Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 9

Sponsored links

Da sallama ciki ciki tashiga main parlour din,tana bin ko ina dawani mugun kallo,Abdul ne yafara hangota,aiji yayi kamar ansashi a aljannah da ganinta,ganin kuma tacigaba da takowa yayi sauri ya dauke kai…… Suko sauran occupants din parlourn ji sukayi kamar an aiko musu da mala’ikan mutuwa,sunsan zuwanta sam babu alkhairi a ciki,haka dai suka daure kowa ya daura murmushi a fuskarsa badan yasoba……. Zama tayi a daya daga cikin kujerun falon tana dora kafa daya kan daya,ai da sauri yanmata guda uku dake parlourn suka sube kasa suna gaisheta saboda gudun abinda zeje ya dawo…. Ko kallonsu batayi ba bare tasan Allah yayi halittarsu a wajan,amma haka suka tashi jiki na rawa suka cikamata gabanta da kayan ciye ciye…. Abdul na kokarin gaisheta shima ta daga mishi hannu…

 

“Welcome my daughter” ta tsinto muryar momma na fadin hakan,kallon kasan ido tabita dashi batace komai ba….. Budar bakin mama itama sai tace “Daughter wata sabon gani yau kintina damu”….. Ko kallon mama batayi ba sai girgiza kafa datakeyi akan kujera……… Momma bata gaji da halin ko inkula data mata ba,ta sake cewa “Daughter ya Khaleel,kuna waya dashi kuwa? Sai a lokacin ta dago ta kalleta ido cikin ido,budar bakinta keda wuya tace “Ni zaki tambaya danki? bakisan inda yake bane?” Karab sai mama tace “In banda abinki daughter meye toh dan an tambayeki masoyinki? Hade girar sama da kasa tayi tace “Ba ruwanki,ni tashima ki dafamin indomie dan bazanci jagwalgwalan da ya’yanki suka ajyemin ba”……… Jiki na rawa mama ta tashi,tanajin wani farinciki a ranta,tana ayyana yanda zata jefi tsuntsu biyu da dutse daya,this is the perfect opportunity that she has been seeking for,yau kuma Allah ya bata so bazatayi wasa dashi ba…………..

 

Bata taba bata lokacinta akan tsarawa wani girki irin na yau,duk da indomie ce kawai amma sosai ta baje basirarta yanda kamshinta mutum yajima kawai zai gigice bare kuma ace ya kai baki,sosai ko gidan ya dime da kanshi kamar wani liyafa akeyi,sadap sadap takoma taki ta dauko wani abu a leda batareda kowa ya ganta ba…..Saida ta tabbatar babu wanda yake ganinta sannan ta kwance ledar tayi injecting content din cikin syringe din zuwa indomie,tana wani farin ciki a ranta,tasan dai komai yazo karshe a yau dinnan,gwara mayyar yarinyar nan tabar duniya kowa ya huta………

 

Fitowa tayi tana murmushi ta ajye well ganished indomien akan center table din dake kusa da Fatimah Zainab,sannan ta kalleta still murmushi daure akan fuskarta tace “Done daughter” …. Dagowa tayi zatayi magana kenan sukaji sallamar daddy…… Kowa na parlourn ya amsa amma banda ita,karasowa yayi yana mamakin ganinta,sai ya boye mamakinshi yace “Daughter yau kece a gidan haka,toh ya karantu,I hope kina maida hankali sosai”….. Kallonshi tayi tace “Not really” kamar batasan magana…… “Haba daughter nafiso kimaida hankali sosai domin ki zamo wata a rayuwa” Bata fuska tayi tace “Ni duk mubar wannan maganar,dama gurinka nazo,so nake amin processing visa zantafi US nan da one week” ….. Cikin mamaki yace “me zakije kiyi a US?”…… “Gurin danka zani” Ta bashi answer kai tsaye…… Zama yayi a chair din dake facing dinta sannan yace”Amma daughter ba soon zaku fara exam ba,why not bazaki bari in kun gama ba,yanada kyau ki maida hankalinki sosai akan jarabawarki,kuma bakima fadamin takemaimai me zakiyi a US ba”…… Hade girar sama da kasa tayi tace”Haba daddy ya zaka dinga min irin wannan question a gaban yara,kuma ni ba abinda zanyi a US,danka kawai nakesan gani?” ….. Girgiza kai kawai yayi yace “It’s alright,I’ll send you the details when the visa is processsed,sai ki zama cikin shiri”……. Batace komai ba ta bude murfin hadaddan unbreakable din da aka zuba mata indomien a ciki,take ko kamshin ya daketa,sai kuma ta fara bin abincin da kallo,smirking tayi tace “Mama bismillah fara ci” Daddy haryamike yaji mama na cewa “Bangane in faraci ba” Sai ya dawo ya zauna incase in wani fitinar fatima zainab zata tada ya tareta,dan sarai ya sani duk sanda tazo saita hada wani gurmi take tafiya……

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button