Hausa Novels and Stories

X World 1

Sponsored links

*York city*

Nifa wallahi nagaji da wanan iskancin da kake mun, haba kullum sai kazo kayi ta tada mun da sha’awa kuma ba cina zakai bah, kai kenan kullum baka da aiki sai romance.

Toh nidae Yau gaskiya na gaji, ayita ta k’are yau kwanan mu nawa da aure?, kusan kwanaki talatin kenan?.

Amma duka saunawa ka taba kwantawa dani, kullum sai kazo kayi ta Romance.

Gaskiya ni dai bazan yarda, bah yau sai ka bani hak’k’ina idan kuma ba haka bah, zan kwata hak’k’ina.

Saboda ni wallahi wannan iskancin naka ba k’aramun isata yayi bah.

Kawai ina cikin zaman zamana agidan mu kazo ka auro ni.

Ka d’auko ni kamun dad’in bakin ku kalar na maza, ka kawo ni nan, nasha da nazo gidan ka Zan huta na samu kulawa da kwanciyar hankali da biyan buk’ata amma sam ina ba haka bah.

K’awayena suna ban labari cewa aure akwai dadi sosai kuma ga samun lada idan nayishi na huta zanji dadin rayuwata.

Duk wata damuwata zanji ta gushe sam bata, saboda farin cikin da nake tunanin zan samu agidan ka.

Nayi tunanin kaine maganin damuwata, kaine wanda zai fito dani cikin haske ayayin dana shiga cikin duhu.

Amma ashe sam ba haka bane bah, na yaudari kaina da yadda da dadin bakinka…” Numfashi ta sauke a hankali tare da gyara Rigar barcin ta mai kaman kimonu,gaban sa a buɗe wanda ya zamana daga ciki bra ne sai pant .

Ciza laɓɓanta tayi na ƙasa tana yin farr da idanun ta na cikakkun yagaggun mata . Motsa bakin ta tayi da take Cigaba da Taunar Chewing gum tana mai cewa “Da nasan tun farko haka kake da bazan yadda na zama abokiyar rayuwarka bah dama Haka Sojoji suke basa da imani,Amma Yaya Suhail sam ba haka yake ba , ba haka yake da iyalin sa ba ai shima Soja ne .

Yanzu fa saboda ni matar ka ce!, ta sunnah, fa kenan ka kasa bani hakk’ina kenan, ya kake so nayi?.

Akwai wand’an da suke zina domin suji dadin su more rayuwar su, amma ni kuma sam ba haka ba auran sunnah mukayi da kai . Ɗago da idanun sa yayi wanda sai a yanzu ma ta samu damar kallo daga gare shi . Takaici ne duk ya ishi zuciyar Muhammad, A Zuciyar shi cewa yake ” Biyayya nayi na Aure ki ba don na taɓa jin son ki a zuciya ta ba , Amma tsarin matar da nake so Sam ba irin ki bane , mace mai Hankali nake buƙata wacce bata da yagewar idon ki , koda na Aure ki ,Ni nasan Ragowar wasu na Aura. Duk kuma yanda nake rashin jina ai bance bana son mace mumina ba . Lumsassun idanun sa ya watsa mata tare da haɗe Girar sama da ƙasa . Ko ba’a faɗa maka ba miskili ne na ƙarshe . Motsa bakin sa yayi kaman zai mata magana sai kuma ya ɗan ciza laɓɓan sa na ƙasa yana sauke idanun sa zuwa Saman Screen ɗin laptop ɗin sa . Lumshe ido Nisa Tayi tana jin Wani karr² a jikin ta ta ko ina .

Cike da masifa irin na ma fama da matsanancin buƙata ta Cigaba tayi da cewa ”

Mu fa karka manta aure mukayi, idan ma mukayi lada zamu samu ba fa zunubi ba.

