Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 93

Sponsored links

Dan jim yayi yana tinanin abinda ya kamata ya gayamusu gashi bayaso yayi karya dan yaga a kwana kinnan yana neman farawa abinda ba halinsa bane;

“I left because of her, I had a very bad dream about her that she isn’t safe shiyasa kawai nayi sneaking out, ina fitowa kuma naganta”….

Ya fada yana nuna fatima zainab da har lokacin take a sume…….

Ajiyar zuciya Mami ta sauke itama tana kallon fatima zainab tace;

“Ke alheri ce!!!”……

“Indeed! Badan ya fita nemanta ba da yanzu wani labarin akeyi, Allah mungode maka”….

Umm ta kara da fadin haka….

“Meya sumar da ita?”..,,

“Wallahi Mami bansani ba, nadai cire wani zobe daga hannunta shikenan ta suma”…..

“Ikon Allah, toh yanzu meye abin yi? Ka zuba mata ruwane bata farfado ba?”…..

Shiru yayi yana ayyana haukar daya tafka, mutum ya suma amma ace ya kasa basa taimako as a Doctor? Shidai wannan yarinya na barar masa da karatunsa…. Kada kai kawai yayi alamun be zuba mata ruwa ba…..

“Allah dai ya shiryeka, you’re a disgrace to the Doctors”….

Umm ta fada tana tashi ta dauko ruwa……

Dan diban ruwan tayi tashiga shafa mata a fuska kamar dai tana wanke mata fuska, saida ta mata sau biyar sannan ta fara tari alamun ruwan ya shigar mata hanci…..

Dagota tayi ta kwantar da ita a jikinta tana bubbuga bayanta tana mata sannu…..

Sunfi minti uku a haka kafin a hankali taji ta dena tari, dagota tayi tana kokarin tattare mata gashinta daya wargaje aranta tana fadin ‘masha Allah’……

Yana tsaye akansu har aka gama tattare kan sai tsaki yake wai an bawa gashin doki mahimmanci haka, babu wanda ya kulasa dan batashi suke a lokacin ba..

Sosai ta basa tausayi amma ya dake dan yanaso ya gano inda matsalar take ganin kamar a tsorace take sosai, dan dai yasan haka kawai bazata masa biyayya ba…..

“A ina yake?”….

“Jikin kofa”…..

Kallon kofar su dukansu sukayi sukaga ba kowa alamun ita kadai ke ganin abunta, kasa motsi Umm da mami sukayi dan ba karamin daga musu hankali abun yayi ba….

Gyara tsayuwarsa Deen yayi yace;Ya fada yana mika mata hannunsa alamun ta miko hannunta ya taimaka mata, ba musu ko ta mika hannun, taimaka mata yayi ta tashi har lokacin be dena mamakin yanda bata masa musu ba…..

Hannunta ya rike gam a cikin nasa sannan ya nufi kofar da ita a ranshi yana ayyana yanda zeci uban koma waye dan yasan baze wuce mahaukatan aljanunta ba……

Suna zuwa bakin kofar abu kamar almara ta nemi wanda take gani ta rasa…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button