Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 40

Sponsored links

“Bazan gaji da tuna miki akwai ƙalubale zagaye da cikar matakin aykinki na biyu ba, kuma wannan ƴar shila na tare da kaddarar ƙalubalenne, sai dai na miki alkawarin tsayuwar daka akan hana faruwar nasarar da zatazo in har bataki bace ba. Tabbas aikin ba namu bane, kuma rigar da aka kai mata ta sanya ba tamu bace itama. Na gano hakane a daren jiya bayan mutuwar waɗan can hadiman da kuma samun lafiyar ƴar shilar.. Hakane ya sani duƙufa bincike tuƙuru domin gano daga ina matsalar take?, wanene ya shirya aikin laɓewa bayan namu? Har yaci nasarar kuɓutar da ita da tarkon makircin sa cikin sauƙi haka?……”

“Uwa kin gano kenan?”. Ta-kurya ta tari numfashinta cike da zalamar son jin amsa……..

Ina kan ƙoƙarin yin hakan yawaitar kiranyanki ya katse ni, amma tabbas wanda ya aikata yana a cikin wannan daula ne, yana kuma da babban shirin daya kamata mu sani tun a yanzu. Ina kuma ji a jikina babban yaƙine da kema ya shafeki, kuma za’a cigaba da amfani da yarinyar ne wajen tabbatar da shi in har tana cikin masarautar nan”.

“Shiyyasa tun farko nace a kawar da ita Uwa, dan babu wani amfani da wannan yarinyar zatamin face cigaba da ɗagamin hankali, gashi kuma har tana neman zama tafinta a al’amurana dake gab da kammala bayan gumurzun yaƙin da naci na tsahon shekaru a baya kafin zuwa lokacin tattara ganima”.

“Abinda kike ƙoƙarin yi shine mafi girman kuskure da zai rusa dukkan nasarorinki Ta-kurya. Domin yunƙurin kashe wannan ƴar shilar da kike tamkar kashe rayuwarki ne baki ɗaya. Tun farko na faɗa miki kasheta kai tsaye bashine mafitar ba, ba kuma shine ƙarshen daƙile yunƙurinta ba ita a karan kanta. Hasalima a yanzu rayuwarta mukafi buƙata, zamu jefata ne matsayin dutse ɗaya dazai wargaza tsuntsaye biyu. An wargaza mana shirin mu na farko a kanta, dan haka zamu tafi na biyu. Yaƙinki a yanzu shine kiyi duk yanda zaki ta baro wancan sashen daga nan zuwa cikar kwanaki bakwai. Zakiyi yanka na baƙar babbar dabba a daren goma sha uku, zakuma ki dawo da rigar data sanya. Kiyi duk wani ƙoƙarin da zai hana kusancinta da Ajlaan a turaka. Dan maganar kaita turakarsa ta rushe kuma zamu sake sabon salo ne domin kama tsuntsu mai wayo…….”

“An gama Uwa mai share kukan masu kuka. Sai dai dawo da rigar nan zai zama abu mai wahala kasancewar tana a hanun Mamma (Malikat Haseena) ne a yanzu haka”.

 

“Wannan umarni ne Ta-ƙurya”.

 

“Zanyi iya ƙoƙarina Uwa. Sai kuma maganar mutuwar Hadiman can, Shahanshan da kansa ya saka kwamitin bincike masu tsauri da basu taɓa ƙetare nasarar cika umarnin da’aka basu ba. Kinga akwai matsala kenan tunda waɗan can sun laɓe ne a jikin aikinmu suka zartar da nasu, sannan suka kashe hadiman tamkar yanda muka shirya kafin mu mu aiwatar da hakan”.

