 

 

 

 

Kallon Sa Nurse Hamdiyya Tayi cike da Muryar shiga tashin hankali tace ” Ka taimaka mun Yallaɓai , Matar Alh Abdullah Shuwa ne ta haihu yanzu , kuma suna tare fiye da shakaru Ashirin da Aure basu taɓa haihuwa ba sai a wannan karon , bayan na sanar masu ne cewa ta haihu na koma duba Jaririyar na tadda bata motsi Yallaɓai ,ina cikin tashin hankali kome ya faru Ni zasu zarga kuma na sanar masu cewar Komai suna lafiya Madam Hajiya Salma da kuma babyn ta ,yanzu haka sun ce suna hanya ka taimaka mun yallaɓai na sanar dasu kamin su ƙariso .

Jikin Malam Kadarko ne yayi sanyi , a hankali ya miƙa mata Wayar tasa kirar Nokia rakani toilet , ko murfi bayan ta babu ,gashi Kirawo su ki sanar dasu . Yayi maganan yana bata Wayar hannun nasa ,wanda cikin sauri ta amsa tana fara latsa nombibin Wannan Attajirin mahaukacin mai arziƙi Wato Alh Abdullahi Shuwa . Ji tayi Malam Kadarko ya buge hannun ta yana cewa ” Ina zuwa dakata . Gimtse kirar tayi tana kallon sa . Cikin wani irin yanayi tamkar na salihan mutane yace ” Wannan wanda kike maganan sa , Mai gida na ne Alh Abdullahi Shuwa , shekara ta Goma sha biyar kenan ina aiki a ƙarƙashin sa ,duk Bama Flower ruwa nake yi , Amma ya gama mun komai a rayuwa . Mutumi ne Adali , ina cikin gidan Ƙannin sa ya ba matar sa Ƙyautar ɗan sa na fari cikin sa ,halak har Abada . Wanda yanzu da faruwan Hakan Shekaru sha biyu kenan ,ba kowa Ni yaro bane face Wato Umar Farouk.

Babu ta hanyar da zan saka masu da ya wuce nima na sadaukar da tawa farin cikin , Wannan Jaririyar dana Haifa a ɗauka a basu .

 

 

 

 

 

Cikin sauri ta kalle shi tare da cewa ” Ban gane ba yallaɓai . Jirani ina zuwa . Yana maganan ya juya tare da nufar ɗakin da matar sa take , Barci ya same ta take Yi ,wannan ya bashi damar ɗaukar jaririyar yana yo Waje da ita . Nurse Hamdiyya ya tarar da ita a inda ya barta . Taho muje a musanya mata da Ƴata ,Ni na ɗauki matacciyar mu saka mata rayayyar. Yallaɓai babu matsala kuwa??. Mai rai fa zamu basu , mu tafi babu komai . Cikin sauri Suka shiga Ɗakin Da Madam Salma take har a wannan lokacin bata farko daga barcin nata ba . A hankali Nurse Hamdiyya Tasa hannun ta tana ɗago da Matacciyar Jaririyar ,shi kuma Malam Kadarko yana saka Tasa Rayayyar Jaririyar . Cikin Azama suka fito a tare ,suna saukowa ne daga Down Stairs ne ruwan sama ya kece ana sakin wani irin tsawa nan take Jaririyar Hannun Nurse Hamdiyya ta fara tsala ihu…

Laa alhmdllh Yallaɓai Jaririyar tasu ba mutuwa tayi ba tana kuka jiba yallaɓai.! Cewan Nurse Hamdiyya tana murmushi na farin ciki , Shiru Kadarko yayi yana ƙin mata magana . Wannan yasa Ta cewa ” Yallaɓai muje a mai da masu da ƴar su ,sai ka ɗauki taka Jaririyar .

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button