Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 91

Sponsored links

Sai kuma ya samu kansa da tura hannunsa cikin gashin nata, sosai tsantsi da kamshin gashin ya tafi da imaninsa har besan sanda yace;

“Dama haka attachment din yake so soft? I love the texture!”……

Haka ya cigaba da tura hannunsa a gashin nata at the same time yana driving da dayan hannun………

Horn yaji anayi masa da karfi ashe yabi one way be sani ba, da sauri yayi gefe da motar inda Allah ya taimakesa space ne da Allah kadai yasan me zasu daka daba karamin accident zasuyi ba, yana cemata bata iya driving ba sai gashi shima ze tapka shirme…

Parking yayi ya daki steering din motar yana fadin;

“Damn it! Kedai komai naki masifa ne, gashi kinsa garin taba artificial gashinki zan kashemu a banza!”……

Sai kuma ya kwantar da kansa ya shiga tinaninta duk da tana kusa dashi…..

Yana cikin wannan hali wayarsa ta fara ringing, dagowa yayi da sauri yana duban me kiran, sosai hankalinsa ya tashi ganin Mami ke kira, yanzu haka an kirasu ko sunje basu gansaba shine take kiransa a waya, wai ya akayi ya manta da consequences din gudunwan dayayi ne, this girl has been putting him in more and more trouble tinda tashigo rayuwarsa…

Yanke shawarar yayi ignoring call din kawai yayi idan yaso in yagama da issue dinta sai yaje yayi facing dinsu…..

Saida ta masa five missed calls sannan ta hakura, ya sauke wani gauron ajiyar zuciya yana addu’ar Allah yasa karta kara kira…. Saidai kash addu’arsa bata karbu ba dan baifi minti uku ta bayar a tsakani ba ta cigaba da kira, duk yanda yaso ya share kasawa yayi saboda kiran is getting out of hand, saida ta mishi 10 missed calls sannan ya daure ya daga wayar…..

“Hello son, kana ina? Can you hear me? Is this you?”…..

Shiru yayi yana kokarin tantance yanayin datayi maganar, indai ba kunnensa bane ya jiyomasa ba daidai ba kamar mami kuka take, toh what could have happened?…..

“Dan Allah Saifuddeen kamin magana, tell me you’re not dead kar zuciyata ta buga, you won’t understand how much I love you”….

Ya sake tsinto muryarta tana fadin haka cikin shasshekar kuka…..

“Relax Mami! It’s me meyafaru? Pls stop crying you’re breaking my heart”…..

Ya fada yanajin zuciyarsa kamar zatayi tsalle ta fado, this is unbelievable! Ace Mami na kuka? No!”…..

“Yimin magana sosai inji muryarka, ka tabbata kaine kuwa?”…..

“Yes mom, meyafaru dan Allah kidena kuka, tell me what happened?”……

Katseshi tayi da fadin;

“Yace nan da 15mins ze karaso, muyi sauri mu karasa gidan”…..

 

“Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode maka daka kare saif, rabbil izzati ka cigaba da karesa, Fisabilillahi meya tsare musu ne?”……

 

“Ameen ya Allah, hmmm shiko ya tsare musu abubuwa dayawa mana amma ta Allah ba tasu ba”…..

 

Umm batace komai ba taja motar suka tafi tana dan wani lissafi a ranta game da abinda mami tace…….

 

Ko breakfast basu iya sunyi ba suka tafi prison dan su samu information a gurin Deen kan yanda zasu fara neman yarinyar mutane, only for them to get to to a burnt building, prison din ya kone kurmus kamar baa taba gini a gurin ba, a rikice suka shiga tambayar yan kallo abinda ya faru dan sun kasa fahimtar komai, kadama Umm taji labari dan har tayi breaking down tun kafin taji abinda ya faru as the emotional person as she is, bayani aka fara musu akan wurin aka kaiwa hari cikin dare aka kona komai naciki da mutanen dake ciki………

 

Tsabar rikicewa Mami batasan sanda ta fara dialing number Deen ba kamar basu suka dawo dashi gurin jiya ba…. Miraculously sai wayar tashiga har tana ringing, hakan yayi diverting attention dinsu suka kasa jin karshen labarin, saidai Deen sam yaki dauka ita kuma taki hakura har Allah yasa a kiran data masa na goma ya dau wayar….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button