Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 103-104

Sponsored links

Bayan wata daya Wise ta kwace Papa sai abinda tace,Yau Sabreen bata da kudi taje har part din Wise dake yau a dakin Wise yake ba na Mama ba ta samu Papa a dining an shirya Masa better Yana iba,tana zuwa tace Papa dan dubu hamsim din da ka min Alkawari,Wise tana cin abinci itama tace baza a baki ba baki da aiki sai shaye shaye kudin a banza ake baki marar tarbiyya,kullum kice kudi kudi sai shaye shayen banza,Papa yace to kinji dama na gaji da baki kudi gaba Daya ke kike talauta ni kece Kika jefa Ni a halaka sabo da na biya Miki bukatunki tashi ki bani waje,Sabreen ta mike cike da takaici,Wise race idan bai wuce dubu daya ba a bak, ko kula Wise bata Yi ba itaje ta fadawa Mamanta,Mama ta fito a fusace tace wallahi na gaji yau sai na tona Masa asiri bangaren Iyamami taje cike da bala’i tace ke tsohuwa wacce bata iya tarbiyya ba ki sani danki Yusuf shi ya kashe Dan Uwansa na Jini Sunusi guba ya sa Masa a hankali ya Fara rashin lafiya ya mutu sabo da hassada da son kudi na gaji da rufa Masa asiri,shine ya tura Yan fashi Suka yiwa Baffa fashin milliyoyin kudi sabo da ya dauki nauyin yarsa,yanzu Haka shine ya siyar da wasu kadarori na Baffa ba tare da shi Baffan ya sani ba, na gaji da rufa Masa asiri,gwara ayi uwar watsi,Papa ya taho wajen Iyamami yaji abinda Mama ke fada jikinsa ya hau tsuma,lokacin tare suke da Wise,ta rufe baki tace cab di,Iyamami ta kwashe Mama da Mari tace Yar sharri,Papa ne ya shiga yace gaskiya ta fada ya zube gwiwoyinsa a kasa hawaye Yana zuba a idanuwansa yace wannan abin da nayi shine mafi Muni a rayuwata na rasa yanda zanyi na iya fada amma abin Yana damuna bana samun sukuni idan na tuna nine sanadin dan Uwana,Ki Kira Sulaiman ya kaini kotu a yanke min hukuncin kisa ko naji sanyi a raina,ya kalli Mama yace kema a yau dole na Fadi naki kece Kika Hana faccalarki zaman lafiya kece munafuka.

Labari ya Fara bayarwa yace Sanda taga faccalarta Mamin Nawwar tana zaune lafiya da mijinta gashi mijinta yafini kudi shine ta hada baki da wani mutum a matsayin babban malami ne yake zuwa Yana fadawa Baffa Mami tana Neman ransa tana Masa asiri nan gaba idan bai gujeta ya kaurace Mata ba zata iya kashe shi,kullum malamin nan Yana zuga Baffan Nawwar Yana fada Masa karairayi tun baya yarda har ya yarda ya Fara wulakanta Mami da yaranta Kuma da sa hannunki kema Iyamami ko Baki San da zancen ba? Iyamami tayi mukus yaci gaba yace sabo da kin tsani Mami kina ganin ta mallake Miki danki kuka hada Baki,sannan ke Kika jawo har na iya kashe Dan uwana kullum sai ki dinga cewa nine abin tausayi bani da komai sai dai na zauna a karkashin Yan Uwana Kika dinga cewa Mami ce tasa Baffa Bai maidani me kudin gaske ba duk kuwa da kokarin da yake ke ba kya gani ai wani baya yiwa wani arziki Kuma gidajen da na siyar na Baffa kece Kika zugani Kika ce na siyar ai bazai gane ba,duk kece Kika dinga hada Yan Uwa fada dama irin wannan wasu Iyayen suke raba Kan yaynsu ya karasa Yana kuka,Iyamami tana kuka wiwi tace ai bance ka kashe Sunusi ba,ke Kika zugani Kika ce sun hada Kai sun ware Ni sun fini arziki kece wallahi ko me ya faru kece kika dinga zugani, Baffa da ya Riga ya shugo tare da Nawwar kafarsa kasa daukansa tayi ya zube saman kujera sabo da bacin rai, Maman Sabreen asirinta ya tonu Sai kuka, Iyamami kuka Papa ma kuka,Nawwar mamaki yake abin kamar a mafarki,Iyamami faduwa tayi ta sume aka kwasheta zuwa asibiti gaba daya Kuma aka tattara har Wise zuwa asibitin,an Dade kafin Iyamami ta farfado,Baffa da Papa sune a kanta a hankali ta Bude idonta tana magana a hankali tace ku yafe min dan Allah,Hannun Baffa ta kamo ta kamo na Papa tace ku yafe min dan Allah ku hada kanki ku yafi juna,Yusuf kayi kuskure Amma da hannuna a ciki ban San abin zai Kai ga kisa ba,tunda ka Gane gaskiya ka tuba ga Allah kabi Allah ka gyara kuskurenka yanzu a Zamanin nan ko an kaika kotu ba lallai ma a yanke maka hukunci dai dai da laifinka ba,Abu ya faru sama da shekara talatin me za ayi,Papa yace za a iya yanke min hukunci Mana Sulaiman ya kaini kotu ko naji sanyi a raina ya sake fashewa da kuka yace wlh tun daga ranar da Sunusi ya mutu na rasa kwanciyar hankali in na tuna nakan kasa bacci ya zanyi da hakkinsa, Baffa bai iya magana ba ma bare Nawwar,Mama tana gida tana tattara nata ya nata ta gudu gida garinsu itama tana ta kuka,Sabreen ce tazo da gudu tace Papa Mama ta tafi,Papa yace tafi ruwa gudu na saketa saki daya Zan rubuta Mata takardarta,Sulaiman yace shashasha mutumin banza mene amfanin sakin nata,Papa Wise ya ruko ta fisge hannunta tace yo Ni ai ban San laifin naka yakai haka ba wlh bazan zauna da makashi ba,Nawwar yace ai Kuwa kinyi karya,wani yace kice kina sonsa ba inda zaije Kuma Zama a gidansa ba fashi idan Kuma kece kike da kanki sai ki tafi gida na gani,Wise tace gidanka Zan koma ai,yace badai gidana ba,tace idan banzo gidanka ba gidan wa zanzo wallahi nan Zan dawo dole ne na taho ta fice daga Asibitin hankalin Papa ya sake tashi shi Kam a baya Dan kudi auri Wise amma tunda tazo gidansa ya fada kaunarta da gaske son da bai taba yin irinsa ba,Nawwar yace Papa kayi kuskure da badan abin nan ya Dade ba wlh da kaina Zan Kai kararka,yanzu ma zaka iya Nawwar mene amfanina,Baffa ne ya harari Nawwar yace Wai Ina ruwanka ne bana son rashin kunya,Nawwar yace ai gashi nan garin son malamanku masu kudinmu sai a samu wani banza kazamin malami ya dinga zugaku tunaninku yasan gaibu,Kuma karya ce sannan ma malamin ma kaji fake ne wani katon banza ne ya shiga rigar Yan tsubu yace Yana hango maka Mami tana Neman ranka wannan daga ji kasan ba gaskiya bane,Mami kafi kowa sanin wacce, Zanci ubanka idan baka min Shuru ba Saura naji zancen a wajen matarka,Nawwar yace ita da take kawarka baka suruka da ita sai kawance kuyi ta hirarku bakwa so ma naji zancenku dan taji Mene.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button