 

Wata irin mahaukaciyar dariya mai amsa kuwwa Uwa ta shiga ƙyalkyalawa, sai da ta ɗauka tsahon lokaci tanayi kafin ta tsagaita ta tsuke fuska tamkar ba itace tayin ba. Har ta ƙurya ta fidda ran samun amsa sai kuma Uwa ta sake ƙyalkyalewa da dariya tana ambaton “Ajlan! Ajlan!! Ajlan!!!” ta ƙara kwashewa da dariya tana mai disashewa a idanun Ta-kurya da zuciyarta ta kasa fassara ma’ana ko dalilin dariyar ta uwa…

Sun dawo har yanzu da ɗan sauran mutane maƙwafta da aketa ɗan ƙus-ƙus akan lamarin. Cikin ƙanƙanin lokaci aka baibaye motar, waɗanda suka shige gidaje suka fara fitowa. A yanayin da aka fidda Ummu mafi yawansu sunma ɗauka dai bata da rai, dan kuwa da gaske babu alamar rai tare da itan. Kuka da salatin da mafi yawan mutane suka ɗauka na tunanin ta mutun ne yasa Abu Zainab saurin dakatar da su.

 

“Dan ALLAH kowa ya kwantar da hankalinsa. Umm-Arfa ba mutuwa tai ba”.

 

Badan hankalin su ya kwantaba sukai shiru, sai dai dama kukan na wasu na munafurci ne dai. Matane suka kamata aka shiga da ita, a tabarmar da suka samu tsakar gida suka shimfiɗeta. Cikin sa’a Abu Zainab yaci karo da wayar Babiy dake yashe a ƙasa. Da alama sanda jami’an nan zasu fita da shine ta faɗi. Jikinsa har tsuma yake a duba contact ɗin wayar, cikin sa’a ya samo number da akai saving da Baba. Baya raba ɗayan biyu mai sunan nada babban matsayin baban a wajen Babiy ɗin, dan haka ya danna masa kira kai tsaye, sai dai harta tsinke ba’a ɗaga ba. Sake kiran yay yana addu’ar dacewa sai ko gashi an ɗaga…

★A lokacin da kiran Abu Zainab ya riski su kaka ta hanyar wayar Babiy ba’a ƙaramin tashin hankali suka tsinci kansu ba shi da Iyyani. Duk da kasancewar yamma tayi kuma yasan a yau dole ne sai ya dangana da daular ruman dole ya bazama neman wani yaro mai mota a ƙauyen nasu dake jigila a ko yaushe, cikin sa’a ya samesa ya dawo kenan ma ko gida bai shiga ba. Amma saboda mutuncinsa da ake gani yana masa bayani babu musu ya amsa masa suka ɗauka hanya harda Iyyani daketa faman sharar hawayen da suka kasa tsaya mata. Ana sallar isha’i suka iso cikin daular ruman. Basu sami mutane ba a gidan kamar ɗazun, sai Umm Yazeed da matar Abu Zainab dake dai tare da ita har yanzun. Zuwa yanzu Ummu ta farfaɗo, sai dai taƙi magana da kowa sai hawaye da taketa faman zirarwa ta gefen ido, ga numfashinta baya fita normal kamar na kowa, tana fitar da shine da fisgosa a wahale sannan a fiffisge. Kuka Iyyani ta sake fashe da shi da rungume Ummu a jikinta tana kiran sunanta. Kaka kam tsaye yay kawai zuciyarsa na harbawa da ƙuna. Suna a haka Abu Zainab ya dawo, dama sallar isha’i yaje. Cikin girmamawa ya gaida kaka, shima ya amsa masa da kulawa da godiya. Ya ɗan murmusa kansa a risine. “Ai ba komai baba yiwa kai ne. Sannan mun zama ɗaya ai mu da Abu Hanash. Ko mu irin haka ta faru da mu zai tsaya tsayin dakane a kan komai. Ruɗanin halin da Umm Arfa ke ciki yasa su bamu bibiyesu musan miya faru ba har yanzu gaskiya. Dan munata yawo a asibitoci amma sunƙi amsarta, ga jikin nata kuma yana buƙatar a duba mata shi, shiyyasa yanzu dana idar da sallar magrib naje na samo ɗan uwana dake aikin asibiti gashi muna tare, sai dai ba wani babban likita bane dai….”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button