Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 52

Sponsored links

Ba karamin shock mama tashiga ba jin wani abu banbarakwai namiji da suna hajara, abu daya tasani alhaji ko giyar wake yasha baze aureta ba mussamman yanda dansa mafi soyuwa ya mutu akanta, cike da gwarin gwiwa tace;

 

“Ke karamar yar’iska bani da lokacinki! Ke ingaya miki dagani alhaji ya rufe kofa wallahi, in banda rashin kunya da rashin tarbiyya ina mutum ina tinanin auren uban saurayinsa”……

Zama tayi akan 3 sitter tana dora kafa daya kan daya fuskarta dauke da dariyar rainin hankali tace;

 

“In banda abinki hafsah ya kamata kisan abun kunya gaba na basa ba baya! Rashin tarbiyya ko da ita aka haifeni, ke in takaice miki nina tarbiyyantar da kaina kinga ko tarbiyya zero!”…..

 

Saita fashe da dariya tana fadin;

“Wallahi harna hango yanda salon kishinmu ze kasance, bari kijima mungama magana da mijinki a part dinnan zan zauna yanda abin namu zefi tafiya daidai!”…..

Wani irin zuciya ne ya dibi mama dukda bata yarda da abinda tace ba, ta daga hannu da niyar kaiwa fatima zainab mari taji anyi saurin tare hannun an kuma ki sakin hannun, juyawa tayi a fusace sukayi ido hudu da daddy…. Sake hannu mama yayi da sauri jin fatima zainab ta fashe da wani mugun kuka, ya juyo da sauri yace;

“Why’re you crying? Fadamin meta miki?”….

Kin magana tayi ta cigaba da kukanta kamar gaske…

Cikin rarrashi daddy yace;

“Talk to me dear, meta miki in rama miki!”….

“Alhaji yanzu a gabana kake cewa wannan shaidaniyar dear?”…..

Be kulata jin fatima zainab na gunguni irin na wanda yasha kuka ya koshi alamun magana take sonyi…

“Gaisheta fa nazoyi shine take ta zagina tana marina, harda cemin iyayena sunyi asarar haihuwata , wai ka taba fadamata ni shegiya ce banda uba!”……

Ta fada tana fashewa da wani sabon kukan irin abun na tabata dinnan……

“Wlh alhaji…..”

Bata karasa ba taji saukar lafiyayyen mari a kuncinta wanda bata tantama daddy ne ya mata,sannan cikin bacin rai yace;

“Makircinki har ya kai kimin sharri hafsa Yaushe mukayi wannan zance da ke?”……

Cikin kokarin kare kai dukda marin ya shigeta sosai tace;

“Alhaji wallahi yarinyar nan ce munafuka, harfa cemin tayi aurenta zakayi saboda tsabar abun kunya?”…..

“Ni nasan bazata miki karya ba, nasan duk abinda ta fada kin fada din ne tinda halinki ne, Toh sai me inna aureta? Inma hada abinki kikayi dan nasan zaki iya toh bari in tabbatar miki aurenmu nida fatima zainab nan da sati daya, kuma a part dinnan ta zabi ku zauna tare”……

Wani kukan kura mama tayi ta chakumo wuyar alhaji, cikin fitar hayyaci tace;

“Wallahi baka isa ba! Kayi kadan kamin kishiya da sa’ar ya’yana, ko zanyi yawo tsirara aurennan baze yiwu ba wallahi!”…..

Fincike hannunta daddy yayi yana hankadata kan kujera yace;

“Ashe ko zakiyi yawo tsirara, dan ko khaleel be isa yasa in dakatar da aurennan ba!”…..

Dariya ce takecin fatima zainab sosai tadai daure ta cigaba da kukan munafurci zuciyarta cike da mamakin yanda daddy ya karbi auren hannu bibbiyu, anya kuwa? anya ba wata a kasa? Kai koma menene bazata hakura ba sai tafitar da mama daga gidan…… Tana cikin wannan tinani tajuyo muryar mama na iwun:

.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button