Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 37

Sponsored links

Cikin abinda baifi mintuna goma ba ɗakin da Iffah ke kwance ya cika da wasu a manyan masarauta. A fuska dai suna nuna farin cikin farkawar tata ne, amma a ƙasan zuciya mafi yawansu kowa da irin tasa manufar. Malikat Bushirat kuwa harda hawayen farin cikinta, farkawar yarinyar da a kallon farko ta gama shiga ranta ya goge mata sauran damuwar abinda ya faru game da kashe Hadiman da aka aika suka aikata sherin daya jawo komai. A take Malikat Bushirat ta bada ƙyauta mai tsoka ga Baba yaro. Hakama wasu a cikin manyan sun masa ƙyautar. Daneen Ammara ce ta biyu, itama kuma ta bada mai tsoka daya bama kowa mamaki.

Ana ƙoƙari daukar Iffah zuwa sashen Malikat Bushirat kamar yanda ta buƙata sai ga saƙo da ga Malikat Haseena cewar akai Zawjata-almilki sashenta. Take fuskokin mutane da yawa ya canja a wajen, saɓanin ta Malikat Bushirat data nuna tsantsar farin ciki da jin ƙaunar surukar tata. Dan dama zuciyarta cike take da fargabar sake kasancewar Iffah babu tsaro. Duk da sashenta ma bazai iya zama kanwar lasa ba ga wani mahaluki a zahiri, sai dai yaƙin sunƙuru. To amma idan ta danganta da abinda zuciyarta ke rawa a kai komawar Iffah sashenta kamar an gudu ba’a tsira bane. Sashen Malikat Haseena kuwa sunyi imanin ko ifiritu da kansa zaiji tsoron gittawa kai tsaye balle wani shiryayye dake a masarautar….

Rashin ƙarfin jiki da rashin dai-daiton tunani yasa Iffah ba fahimtar komai take ba, hasalima tun yunƙurin farko bata sake gwada buɗe idanunta ba suna a lumshe. Sai dai tana jin komai dake gudana har ɗaukarta da akai akan keken asibitin zuwa waje. A mota a ka sakata Daneen Ammarah tare da ita. Sai Malikat Bushirat da tabi bayansu a tata motar da ake tuƙata. Ganin haka sauran ƴan son ganin ƙwaf suma duk suka bisu can dan babu mai fatar yin laifi ga Malikat Haseena…….

Tun bayan barin Iffah gidan ɗan sauran kakkaɓin farin ciki da ƙwarin gwiwar da su Fareeha suka barsu da shi ya ida kakkaɓewa. Ummu bata da aiki sai kuka. A kwana uku kawai duk ta rame saboda ko abinci bata ci yanda ya kamata. Hanash kam ba’a magana dan makamancin irin ciwon Iffah na damuwa ne ke neman bugarsa (Depression). Shi kansa Babiy dake dauriya duk ya zuƙe a tsaye wani lokaci har yi yake kamar zai faɗi. Komai ya tsaya musu cak, kunnuwansu ne kawai a buɗe na jiran kiran jana’izar tilon ƴarsu mace data rage. Dan gushewar kwana uku bai sa sun saka ran ta tsallake ba. Suna tsaka da wannan zaman jigum-jigum akai sallama da Babiy ƙofar gida. Kamar bazai fita ba sai kuma ya miƙe cikin ƙarfin hali ya zura takalma ya fita. Ɗan turus yayi idanunsa kafe akan wanda yay sallamar da shi… Abu Moosa da shima ke kallonsa ya iso gabansa da ƙyar yana tangaɗi. Riƙesa Babiy yay da sauri da faɗin, “Subahanallahi Abu Moosa!”.

Bai iya ya amsa masa ba saboda halin da yake ciki. Riƙesa da ƙyau Babiy yay suka shiga ciki yana jera masa sannu. Zai zaunar da shi a soro ya girgiza masa kai cike da ƙarfin hali. “Kamin alfarma mu shiga ciki”. Ya faɗa da ƙyar tamkar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa. Cikin sauri Babiy ya cigaba da riƙesa suka shiga cikin gidan, shigowarsu yasa Ummu miƙewa da sauri ta ɗakko tabarma ta shimfiɗa a ƙasan bishiyar dake tsakar gidan…

“Ku bani ruwa dan ALLAH”.

