Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 66

Sponsored links

Deen tin sha biyu yake zarya a part din su mami basu dawo ba, gashi kiran duniya ya musu sunki daga waya, su kuma suna sane dan sun san tsap ze iya biyosa shiyasa kawai suka share shi…… Har yaje yayi sallahr azahar ya dawo basu dawo ba, lokacin ya zama so frustrated har ya fara wurgi da throw pillows, yana cikin wannan hali yaji wayarsa na ringing, da sauri ya dauka duk a tunaninsa su umm ne kawai yaga number sudais ta Nigeria, tsaki yayi ya dauka yasa a speaker yace;

“Kai kuma yaushe ka shigo kasar?”….

Kwashewa da dariya sudais yayi yace;

“Kai kuma waya taboka haka? Gaskiya ka rage zuciga man”…..

“Bazan rage zuciyar ba dan ubanka!”….

Wata dariyar sudais ya kara fashewa dashi yace;

“Dan uwan babarka ka zaga ni ba ruwana”….

“Kai kasan wannan, idan dariya ka kirani kayi zan kashe wayata”….

Saita muryarsa sudais yayi yace;

“Allah ya wuci zuciyar dan gaban goshin umm da anna da bappa, ni dama kiranka nayi in sheda makamuna tafe yanzu”….“Ni nazo ma bare su? Ta fa rantse kowa na familyn shuwa sai yazo ya ganta, duk wanda kaga be zo ba tace uzuri babba ya bayar, shima kuma sai taga damar amsa, a hakan ma da alkawarin zuwa ko ba yanzu bane”…….

“Ikon Allah amma su bappa sun shammace ni, dana ce musu kar suyi gayya cemin sukayi fa toh”….

“Taaab lallai sun saka a kwalba, anna harda cewa kafi kowa imani a familyn dan tinda aka tsinci yarinyar ka tare a abuja”…..

Sudais ya fada yana dariya…..

Girgiza kai kawai deen yayi zuciyar na buguwa, haka kawai yaji bayasan gayyar nan gabadaya, kuma daya sani da sai yasan yanda yayi ya dakatar dasu, amma ko a hakanma ze gwada sa’arsa yagani…..

“Will call you later sudais”…..

Ya fada yana kashe wayar……

Number bappa ya fara kira amma sai ringing take ba’a dauka ba, sai ya maida akalar kiransa zuwa number anna, itako a kashe ya sameta ma, sosai yaji hankalinsa ya kara tashi ya cigaba da kiran bappa still ba’a dauka ba…….

Yana cikin wannan hali yaji sallamar baby tee, da sauri ya dago yana kallonta, ganinta ita kadai rai a bace yace;

Shiru tayi batace komai ba, kawai taga ya saka yatsunta na tsakiya guda biyu a baki yana tsosa, wani iri taji tayi nufin janye hannunta saidai ina ko motsi hannun beyiba, sai ma lashe duka yatsu goman daya farayi kamar wanda yaci danwake yake lashe hannunsa….

Sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, mutum kawai ya tsaya yana lashe hannun wani kamar wani maye, janye hannun ta sakeyi tana fadin;

“Saif sakemin hannu, meye haka wai!”…

Ko jinta beyiba dan ya riga yayi nisa a abinda ya sawa ransa….

Sake janye hannun tayi saboda yanda tsikar jikinta ke tashi kamar yana mata tafiyar tsutsa, kawai ya janyota cikin jikinsa gabadaya sannan ya cigaba da lashe lashensa….

Suna cikin wannan hali taji anbude kofa, shi dama ya dade da barin duniyar mutane, juyowa tayi taga……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button