Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 69

Sponsored links

Shiko da tun sanda ta maida kai ta duƙar ya fahimci inda ta dosa hanyar fita ya nufa, sai da ya je gab da ƙofa a maganar nan tasa kamar ta dole ƙasa-ƙasa ya furta “kiyi wanka” ya ƙarasa ficewa. Ta jima zaune maganar kiyi wankan na juya mata a rai, tana da buƙatar wankan, amma tana jin kunyar yinsa saboda sanin bata da kaya a nan. To amma tunda shine ya ce tayi tasan maybe ya ɗauka mata kamar wancan ranakun. Da wannan tunanin ta gamsu da yin wankan. Sai da kuma ta kammala ta duba babu bathrobe duk sai towels a bathroom ɗin. Kamar zatai kuka ganin duk basu da wani girma, da ga ƙarshe ta samu ɗan babba da ya kai mata gwiwa da ƙyar.

Kamar mai shirin yin sata haka ta fito da sanɗa, ta saki wata wawuyar ajiyar zuciya ganin babu kowa a ɗakin, da ɗan hanzarinta ta ƙaraso cikin ɗakin tana dube-duben koya ajiye mata kayan, ganin dai babun tai ƙwalƙwal da idanu kamar zatai kuka. Zuciyarta na raya mata ta koma ɗakin da kayanta suke, ɗan ɗagowa tai firgigit dan jin motsi da tai har towel ɗin na neman suɓuce mata saboda tun asali ita fa bata iya ɗaure towel da ƙyau ba sai Arfa ta mata, shiyyasa tafi son babban towel da zata iya cikuyewa a hanunta ta riƙe.

 

Cak ya tsaya sakamakon saukar idanunsa kan wani damɓareren tabon tawadar ALLAH a bayanta dake fari sol a ta ɓangaren kafaɗar damanta. Iffah da duk ta rikice da ganinsa tuni ta ɗane gadonsa taja lallausan duvet ɗin sa ta cikuykuye jikinta dake mazarin rawa. Babu abinda ta tsana kamar namiji ya gammata jikinta. Musamman ma shi da takema kallon wani abu da ban. Gwanin naku tuni ya basar da haɗiye komai kamar ma bai san da zamanta a ɗakin ba. Sai ma ƙarasa takowa da yay jikin gadon ya ajiye mata kayan da ke hannunsa ya kai zaune shima ya bata baya. Idanunsa ya rumtse zuciyarsa na wani irin harbawa da ganin ƙyaƙyƙyawar surarta da tabon nan na tawadar ALLAH da ke a bayanta. Buƙatar son sake gani yake dan tabbatar da abinda zuciyarsa ke cusa masa yana ƙaryatawa. Sai dai yasan haka gatsau gareta bazai yuwu ba, dan haka sai kawai yama miƙe ya fice a ɗakin domin bata damar shiryawa.

Tsahon mintuna goma sha biyar ya ɗauka kafin ya sake dawowa ɗakin. Ta saka kayan sai dai tana zaune a kan gadon ta cusa kanta cikin ƙafafunta komai da ya faru na dawo mata tamkar mafarki. Dan tsantsar tsanarta data hango cikin idanun Malikat Bushirat yaƙi barin ranta sam. Tasan zata iya ganin fiyema da haka saboda abinda ta aikatama tilon ɗanta amma sai zuciyarta ke tabbatar mata akwai dai….

 

Motsin shigowarsa ta sata katse tunanin sai dai bata ɗago ba. Kallo ɗaya yay mata a cikin kayan nasa da sukai mata burum-burum duk da t-shirt ce fara da wando 3quater ya ɗauke kai. Bayan minti ɗaya da wasu ƴan sakkani taji motsin zamansa kusa da ita. Ɗagowa tai tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta, dan wani kewar iyayenta da yan uwanta takeji. Shayin da ya ajiye a ɗan coffee table ɗin gaban gadon ya tura mata batare da ya ce komai ba. Ƙyakyƙyawan kofin ta bi da kallo, sai taji shayin ya burgeta dan tunda ta shigo ɗazun dama ƙamshin ya cika mata hanci. Ɗan ɗagowa tai, sai ko suka haɗa ido, ƙif-ƙif ta farayi da nata kamar zata sake sakar masa wani kukan da take ƙoƙarin haɗiyewa.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button