Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 12

Sponsored links

Ku bamu kuɗin hannun ku ku tafi cikin salama. Wallh baki isa ba , kin san yanda muka sane shi ne? . Cewan Laurat tana fiddo da idanun ta waje.

Me yasa kk zaɓi wannan sana’ar zalunci n a matsayin ki ta mace? Mata da tausayi aka sansu bada irin….ke yi mun shiru Nice nan Bilkisu mai gado , ba zaku tafi da kuɗin nan ba indai kun tafi dashi to na tashi daga sunana ne. Kina faɗin Ni macace , a lokacin da yunwa yake damuna da ƙanƙantan shekaru na ,ina kuka ina cewa ” Su bani abinci ko ruwan sha basu bani ba , da ƙarfi na na ƙwata daga hannun su , na zama sarauniya a fadata , na zama tantitiyar mara ji na fara fashi , yanxu sai ku kawo mun Allah ɗaya ne…ku bani kuɗin kona gwada maku damtse.

Shiru sukayi Idon su kaf ya kyakyashe babu mai iya kuka , Sumayya ne tace ” Da hakan kika yi da yafi mana ,idan kin cika Bilkisu ki amashe kuɗin nan daga gare mu , ba tare da makami ba , kawai ƙarfin naki , yanda ki ke taƙama kin wahala ,muma duk a wahalcen muke……wani irin zafi maganan Sumayya yayi mata wanda yasa ta miƙewa tana tun karo ta kai tsaye….zagaye ta sukayi suka rufa mata dambe suke na ƙwatan rai ,tabbas sun ji jiki a hannun Bilkisu , wanda Sumayya ce ta buga ta da bishiya nan take ganin ta da jin ta ya ɗauke , ɗaukar Umma tayi suna neman hanyan barin jejin….

Saukar jirgin yayi dai dai da fara saukowan Fahad cikin shigar ƙananan kaya da suka amshi fatan shi ƙwarai , ɗaga kai yayi yana hango Sir Khamal da yake sanye cikin shigar Trac suit arsh colour abin ka ga farar fata baƙaramin kyau sukayi mashi ba…Nufo inda yake Fahad yayi yana bashi hannu , suna gaisawa ba tare da kowa yace komai ba suka shige moton haɗi da barin airport ɗin take…..

Me napep ne ya kalli su Sumayya yana cewa ” Hjy ina za’a kai ku? .shiru su duka sukayi don Basu san ko ina anan ba! Sumayya ne tace ” Kai mu layin masu kuɗi a Zaria.

Me napep ɗin ne yace” Aƙwai G.R.A , aƙwai Tukur Tukur , aƙwai kuma ƙaura…wanne ciki za’a kai ku? . Laurat ne tace ” Yi mana bayanin ko wacce a ciki ya tsarin wurin yake?.

Me napep ɗin ne ya basu amsa da” G.R.A. Nan ne unguwan masu kuɗi alhazan Zaria mny ƴan siyasa da sarakuna.

Ƙaura a cikin City yake unguwan masu mulki da sarauta kenan da ƙafarta , kuɗin akwai amma ƙaryar su tasha ƙarya….

Tukur Tukur unguwan matasan masu kuɗi yara samari da masu shekaru dai dai….kuɗi boko ƙaryar komai ya haɗaa

A wannan layi . Aaa’aaa’aaaa kai mu Tukur Tukur cewan Safna da Sumayya suna haɗa baki a tare. Nan take me kafu babur ya kwana yana nufar tk road.

A tangaɗi ta Nufo Asibitin A.B.U tudun Wada…cikin tangaɗi take tafiya wanda kowa darewa yakeyi yana bata wuri , kai tsaye inda likitocin ke zaune Bilkisu ta nufa ,kanta na xubda jini kaman jinin jikin ta zai ƙare….da sauri wata nurse tayo kanta don taimakawa ,amma sai ta ɗaga mata hannu alaman a’a .

Zama tayi a kujera wanda likitocin da ganin ta gaban su ya faɗi ,don ko ba’a faɗa ba sun san wannan tantiriya ce lamba ɗaya. Kowa kasa tunkarar ta yayi sai Nurse Yusrah dake shigowa , cikin wani irin sauri ta nufo ta tana kama fuskar ta tana cewa ” Nurse a bani bandeji da auduga …cikin zumma suka miƙo mata , hannun ta takai tana fara masa treating raunin da taji , kana tace ” Ina ƴan Uwanki ina Mama da ƙanni? Yusrah tayi maganan tana kallon Bilkisu , wanda cikin murya ta barasa alamu bayan abin ya same ta sai da tasha tayi nak sannan ta nufo asibitin…Nuna Yusrah ta hauyi da hannun ta kamin tace ” nine Uwana nine uban kaina kuma nine ƙani Yayan kaina”.

Wannan wani irin shashanci ne? Cewan Nurse Yusrah tana jan tsaki , tana cigaba da aikin ta don ganin ta tsaida jinin. Hannu Bilkisu takai tana amsan Almaka shin tana caka shi a raunin goshin ta da shima yake jini….wani irin rintse ido duka sukayi ,kamin tace” rana ta farko dana nema abu ya kuɓce mun , ina xan same wa’annan yaran? Dole na gansu naji su waye su? Taya suka samu kuɗin nan….. Cewan Bilkisu tana caccakar kanta da almakashin , jini ke da zuba cewan Yusrah cikin tsoro da tausayawa don ta fahimci a maye Bilkisu ke maganan.

Wai me kkce waye iyaye na? To babu ! Amma ke zaki iya zama iyaye na inkin damu da gani na a haka , shegun likita baku iya komai ba sai saka fararen kaya na banza da wulaƙamci , duk wacce bata zo inda nake ba sai……keeee waye sunan ki?

Yusrah tayi maganan cikin fusata . Cikin Muryar ta da ya fashe tace ” Bilkisuuuuuu

.

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button