Hausa Novels and Stories

The Sexy Boss 3

Sponsored links

Ɓangaren gidan Umma Ramatu kuwa hankali a tashe yake , musamman yayyun Umaima don dukan su kowa ya taho gidan baya iya fita , kowa tunanin a kowani lokaci za’a iya ganin Umaima yake . Cike da ihu da

 

kururuwa Hajiya Balki ta shigo gidan , ƴar tsohuwa hannun ta aka duka biyu , Ina Rahmatu take? Rahmatu yanzu wannan kun riƙe mun Amana kenan? Yanxu marainiyar Allah ce kuka bari rayuwar ta ke barazanar salwanta? . Magana Hajiya Balki take cike da ɗaga murya da hargogowa . Ƙwallah Umma Ta goge da habar zanin ta kana tace ” A’a Hajiya Ƙaddarar Allah ne . Yi mun shiru , sakacin ku dai. Ai labarai na zuwan mun ,yanda Umaima kullum da sanyin safiya ta gindin rijiyar masallaci ɗebo ruwan subahi , haka nan ma da yamma take , duk don bakyace kika haife ta wannan shine dalili. Shiru kowa na tsakar gidan sukayi ciki harda su Yaya Hannatu , don sun san wacece Hajiya Balki ,mahaifiyar mahaifin su wato malam Ibrahim mahaifin Umaima . A duniya bata da jikar da take so ,suke wasan jika da kaka sai Umaima , don itace Auta A wurin Malam Ibrahim ,kuma aƙwaita da barƙwanci ,duk ɗaurewa irin na Hajiya Balki ta zauna da Umaima sai tasanya ta dariya , duk da kuwa a cewan ta bata wasan jika da Kaka ,amma suna taɓawa da Umaima . Abun da ita kan ta Umaima bata sani ba shine , Umma Ramatu ba itace ta haife ta ba , mahaifiyar ta Allah yayi mata rasuwa wurin Aihuwar ta ,wannan yasa Umma Ramatu shayar da ita , kasantuwar Malam Ibrahim ne dama Mahaifin nata , kuma sun yi zaman mutunci da amana da Umma Rahmatu , lokacin da ta rasu Umma ta shiga halin damuwa ainun , duk da kasantuwar an auro ta daga dangin mijin a matsayin ƴar Hajiya Balki take , ita da Malam Ibrahim auren zumunci akayi ,da kuma yanda Hajiya Balki ta nuna fifiko akan ta da Umma ,amma bata taba raina Umma Ramatu ba ,haka ba’a taɓa jin kan su ba. Haihuwar ta na fari wato Umaima ta rasu ta bar duniyan.

 

 

 

 

Wannan yasa Umma shayar da Umaima ,kuma har ya wannan lokaci ana tunanin su Umaima bata taɓa sanin Wai ba Umma ce ta haife ta ba . Haka dangi da yan uwa wanda suka san ba Umma bace mahaifiyar Umaima Babu wanda ya taɓa magana akai ,har ya wannan lokaci . Amma abun da basu sani ba shine , ruɗun tsufa irin na Hajiya Balki tuni ta sanar mawa Umaima cewa ” Umma ba itace ta haife ta bA , an yi ƙwana da ƙwanaki Umaima idan taje ta dawo zata je gidan Hajiya Balki tace ” Hajiya wai da gaske ne ba Umma ta haife Ni ba? , Nan zata ce mata eh , duk abun da tayi maki na

Wannan yasa Umma shayar da Umaima ,kuma har ya wannan lokaci ana tunanin su Umaima bata taɓa sanin Wai ba Umma ce ta haife ta ba . Haka dangi da yan uwa wanda suka san ba Umma bace mahaifiyar Umaima Babu wanda ya taɓa magana akai ,har ya wannan lokaci . Amma abun da basu sani ba shine , ruɗun tsufa irin na Hajiya Balki tuni ta sanar mawa Umaima cewa ” Umma ba itace ta haife ta bA , an yi ƙwana da ƙwanaki Umaima idan taje ta dawo zata je gidan Hajiya Balki tace ” Hajiya wai da gaske ne ba Umma ta haife Ni ba? , Nan zata ce mata eh , duk abun da tayi maki na

 

Cutar wa ki zo ki sa meni nayi maganin ta .

 

 

 

Wannan maganan ta Hajiya yasa Umaima yarda ,don har hoton mahaifiyar ta ta nuna mata , shiru tayi tun daga lokacin bata taɓa faɗawa Kowa maganan Hajiya ba ,tabar ma cikin ta . Sau da yawa tana ƙara jin ƙaunar Umma ,a cewan ta ita ɗin uwa ce ta gari ,mai karamci matuƙa…

Jin an mawa Hajiya Balki shiru yasa Ta ɗaura hannu aka tare da sakin ihu tare da cewa ” Au babu Wanda zai tankani yace mun wani abu . Kamin kowa yayi magana sai ga Malam Ibrahim da yayan sa Malam Sule sun shigo gidan cikin sauri , Duƙawa sukayi gaban Hajiya Balki suna aikin bata baki da rarrashin ta . Ɗago da fuskar ta tayi kaman mai nazari kana cike da firgici na tsufa tace ” Kunji labari akan Umaimatu kuwa? Umaimatu tana wani hali . Ki ƙwantar da hankalin ki Hajiya Inshaallhu a ko ina Umaima take Allah zai bayyana mana ita bi rabil rahmti. Cewan Malam Sule . Juyawa Hajiya Balki tayi tana kallon inda Umma ke tsaye . Ramatu ɗauko tabarma ki shimfiɗa mun a tsakar gidan nan . Cikin sauri Umma ta juya tare da nufar ɗakin ta don ɗauko mata tabarmar kaman yanda ta buƙata. Yaya Hannatu ne ta dafa ta tare da taimaka mata ta miƙar da ita tsaye .tana ɗan dingisawa ta nufi Tabarmar da Umma ta shimfida mata a inuwa ta zauna tana furta ” Bismillahi”.

 

 

 

***

 

 

 

 

 

Tun da Umair ya fito daga Privacy yake shirin shi kallon inda Umaima yake bai ƙara ba , shi sunan ta ma bai sani ba . Juyawa yayi yana shirin fita daga Bedroom don don Asibiti zai nufa yanzu. Jin shashsheƙar ta yasa shi dawo da ƙafar sa baya kana yace ” Ke ki tashi ki shiga privacy ki gasa Jikin ki , kar ki karambanin ƙin gasa wurin da ƙyau , idan ba haka ba ,Ni bai dame Ni ba , ƙwana uku zanyi ina amfani dake , juyawa yayi yana ɗan sosa sumar kansa da yake a ƙwance kana yace ” Kin cika mai Sa’a da har Umair zai ƙwana uku yana… Shiru yayi bai ƙarika maganan ba jin yanda cike da tsiwa da a tunanin sa bakin ta ya mutu ta fara cewa” Waye sunan ka? Umair ko?? Bari na faɗa maka wani Abu ka sani , shi rayuwar nan komai fararre ne kuma ƙararre . Duk iskancin ka giyar kudin ka ,ka sani anyi wanda suka fika a duniyar nan.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button