Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 109

Sponsored links

Da ga can cikin muryar tashin hankali ta ce,”Dolene na kiraka Arshaan. Dan tabbas akwai matsala. Matsala babba why. Na kasa gane komai, ka saka zuciyata a rudani gaba daya game da abinda ka aikata a kotu. Shin mi hakan ke nufi? Taya komai da muka aikata mu ukkoma kansa shi kadai? Kai ne kai hakan kokuwa hatsabibin yaron can ne ya kulla mana gadar zare ta hanyar yar iskar yarinyar can. Wihy kaina ya kwance gaba daya, dan ALLAH ka zaba mana wajen haduwa yanzu da gaggawa kar zuciyata ta buga”.

“Da zata buga din ma da kowa ya huta.Please malama ki kyaleni bana bukatar magana da kowa okay”. Kittt ya yanke wayar batare da jiran cewarta ba.”Ashe zan kasheka na kashe banza idan kace zaka zamar min matsala Arshaannn!!!”.

Ta fada cikin karaji da cije lips dinta jikinta na rawa. Wayar ta cilla saman gadonta ta cigaba da kaikawon da take tun dazun a cikin dakin. Tunda ta baro kotu ta gagara zaune ta gagara tsaye.Tasan in har Miran Arshaan ne ya shirya komai ga Miran Jasim hakan na nufin itama bazata tsira ba dan tare sue kulla komai. Idan kuma Tajwar Eshaan ne ya ganosu kama Miran Jasim kawai ba komai bane garesu face talala. Don dole ma akwai wani abu da ya kamata ta sani, dole ta sanshi a yau din nan yanzun nan basai gobe ba. Idan Miran Arshaan ya cigaba da wofantar da tuhumar da take masa to lallai zai ganta yanzu a sashensa kuwa. Sai dai duk ma abinda matar tasa zata zarga ta zarga. Ko kuma in ma barewa zatai why sai dai ta bare da su su duka amma bazata taba barin Miran Arshaan ya sha ba shima ko ya kaita kasa kamar yanda ya kai Jasim. A fusace ta sake fisgar wayarta ta hau rubuta masa dogon text message jikinta sai tsuma yake. Ga uwar zufa ta mata sharban kamar wadda taci gudu a cikin dokar jejin da babu komai sai sahara mai zafi da ta dauki zafin rana.

Yi take kamar zata tsumbula cikin wayarta dake a hanunta. Ihu kawai ya rage ta kurma akan kiran Daneen Waheeda da take faman yi tun bayan fitowarsu kotu amma bata daga ba.Ta bata lokaci da tunanin zatai kiranta in ta gani amma babu alamar hakan zata faru. Kuma asha ba shima ko ya kaita kasa kamar yanda ya kai jasim. A fusace ta sake fisgar wayarta hau rubuta masa dogon text message jikinta sai tsuma yake. Ga uwar zufa ta mata sharban kamar wadda taci gudu a cikin dokar jejin da babu komai sai sahara mai zafi da ta dauki zafin rana..

Yi take kamar zata tsumbula cikin wayarta dake a hanunta. Ihu kawai ya rage ta kurma akan kiran Daneen Waheeda da take faman yi tun bayan fitowarsu kotu amma bata daga ba.Ta bata lokaci da tunanin zatai kiranta in ta gani amma babu alamar hakan zata faru. Kuma a kalla kira na goma sha bakwai kenan take mata.Banda text message da zai iya zama biyar koma fiye da hakan.

Kamar almara aka daga wayar, cikin rawa da kakkarwar jiki ta kaita kunnenta tana fadin.

Kamar almara aka daga wayar, cikin rawa da kakkarwar jiki ta kaita kunnenta tana fadin.

Da yar raha-raha da ga can Daneen Waheeda ta ce, “Oh oh Kinga kwantar da hankalinki nabar wayar ne a daki why ina sashen surukinki. Halan wani masifar shegiyar can ta sake jangwalowa?”.

“Uhhm ai wannan karon ba ita ta jangwalo ba ita aka jangwalowa. Ni Ashwaq naga abinda zai kasheni a wannan masarautar yau da raina. Wai kin san kuwa madarar da aka shayar da dakinki wai Miran Jasim ne ya samar da ita”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button