Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 114

Sponsored links

Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa ƙarfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na kuma ƙoƙarin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima Miran Arshaan ɗin ya karɓa masa a nasa zafin.

Shiru Miran Jasim yayi da dafe kansa yana murza goshinsa dan ya tuna tabbas anyi hakan. Amma wannan aikin na cikin gida da rashin sanin mi Tajwar Eshaan ke ciki ya ɗauke hankalinsa bai nutsu yayi nazari kan batunba kasancewar akwai abubuwa da yawa da bawai yana buɗema Miran Arshaan ɗin bane, kamar yanda shima Miran Arshaan ɗin ba komai yake yarda ya buɗe ma Miran Jasim ɗin ba. Sai dai a yanzu dukansu sun fahimci yin kuskure, dan haka kowanne ya ajiye ɓoyayyar manufarsa suka fuskanci juna.

“Ni ina ganin in har an yarda da aikin Barrister ɗin nan shawararsa ba abar yardawa bace. Sannan dole ne fa mu gaggauta ganawa da yarinyar can in ba hakaba aikinmu zai iya buɗewa. Dan idan ya kasance Barrister Aas na raye bazai samu ɗaki bane ya kulle kansa domin hutu kaima ka sani”.

Miran Jasim ya gyaɗa kai da faɗin, “Hakane maganarka na kan gaskiya. Yanzu minene abinyi?”.

“Abinyi ɗaya ne bama Barrister Akeem damar shigewa gaba kafin kwana biyun nan na cikar aikinmu abar ƙasar nan da mutanen. Bayan ka haye karagar mulki shi kuma shegen duk inda yake zamu nemishi ne ya ɗan-ɗana kuɗarsa”.

“Ina sake godema ALLAH da kasancewar ka kusa da ni, dan kana farkar da ni a duk sanda kaina ya shiga duhuwa ɗan uwana”.

Murmushi Miran Arshaan ya saki a zahiri, a zuciya kam faɗi yake, (Banza ka gama cusamin ƙayar a rumbu na rufeta da ɗan boto ina daga kwance).

Ɗaukar wayar Miran Jasim dai-dai da kammala wayar Iffah da Daneen Ammarah daga can

Tana ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, kamar zata share dan bata san number ɗin ba sai kuma dai ta ɗauka da tunanin ko Sir Ajmaal ne kasancewar a saƙonta na ƙarshe ta roƙesa idan ya gani ya kirata. Daga can aka amsa sallamarta kai tsaye, hakan ya sata Ciro wayar a kunenta ta kalla tamkar mai son gano muryar. Miran Jasim da kamar yana ganinta yay gyaran murya, hakan ya sata sake maida wayar.

“Kina magana da Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy”.

Kai tsaye Iffah ta ganesa, dan haka ta fara gaidashi da girmamawa. Hakan ya masa daɗi, dan yanda yake amsa mata da kulawa zai baka tabbaci. Shiru ne ya ɗan biyo bayan gaisuwar, kafin ya katsesa da faɗin, “Ibnati inata zaman jiran ji daga gareki amma shiru. Ko baki amince da abinda kika gani bane ba dai?”.

Iffah da ke jin an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi hawaye suka shiga rige-rigen sakko mata. Hannu tasa ta sharesu da ɗan jan hanci. “Ba yarda ne banyiba ranka ya daɗe, kawai dai zuciyata na kaikawo ne na son sanin dalilinka na yin hakan a gareni. Idan ban manta ba kai fa Ammi ne garesa, mizaisa ka zaɓeni sama da shi? A barshi ma zaka iya hakan kasancewar ka mai gaskiya ko ƙyamar abinda yake. Amma miyasa su na baya da aka rasa bakuyi wani yunƙuri ba sai ni a kaina bayan akwai ƴaƴan Tajwar mafi rinjaye a cikin wanda ya halaka?”.

(Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan tura miki lokaci da adireshi mu haɗu zai fi”.

Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa cikin gyaɗa kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button