Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 75

Sponsored links

Tasowa mai gadin gidan yayi da sauri ya leka ta karamin gate dan yaga su waye……

Sameer ganin mai gadi ya leko ya sasa fitowa daga mota yazo ya samesa yana tambayarsa ko mai gidan na nan…..

“Eh yana nan”…

Mai gadin ya basa ansa…

“Toh ko zaka iya mana sallama dashi?”….

“Toh shikenan bari in sanar masa, amma wa zaa ce?”…

“Kace masa sameer ne”…

“Toh ina zuwa”…

Gyada kai Sameer yayi yayinda mai gadin ya shiga ciki dan neman izinin Deen….

Dai dai kofar main parlour sukayi kicibus da Deen daya fito jin karar horn sosai…..

Gaishesa mai gadin ya karayi kamar ba dazun suka gaisa ba, be amsa ba yace masa;

“Ya akayi”

“Sallama akeyi da kai yallabai”….

“Waye?”…..

“Yace ace sameer”….

Dan jim Deen yayi yana tinanin su mami dake ciki, baze so sameer ya hadu da mami yanzu ba dan yasan haduwarsu bazatayi kyau ba, sannan bayasan sameer yaga yarinyar, so yake kawai ya maida ita gidansu batareda sameer ya biya bukatarsa ba, sai kuma yasa masa ido karya kuma kai mata hari…….

“Kace masa ina zuwa”…….

Deen ya fada yana komawa ciki…….

Juyawa mai gadi yayi dan ya isar da sakon…….

Sameer na hango fitowar Deen ya kalli mutumin dake gefensa yace;

“Gashi ya fito, muje!”,,,

Kallon Deen yayi ya girgiza kai yace;

“Bana fadamaka yana nan tareda yarinyar ba? Yanzu ka yarda dani?”…..

“Sosai, muje mu samesa”…

“No basai naje ba, duk abinda zece maka karka yarda dan tana cikin gidannan”……

“Toh nagode”….

Fita daga motar Sameer yayi ya karasa inda Deen yake a tsaye a bakin gate……

Mika masa hannu Deen yayi suka gaisa sannan yace;

“Ashe kana tafe”…

“Ka fadi haka mana, wallahi Deen ka bani mamaki, ashe kaima sonta kake shine kake raina min hankali tuntini?”……

Cewar sameer rai a hade…..

“You’re very stupid for saying this! An gayamaka kowa shashasha ne irin ku da zaka zo kana gayamin maganar banza daga taimako, kai yanzu kana tinanin zan iya san yarinyar da kuke hauka akai? Toh ka bude kunnuwanka da kyau kaji I can never stoop so low and love the fucking girl you’re talking about, now get out of my sight”…..

Deen ya fada cikin zafin rai kamar ze mari sameer, dama yana neman wanda ze saukema bacin ran dayake fama dashi sai ga sameer yazo masa da maganar banza……

Ganin yanda Deen ya fusata yasa sameer kama kansa, dama ba wani yarda yayi da zancen ba, amma kuma abinda yake daure mishi kai ya akayi yaga Deen a gidan kamar yanda wancan ya fada?…..

Dafa kafadar Deen yayi yana fadin;

“Calm down man, abin be kai haka ba, I guess i misunderstood, honestly ba laifina bane wani ne ya fadamin haka”…

Nan ya kwashe duka yanda sukayi da wanchan ya fadawa Deen….

Jinjina kai Deen yayi yace;

“Ya yake”….

Describing dinsa yayi kamar yanda Deen yayi expecting, ya kuma fadamasa tare sukazo, yana cikin mota ma……

“Muje na gansa”….

Karasawa gurin motar sukayi, sameer ya zagaya ta inda mutumin yake zaune ya bude kofa yana mishi magana ya fito……

Shiru yaji baa amsa ba….

Lekawa ciki yayi yana tinanin ko ya chanja guri ne, sai yaga wayam, sama da kasa kuma ya nemesa ya rasa a motar…. A birkice ya shiga duba ko ina a motar Deen na tsaye yana binshi da kallon banza….

Ba karamin tsorata sameer yayi ba da ganin baiga mutumin a ciki ba, if he can recall ya fita ya barsa a ciki kuma shida Deen na facing inda motar take so bayanda zaayi ya fita be sani ba, abu kamar magic?…

Dage kafada Deen yayi yace;

“How can you even believe a stranger? Dan iskan ai da yasani ya tsaya danaci ubansa a gurinnan, Well zan baka shawara karka kara bawa shedaninchan face if not kai zaka kwan ciki, ruwanka kuma ka yarda dani ruwanka ka yarda dashi”…..

Cikin zaro ido dan harga Allah har lokacin a tsorace yake yace;

“What do you mean by shedani?”……

“You’ll see for yourself if you keep on believing him har kana zuwa kana min shouting, kaga bacewar nan dayayi? Kadanne daga cikin abinda zaka gani, just give him chance and see”…

“Boss why’re you doing this to me? Kana nufin ba mutum bane, stop giving me uncompleted statement pls, bakaga yanda na tsorata ba wallahi”….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button