Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 97

Sponsored links

Ni dama nasan zaka nemeni! Ba ka dauka karya nakeyi ba?, ka dauki yarda ka dora masa bakasan macuci bane”……

“Kayi hakuri, ni kadai nasan irin dana sanin da nakeyi dana barsa yayi fooling dina ban shiga gidannan ba, harda min wayo wai nabar kasar it isn’t safe here”…

Sameer ya fada yana jin daci a ransa…..

“Karka damu zan taimaka maka, kaine zaka sameta”…..

“Toh amma bacewa kayi matarka bace?”….

“Wasa nake, haushi kabani na kin yarda dani shiyasa na fadi hakan”…..

“Kai har naji hankalina ya kwanta wallahi, yanzu kasan inda yake tinda kace baya cikin prison din sanda abun ya faru?”…..

“A’a bansani ba amma nemo inda yake abu ne me sauki sosai, kawai ka kwantar da hankalinka”….

Ya fada yana smiling ganin komai zezo masa da sauki, zeyi amfani da sameer ya dawo da masoyiyyarsa…….

“Toh nagode, amma Deen yacemin I should stay away from you, wai kai mugune is that true?”…..

“Inda mugune ni bazanzo inyi kokarin taimaka maka ba ko ka taba ganin inda mugu ke taimako? Kawai yazo ya shirya maka karyane dan yana son yarinyar”….

Ya fada yana bata rai alamun beji dadin abinda sameer ya fada ba……

“Yi hakuri abokina, na yarda kai ba mugu bane dari bisa dari, yanzu meye abunyi, ko zaka bani phone number ka?”……

“Karka damu mu hadu anan gobe by 2pm, so nake ka nuna masa bakasan komai ba, you’ll play him smart as he did to you, sai goben”…..

Yana fadin hakan ya juya ya fara tafiya…..

Dakatar dashi sameer yayi da sauri yana fadin;

“Baka fadamin sunanka ba pls”…..

“Yusuf!”….

Ya fada yana karawa gaba da sauri…..

“Alhaji Ibrahim kana gani shadaya ta wuce amma yarinyar nan shiru batazo ba ka tabbata kayi yadda akace kayi kuwa?”……

Dan jimm daddy yayi sannan yace;

“Nayi wallahi! Kuma munyi da ita zatazo da sassafe ma, I don’t know what is happening yanzu”…

“In banda abinka ai kayi ganganci ya zaayi tazo ka bari ta fita daga gidan, ai cewa zakayi ta kwana anan gidan naka tinda tanada guri anan amma sai ka barta ta fita?”…..

Cewar Alhaji habibu rai a bace, bama shi kadai ba kusan duk wanda suke parlourn hankalinsu a tashe yake……

“Gaskiya nayi mistake, wallahi saida ta tafi nima nayi tinanin hakan, yanzu meye abinyi toh?”…..

Alhaji lawal ne ya karba da fadin;

“Hmmm kallonku kawai nakeyi, bari in fada muku gaskiya wannan abu ya lalace dan bazaisa tazo ba, saidai abi ta wata hanyar a mata kiranye ta tawo ko a ina take!”……

“Ka kawo shawara me kyau, asan yanda zaayi a mata kiranye instantly, kayiwa boss text message”…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button