Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 19

Sponsored links

Sake maida idanun nasa da ya ɗan kauda daga kanta yayi, sai dai yanzu a kan kofin shayin da take faman damƙa ya sauke su, ya ɗanyi sama da su zuwa ƙirjinta da girman rigar asibitin ta sakaya, sake sama yay zuwa kan fuskarta da ke nuna ainahin yanayinta. Lumshesu yay da sake buɗewa cikin salon shanyesu matuƙa mai son nuna kasala a bayyane, sai dai tsaf ya shanye komai daga kan fuskarsa ya haɗiyema ransa yana mai furzar da iska kaɗan tare da gyaran muryar da ta sakata zabura alamar hakan yazo mata a bazata. Dubansa ya maida ga Daneen Ammarah da itama gyaran muryar tasa ya sakata ɗagawa kamar su doctor, sai dai maimakon shi bakinsa ya ce wani abu sai Sayeed Fayzul-haq ne yay saurin faɗin, “Ranki ya daɗe, adalin shugaba mai musanya sharri da alkairi na miƙo gaisuwar yaya jiki ga Zawjata-almilk. ALLAH ya ƙara mata lafiya da rayuwa mai albarka.”

Daneen Ammarah ta ɗan nisa kaɗan da jinjina kanta tana mai gyara tsaiwa. “Zawjata-almilk na godiya da wannan karamci, tana mai fatan alkairi da addu’ar samun lafiya ga Shahan-shan shima”.

Iffah da ke saurarensu cikin tsinkewar zuciya ta ɗan ɗago ido kaɗan da niyyar duban sa dan rashin gamsuwa da zancen Sayeed Fayzul-haq a maimakonsa, tasan bazai barta ba, dolene ta samu hukunci dai-dai da laifinta. Sake tsinkewa zuciyarta tai sakamakon shigar idanunta cikin nasa da ke mata kallon ƙasa-ƙasa da ta gagara iya bashi fassara, sai kawai taji jikinta ya fara ƙyarma. Bata san ta ya ba, bata san ya akai ba taji an riƙe kofin shayin hanunta da ke faman tangal-tangal zai kife a jikinta. A raunane, a kuma birkice ta sake ɗago manyan idanunta da ciwo ya sakasu raunana haɗe da kumburowa. Damar sarƙesu ya sake samu cikin shanyayyun nasa masu kaifi, sai kawai ta saki kuka, kuka irin wanda ta jima da son tayi, kuka irin wanda take buƙatar mai lallashi, kuka irin mai nuna tsananin bukatuwar ɗumin mahaifa ko shaƙiƙan ƴan uwa da zasu rungumeka su lallasheka. Cigaba yay da kallonta kawai shima zafin shayin na ratsa masa hannun da har ya fara gumi ga raɗaɗi na shigarsa. Baya son ji dan yana matuƙar sukarsa, sai dai bazai hanata ba dan yafi son tayisa har iya iyawar jin ta gamsu a karan kanta. Takoyi ɗin fiye ma da yanda yake buƙata, dan sai da ta kai har ya fara cije lips ɗinsa a tsakkiyar haƙora. Sai dai ƙasaita, izza da tsananin miskilanci mai samun jagorancin gudanar jinin mulki da ke tare da shi ya hanashi cewa da ita komai, koman da koda kuwa abinda ya shafi laifinta ne harta fara jan numfashi a suƙe mai alamar ƙoƙarin haɗiyewa……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button