Taƙare maganan tana kallon fuskar shi wanda taga gaba Ɗaya Attention din shi ba akan ta yake ba . Hannun ta tasa tana ɗago Fuskar shi tare da shafa Sajen fuskar sa kai da gani kasan Wannan tasan waye namiji in and out . Kallon sa take yi shima yana mata Wani irin kallo wanda tafi kama dana Wulaƙanci .

Ka gafa tun d’azu nake ta faman zuba sai ka ce  radio, amma shiru sam ko tankamun kaki yi…. amma ba komai yanzu wurin karfe goma kenan na dare amma baka da niyyar yin komai akaina.? Kwanan mu Fa biyu kenan da zuwa honeymoon anan York city,Amma babu wata Aya da ta Gifta tsakanin mu.?

Cikin Murya kaman zata saka masa Kuka tace tun dazu fa nake jin gindina ajike, narasa inda zansa kaina.

Hannun sa yasa yana raba jikin ta da nashi tare da komawa yana jan bargo bai ce mata ci kanki ba. Zama tayi idanun ta na fara tsiyayar da Hawaye na tsaban bakin ciki da damuwa na buƙatar ta . Tana zaune kusan 11pm . Juyawa tayi tana kallon kyaƙyƙyawar fuskar shi kaman Balarabe musamman kwantacciyar Sajen fuskar shi da ta ƙara ƙawata shi . Pink lips ɗin shi take kallo tamkar ta saka bakin ta ta hade tayi ta tsotsa amma ba hali sarai tasan zafin zuciyar sa sai yayi mata Abin da bata zata ba .

Data lura da cewar bacci ma har ya kwashe shi yasa ta jan dogon Tsaki mtswwwww …. Miƙewa tayi tana ficewa daga Ƙayataccen Bedroom din nashi .

A tsakiyar Falon ta tsaya jikinta sanye da rigar baccin nan mai shara-shara duk tana yin hakane domin jawo hankalin shi gare ta amma sam shi ba ta kan ta yake ba bata a gaban shi gata dai ita matar shi ce duk da kasancewar kamin Auren nasu komai ya gama ida faruwa tsakanin su , shiyasa a yanzu baya da buƙatar ta kwata² .

Zuwan ta cikin parlour kenan ta samu wuri ta zaune takaici ya isheta… ta rasa ma abunda ke mata dadi sam haka nan taji zuciyar ta ya tsinke wayar ta kara a kunnen ta tare da kirar numbern Aminiyar ta wato Khady. domin ta bata shawara, akan al’amarin nan nasu gaskiya abun na damun ta matuk’a sosai.

 

*Kaduna*

 

*Zongo road*

 

Masu layin lalli ne sun taru iya ganin ka sunfi ƙarfin mutum Talatin duka zaman Jirar mai lallin suke yi . Inna Salame ne ta fito daga Ɗakin ta Wanda ya kasance falle Ɗaya duk da kasancewar a layin akwai masu hali amma su dai suna daga cikin marasa ƙarfi sosai . Don kofar Gidan ko kofar Arziki babu a haka suke kwana a bude da yake Kasantuwar tana da yara maza kusan Rai shida , Sai Kuma Autar ta Mace kuma itace ta bakwai . Wanda duka Wannan layin ita kaɗai ake zaman Jira . Kallon masu lallin Inna Salame tayi tana faɗin ” Kuyi hakuri Don Allah Autar nawa ne badai Yawo ba . Zaliha ce ta kalli Inna Salame tana cewa ” Allah kuma yasa ba tana can tana Faɗa Da Mutane a layi ba . Don Zahra ba Haƙuri sam badai iya masifa ba . Assalamu alaikum A bada Shinkafa me mai da Yaji na Dari da Hamsin. Juyawa Inna Salame tayi tana faɗin ” To kawo kaman kuwa kasan yanzu aka sauke. ” Amsan Kudin Hannun yaron tayi tana Nufar madafin ta inda take sayar da Shinkafan , Wanda lokacin damuna take jin jiki don ko rufi babu .

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button