Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Page 1

Abban Sojoji Page 1

Sponsored links

Hannu tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da jin masifar da Buzun maigadin yake ta surfa mata, “Ke wannan idan mayya ce kika kama mutun wallahi sai an yi da kyar za a samu magani.”

 

“Na she miki hajiya ba ta nan kullum sai kin zo, ba ki da zuciya ne kare ya lashe ko? Yarinya karama da ke sai taurin kan tsiya, da wasu kwala-kwalan idonki kamar na kwarton mazuru, kina kallon mutane da su ba kunya ko? Kai ga d’an iska!”

 

Dagowa ta yi a hankali tana kallon sa jin cin mutuncin da yake yi mata , idonta ne suka ciko taf da kwalla, kananun labbanta suka soma kyarma, tuni yanayin fuskarta ya canza.

 

Duk a tunaninsa yarinyar za ta mayar masa da martani saboda ya san yaran zamanin nan ba ka taba su su yi maka shiru, zuba mata ido ya yi kuri yana kallon ta. Gani ya yi tana ja da baya a tunaninsa tafiya za ta yi tabar wurin amma sai ta samu wuri a jikin bangon gidan ta tsugunna tare da kifa kanta a saman guiwowinta sannan ta soma rera kuka mai tsuma zuciya.

 

Tsayawa ya yi yana kallon ta, da alamun nadama a tattare da shi, har cikin zuciyarsa yake jin bai kyauta mata ba, yana Musulmi da shi ya gaza fahimtar yar karamar yarinyar da ke zarya kullum a bakin gate din gidan, bai taba tambayar kansa dalilin da yasa yarinyar take zuwa wurin ba. Ba irin korar karen da bai yi mata ba amma hakan bai sa gobe taki dawowa ba.

 

Jiki a sanyaye ya matsa inda take ya tsugunna a gabanta ya ce, “Kai kukan ya isa haka! Dago ka gaya mini mene ke damun ka me yasa kake zuwa kullum kana neman hajiya?”

 

Dagowa ta yi fuskar nan ta yi jaga-jaga da hawaye ga majina cikin shesshekar kuka ta ce, “Ina zuwa neman hajiya ne saboda na ji an ce tana taimakon ‘yammata ta sama masu aikatau ana biyan su kudi.”

Jim ya yi yana kallon ta kafin ya ce, “Kai ko mai yasa kake neman aiki karamin yaro da kai gidanku ba manya ne?”

 

Girgiza kai ta yi, “A’a babu kowa, ba mu da kowa, ni da ‘yan uwana ne kuma ba su da lafiya an kwantar da su a asibiti, kuna likita ya ce aiki za a yi musu, ba ni da kudin aikin saboda suna dayawa, shi ne nake so na samu aikin da zan yi ina samun kudin da zan tara a ayi musu aiki kada su mutu su bar ni ni kadai!” Karasa maganar ta yi tare da mayar da kanta kasa tana kuka.

 

Yanzu ya gane dalilin da yasa yarinyar ta nace sai taga hajiyar, a cikin zuciyarsa ya ce, “Baiwar Allah tana shikin damuwa karama da ita. Oh amma yana da tunani mai kyau!”

 

Riko hannunta ya yi tare da cewa, “Share hawayen ya isa haka, zan taimaka maka ka ga Hajiya, taso mu je ka zauna saman benchi ka ji.”

 

Mike wa ta yi ta bisa, a tare suka zauna saman bencin, jim suka yi na d’an wani lokaci kafin ya ce, “Ka yi shiru kaji ka daina kuka Allah shi ne gatan bawanSa ko mutun bai da kowa indai ya yi imani da Allah shi ne zai zama gatansa, ka shi gaba da addu’a ‘yan uwanka za su samu sauki har ku yi wasa da su.”

 

Murmushi ta yi saboda ta ji dadin maganarsa, hannu ya kai ya dauko ruwan bunun da yake dafawa a saman ‘yar butarsa, dama akwai karamin kofi guda biyu da yake amfani da su wurin zuba shayin.

 

Lekensa ta dinga yi tana kallon ‘yar butar karfen da yake dafa shayin da ita, ta burge ta musamman abin da ke cikinta. Kofin ya dauko ya tsiyaya mata a ciki, mika mata ya yi. Hannu biyu ta sa ta karba don rabon ta da ta ci wani abu a cikin ta tun jiya. Sannan shi ma ya zuba wa kansa a d’ayan kofin yana kurba yana ba ta labarin gizo da koki.

 

Sam ba ta gane me yake cewa, d’an ruwan bunun da ya ba ta ya dauke mata hankali saboda dadinsa musamman daya sanya sugar a ciki, a hankali take kurbarsa, kusan so uku tana shanyewa yana kara mata, a karshe ya ce “Aradun Allah shegen ci ne da kai ga shi harka shanye mini ruwan bununa, idan hajiya ta samo maka aiki ka fara yi sai ka biya kudin shayina.”

 

Murmushi ta saki tana sauraron shi tana mamakin yadda yake suffanta ta da namiji, ga shi shi dai ba makaho ba sarai ya gan ta da kayan mata a jikinta.

har marece ya yi hajiya ba ta dawo ba, da lokacin sallar Azahar ya yi da kansa ya bude musu kofar dake a jikin gate din suka shiga. Ruwa ya debo musu a buta, suka yi alwala tare sannan ya shimfida musu tabarma, shi ya ja su sallar yana gaba tana daga bayansa.

 

Bayan sun gama , suka ci gaba da zama a saman sallayar yana jan cazbi a hannunsa ita kuma ta shiga tunanin duniya, a haka har La’asar ta yi suka sake kabbara sallar, tun kafin su sallame yake jin karar motar hajiya alamar ta iso.

 

 

 

Dadi har cikin ranta yau dai Allah ya yi za ta gana da hajiyar nan, yana sallame sallar da sauri ya tashi ya bude mata kofa, ta shigo da dankareriyar motarta, wucewa ta yi da motar zuwa wajen ajiya. Zuge kofar ya yi sannan ya bi motar hajiyar a baya yana mata kirari kamar yadda ya saba.

 

Farinciki ya sa ta kasa rufe bakinta sai faman murmushi take yi, ba ta tashi daga samman sallayar ba, zama ta yi tana jiran maigadin ya yi wa hajiyar maganarta. Bude mata motar ya yi ta fito, ma sha Allah irin matan nan ne masu jiki ‘yar dumurmur da ita, ta ji hutu fara ce tas amma da alama tana karawa da man bleaching, jikinta na sanye da tsadadden leshi shudi wanda aka yiwa ado da stones, ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta kashe daurin kallabinta, hannunta na sanye da diamond rings, haka sarkar wuyanta ta diamond ce, kwalliya ce sama-sama a fuskarta tana da dara-daran idanu ga hanci dogo, tubarkalla, sai jan-baki da ta shafa ja ne

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button