Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 11

Sponsored links

Fatima Zainab tashi tayi da niyar dauro alwala kasancewar mutum me Ibada,a duk halin da take ciki bata yarda sallar farillan nan ya wuceta,kuma duk girman uzurinta barinshi take tayi sallah ta dawo…. Fitowa tayi daga toilet din parlourn duk suka bita da kallo…… Tsaki taja kamar batasan magana tace “sai nace abani abun sallah sannan za a bani in gaida ubangiji na?”……. Da sauri imaan da tafi kusa da ita tashiga daya daga cikin bedroom din dake parlourn,ta dauko abun sallah ta shimfida mata sannan “Bismillah anty”….. Bata kulata ba ta tashi ta tada sallah………

Shigowar Dr Deen da alhaji ne ya razana mama,hankalinta ya tashi,budar bakinta keda wuya sai tace “Alhaji Ina Doctor din,ko be karaso bane”….. Hade rai yayi yace “bagashi a kusa dani kina gani ba”….. A kidime ta sake cewa “Toh ai ba wannan bane family Doctor dinmu ba”….. Ko kallonta alhaji be sakeyi ba,ya dago yana kallon deen da gabadaya ya zama absent minded…… Shiko Deen tinda ya shigo yakebin occupants din parlourn da kallo yana tinanin ta ina ze hangota,abinda yakeji a cikin ransa na kara basa assurance din cewa lallai tana parlourn nan,amma abin mamaki be ganta,kalle kalle ya cigaba dayi saiya hango wata a edge din parlourn ta juya baya tana sallah,hakanan kawai ya samu kanshi da bin bayanta da kallo ko kifta ido bayayi,shidai burinshi kawai ta jiyo yaga wacece ita?,ko ita din yake nema?….. Alhaji ne ya katseshi da cewa “son karaso mana,tinanin me kakeyi haka at this young age”……. Sai kuma yace”wai ina Fatima Zainab ne? Tinda nashigo banganta ba”……. Momma ta bashi amsa da”gata chan tana sallah”….. Murmushi yayi yace “Daughter case,ta dauko rigima kuma ko a jikinta ta barmu ta tafi tana gaida ubangijinta”……

“Son, sample din abincin nan nakeso ka dauka,ka duba if there’s any harmful abu a ciki pls”…… Murmushi Deen daya kara shiga rudanin jin wani suna waishi ‘Fatima Zainab’ yayi,toh tayaya zaace mutum yanada sunaye guda biyu masu asali?Kuma tabbas wacce ke sallahn nan ce me sunan tinda yaji ance tana sallah,sai hakan ya kara mishi curiosity akan wanda yake ciki,yaji lallai yana san ganin me sallahn nan,amma saiya daure ya dauki sample din kamar yanda alhaji ya umarce shi,sannan ya tafi domin tsayawa ta idar ba huruminshi bane…

Fitarsa keda wuya ta sallame,ta karaso inda daddy yake tana cewa “Toh shi wannan wani irin shashashan Doctor ne,harya gama binciken?”……. Girgiza kai daddy yayi yace “Kai daughter haryanzu wannan gajan hakurin naki baki dena ba?,toh ya dauki sample din abincin ya tafi dashi lab domin ya bincika,sai mujira result din ko” Tabe baki tayi batace komai ba tasamu guri ta zauna…… Suko gabadaya mutanen parlourn sunyi jigum kamar shukar da akayi ruwa ya dauke kam,kada ma mama taji labari dan tafita hayyacinta kamar ace kyat ta zura da gudu,sai sake sake takeyi a ranta shikuma wannan doctor daga ina alhaji ya samoshi?. Karfa yazo ya tona mata asiri a banza,ya bata mata nomar data dade tanayi, gaskiya dole ma tayi wani abun…… Tashi tayi da sauri,ta manta cewa da mutane a parlourn saboda tsabar rudewar da tayi,ta rasa ina zata saka ranta taji dadi…. Daka mata tsawa daddy yayi yace “koma ki zauna” ganin yanda duk ta rikice….. Da sauri ta koma ta zauna tana rarraba ido kamar wata tababbiya…….. Kallon mama Fatima Zainab tayi tace “ko ni ko ke a gidannan yau” sannan ta kalli daddy tace “nifa yunwa nakeji, zanje part dina in nemi abinda zansa a cikina,dan ban yarda da mutanen gidannan ba”….. Gyada kai daddy yayi yana mata addu’ar shiriya aranshi……. Batako sauriri me zece ba ta ficewarta..…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button