Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 8

Sponsored links

Eesha dake kwance ta mike zumbur,tana rarraba ido,yau taga ikon Allah,gabadaya saita nemin ciwon marar tarasa batareda tasha magani ba,mamaki ne fal cikin ranta tana kara bin hannunta da kallo,tana kara tinanin wani kalan sura Allah ya zuba a wannan halittar,hannunta kawai ma ta gigice,toh inaga fuskarta,karshen tikatiki idan da’ namiji yayi arba da ita fa,yaya zata kasance? Anya bazaa sume ba?…. Dawowa tayi daga shirmamman tinaninta jin anyi banging kofar………. Itako Fatimah Zainab ranta inyayi dubu ya baci ganin yanda shashashar yarinyar tacigaba da binta da kallo,hanglove din hannunta ta mayar,tana kakkabe jikinta kamar wacce aka zubawa kashi bayan ko ruwan be tabata ba,chan kuma ta figi jakarta ta fita a fusace,tana buga kofar…………

 

Direct lecture hall ta nufa,kawai saitaji kuma bazata iya bata lokacinta ta saurari wani lectures ba,sai ta chanja akalar tafiyar ta zuwa hanyar gate………

..Tana fita ta hango motar a fake kamar yanda tayi expecting,yana ko zaune a ciki yadan kwantar da kujerar baya yana bacci,bude daidai driver sit tayi,ta mishi nuni daya fito…….. A zabure ya mike yace “Good morning ma’am,I’m sorry if I do anything wrong” ya fada hankali tashe dan wlh shikadai yasan yanda yakeji da aikin nan nashi,wani inya ganshi saiya dauka wahala kawai yakesha,amma irin kudin dayake samu da wannan aikin yasan ko kwalin degree dinshi bazai bashi ba,shiyasa duk wanda Allah ya taimakeshi ya samu aikinnan,yake kapkap dashi,dan wayanda sukayi a baya sun bashi lbr,bazata ce maka komai ba saidai kawai kaji notice daga sama an koreka,shiyasa suka bashi dan wani tactics da suke tinanin red button dinta ne akan zata kori mutum,shikenan ko yaya yaga reaction dinta ya chanza saiya fara bata hakuri…………….. Girgiza mishi kai tayi alamun ba komai ta kuma bude jakarta tazaro bandir din kudi bata ko kirga ba tamika mishi,tana mishi nuni daya tafi gida kawai sai gobe……. Tsugunawa yayi harkasa yanata mata godiya kamar ze mata sujjada dan murna da farinciki….. Ko kallonshi batayi ba tashige motar,taja tinted glass din sama,ta fizge niqab din sannan ta figi motar a guje,ya bita da addu’ar Allah ya tsareta………..

 

Tafiya tayi na kusan 30mins,dama tasaba idan zatayi irin wannan tafiyar ita kadai take zuwa,achan jikin wani kango tayi parking tana kalle kallan ta’ina zai bullo,kawai sai jitayi mota tayi horn a bayanta,mamaki ne yakamata yau kuma da mota yazo?, batace komai ba ta fito shima ya fito suka hade, basuyi magana ba ta zaro wayarta tamasa transfer din 5m a take,ta jiyo da fuskar wayarta tana masa nuni da ‘transaction successful’,gyada kai kawai yayi ya mikamata box din dake hannunsa,shigewarta mota tayi taja a guje tabar wajan………

Harta dauki hanyar transcorp sai kuma wani tinani ya fadomata arai,guntun murmushi tayi tana ayyana ta kwana biyu bataje gidan tayi tijara ba,gashi kuma tasan irin wannan lokacin kowa na gidan na nan,kawai saita juya akalar motar ta dauki hanyar gidan……..

 

Horn tayi da karfi,gateman ya fito da sauri ya bude mata gate,daidaita parking dinta tayi sannan ta dauki karamin box din tajefa a cikin jaka,ta fito a hankali ta nufi main entrance din gidan……. Mai wankin mota naganin tashige ya taso da sauri ya rufe motar domin al’adar tace inta dawo da mota bazata kara fita da itaba,sannan yafara goge sauran motocin dake parking lot din dukda gabadayansu sababbi ne………..

 

Da sallama ciki ciki tashiga main parlour din,tana bin ko ina dawani mugun kallo,Abdul ne yafara hangota,aiji yayi kamar ansashi a aljannah da ganinta,ganin kuma tacigaba da takowa yayi sauri ya dauke kai…… Suko sauran occupants din parlourn ji sukayi kamar an aiko musu da mala’ikan mutuwa,sunsan zuwanta sam babu alkhairi a ciki,haka dai suka daure kowa ya daura murmushi a fuskarsa badan yasoba……. Zama tayi a daya daga cikin kujerun falon tana dora kafa daya kan daya,ai da sauri yanmata guda uku dake parlourn suka sube kasa suna gaisheta saboda gudun abinda zeje ya dawo…. Ko kallonsu batayi ba bare tasan Allah yayi halittarsu a wajan,amma haka suka tashi jiki na rawa suka cikamata gabanta da kayan ciye ciye…. Abdul na kokarin gaisheta shima ta daga mishi hannu……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button