Abu Moosa Ya sake faɗa da ƙyar yana fisgar numfashi. Ruwan Ummu ta kawo masa, dai-dai da fitowar Hanash daga ɗaki saboda jin maganganu na tashi a gidan nasu. Da ƙyar ya iya maƙwarwa uku saboda numfashinsa fisga yake. Babiy ya ajiye ruwan da sake tallafosa jikinsa. “Abu Moosa mike faruwa ne haka? Daga ina kake?”.

Da ƙyar ya iya ɗaga idanunsa dake zubar da hawaye ya kalla Babiy. Sai kuma ya girgiza kan yana jan numfashi da shashsheka. “Abu Hanash ka gafarceni dan ALLAH, nasan wannan yana cikin numfashin bankwana da nakeyi”.

“Babu abinda kamun nikam, dan ALLAH kuma ka daina faɗar wannan magana bara mu kaika asibiti”. Riƙo hanun Babiy dake yunƙurin tashi yay yana girgiza masa kai da ƙyar. “Babu buƙatar hakan, domin ban cancanci kwatankwacin wannan adalcin daga gareka ba, kayi haƙuri ka zauna ka saurari abinda zan faɗa maka da yafi kaini asibiti muhimmanci, nasan kuma insha ALLAHU zai maka amfani da kuɓutar da yarinyarka dama sauran yaran da zasu iya biyo baya a makamancin halin data tsinci kanta”. Numfashin dake neman kufce masa yaja da ƙyar kafin ya cigaba da faɗin, “Abu Hanash ka gafarce ni nine nai sanadin shigar ƴaƴanka wannan halin, dan nine nai shunensu ga masarauta”. Da ga Babiy har Ummu da Hanash wani irin zabura sukai mai bugawa da bugun ƙirji. Ya cigaba da faɗin, “Nayi hakane dan son zuciya da shegen son abin duniya. Sai hassadarka data daɗe a zuciyata saboda sana’armu ta kasance iri ɗaya, ada tare ake amsar zumar mu a masarauta amma daga baya aka koma amsar taka kawai saboda gaskiyarka da rashin algus. Maimakon na gyara nima na zama mutumin kirki kamarka sai na kasa hakan, shaiɗan ya dinga tunzurani akan kayi sammu ne shiyyasa. Tun daga wancan lokaci naketa ƙulla hanyoyin ganin bayanka a matsayin ɗaukar fansa, sai dai duk wadda na ƙulla sai ALLAH ya kuɓutar da kai, hakan ya cigaba da ƙaramin tsanarka, dan haka na cigaba da kutsa kaina cikin masarauta dan kawai naga na ɓataka an wulaƙantaka, nan ma banci nasara ba dai. Kwatsam sai aka samu canji gwamnati, ni kuma nai amfani da wannan dama wajen sake cusa kaina cikin tsakkiyar masarauta harna samu nasarar amsuwa, nasan komai game da mutuwar Zawjata-almilki, dan ina gaba-gaba a hadiman da ke aiki ga masu aikatawar”. Yaja numfashinsa da ke fisga da ƙyar. “Lokacin da aka sakamu aikin binciken yara mata guda biyu masu hankali dan a aurama Tajwar naji a raina lokacin nasarata a kanka ya yi, dan haka na bada sunanka da adireshin gidanka. An ɗauka tsahon kwanaki ana bibiyar yaranka da kai kanka kafin azo gareka. Ko bayan mutuwar ta farko ni na ƙara ƙulla aka sake dawowa ta biyu dan burina kawai naga na durƙusar da kai ƙasa. Ka gafarceni Abu Hanash dan nayi nasara, sai dai ramin muguntar dana gina daga ƙarshe ni na afka ciki……”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button