Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 58

Sponsored links

Duk yanda yaso dai-daita kansa hakan ya gagara. Tabbas ya yarda SO wani abune mai matuƙar kaifi. Duk yanda kaso ɓoyeshi da ƙin son bayyanashi hakan gagara yake. Duk matsayinka, duk girman shekarunka, sai ya kaika ƙasa. Shi shaida ne akan hakan, tunda gashi yana gani akan kansa. Gaba ɗaya idan yana a gaban mitsitsiyar yarinyar nan manta shi ɗin wanene ya ke da matsayinsa. Ya rasa wannan abu haka mai kama da kamar wata almara. A gurguje ya canja shiga da ɗaura alwala ya fita masallaci. Ya wani tsume kamar bashi ba, dan a Shahan-shan ɗin sa ya fita mai tsananin ƙasaita da izzar nan ga miskilancin tsiya.

 

Bayan idar da salla bai shigo ba ya zarce fada, umarnin isar da saƙon tattaro masa wasu a cikin manyan masarautar ya bada. Cikin ƙanƙanin lokaci duk wanda sunansa ya fito a zaman saƙo ya riskesa. Kafin cikar wasu mintuna duk sun hallara. Duk da kasancewar yana a cikin fadar a wani matsakaicin falonsa yake zaune ba cikin ainahin fada inda karagar mulki take ba. Da ga shi sai amintaccen hadiminsa na amana da ako ina ka gansa shima zaka ganshi, idan ka cire ɗakin barcinsa kawai. Suma ɗin yana shiga kai abinda ake buƙata da kuma gyarawa.

 

A zahiri zaka ɗauka hankalinsa kan television ɗin da ke aiki a falon suke, dan manyan kaifafan idanunsa na kanta ne. A gabansa ƙyaƙyƙyawar butar shayi ce irin ta hamshaƙan sarakai kalar golden mai tsananin ɗaukar idon mai kallo. Dan har wasu irin fararen stones aka jera jikinta da ya sake ƙayatar da ita. Sai dai hankalin nasa sam ba’a nan ɗin yake ba. Gaba ɗaya a tunanin zantukan Iffah ne na ɗazu. Dan shauƙin da yake ciki bawai ya mantar da shi bane ba. Ya dai tattarasu ne ya ajiye gefe domin basu nasu lokaci.

Sallama Sayeed Fayzul-haq ta saka amintaccen Ghazi ɗinsa da ke gefensa tsaye ko gajiya bayayi amsawa. Sai kuma ya nufi ƙofar domin duba wanene. Shi dai bai motsa a yanda yake ba, kai kace ma bai san abinda ake ba. Minti ɗaya da wasu sakanni amintaccen nasa ya dawo, a gabansa ya zube murya cike da tsantsar girmamawa yace, “Kariyar UBANGIJI ta cigaba da kasancewa zagaye da adalin shugabanmu. Sayeed Fayzul-haq ne ke isar da saƙon kammalawar kasancewar kowa”.

 

Shiru babu alamar zai tanka har kusan mintuna biyu, sai ka rantse baima jisa ba. Sai da ya mula dan kansa ya motsa lips da ƙyar. “Zasu iya shigowa”.

“Umarninka shine abin jiran kowa”.

Hadimin ya faɗa yana rissinar da kai sannan ya miƙe da sauri. Cikin abinda bai fi minti uku ba dattijai masu cikakkiyar kamala da nutsuwa suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya a nutse. Duk wanda ya shigo sai ya miƙa gaisuwa kafin ya wuce ya zauna. Sayeed Fayzul-haq ne ƙarshe hannunsa ɗauke da ledar da aka zuba kayan surkullen nan. A gaban Tajwar Eshaan ɗin ya kai ya ajiye yana ɗan matsar da ƙyaƙyƙywar butar shayin nan kaɗan. Leda ɗin ya buɗe sannan ya ja da baya shima ya zauna.

Yanzun ma sharewa yay tsahon wasu mintuna kamar bashine yasa a tarasu ba, kowa kuwa a cikinsu ya zubama ledar ido musamman Miran Arshaan da jikinsa har tsuma yake, sai dai yana ta faman taushe kansa. Tajwar Eshaan da ke nazartar kowa ta ƙasan ido ya motsa lips ɗinsa da ƙyar yana mai buɗe idanunsa masu saka mara gaskiya tsuma tar-tar a kansu da ƙyau.

 

 

“Bana bukatar sanin wanda ya ajiye su balle dalilin ajiye sun. Sai dai zan gargaɗi mai ajiyewar da abu uku. Eshaan a koda yaushe yana zagaye ne a cikin kariyar UBANGIJINSA insha ALLAHU. A komai na ina amfani da zuciya ne fiye da ƙwanji na da ƙwaƙwalwa. A kuma duk sanda maƙiyi ya sokeni ta baya sunansa matsoraci a wajena, jarumi gaba-da-gaba yake zuwa filin daga in har ya cika sunansa jarumi. Saboda haka, idan har ya shirya na bashi tabbaci ɗan Haysam bin Abdul-majeed Aliy Qutb a shirye yake shima”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button