Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 74

Sponsored links

Ba karamin shock sameer ya shiga da jin wannan mummunan labarin gashi dama yayi mugun mafarki akan hakan…. Daurewa yayi cikin yarda da Deen yace;

“Karyane ni nasan Deen bazeyi haka ba, kuma Deen bashi da gida a abuja, dacemin kayi yana chan ana dauramin aure sai na yarda, tukunna ma kai waye da kasan duk wannan?”…..

“Sanin ni waye baze maka amfani ba, abu daya nakeso shine ka yarda da abinda na fada ni kuma zan taimaka maka ka samu yarinyar dan tafi dace wa da kai akan shi”….

“Toh meyasa kake magana kana dariya, sannan kuma tayaya zaka tabbatarmin da abinda kake fada?”….

“Karka damu da dariyar dana keyi haka yanayi na yake, ko yanzu kace in kaika inda ya kaita zan kaika ka tabbatar ma idonka abinda na fada maka”…..

“Naji, muje!”…..

Dan dakatarwa Umm tayi da taba kafar tana kallon wani black dot a tafin kafar fatima zainab, dagowa tayi ta kalli Mami tace;

“Itace kikeson nagani da sukayi accident da Saif?”….

“She’s not alright wallahi, kamar harda jinn a lamarinta kuma, kamar ma aurenta sukayi”…

Dariya sosai Umm tayi dan dama bawai tayi wani fushi dashi sosai bane, lesson kawai take son koya masa, sai kuma Allah yasa abinda suke zata ba hakan bane, duk saitaji hankalinta ya kwanta, tace;

“Allah bazesa ba, wannan wani kalan mugun fata ne haka? Dan baka sonta sai kace aljani ya aureta, ni wallahi taban tausayi, I’m in love with her already, a ina iyayenta suke?”…..

Ta fada tana shafa fuskar fatima zainab dan ita haka Allah yayita da son mutane, kowa tagani ya mata tana sonsa, shiyasa she’s every body’s fav ba kamar mami ba that is kinda bossy….

“Hmmm shikenan tinda baki yarda ba, karma ki wani sota dan wallahi da kanki zaki tsaneta inta fara haukarta, nifa bansan……”

Be karasaba mami ta daka masa tsawa tace;

“Shut up my friend! Koda yake lefin ki ne, yanzu harkin manta da tarin laifuffukansa kina masa dariya, toh wallahi zakaci gidanku, now tell me what’s the essence of the face mask da har kasa wani a hatsari?”…

Shiru yayi bece komai ba yana sauraranta, ta cigaba da fadin;

 

“Ashe you’re this heartless bansani ba? Yanzu imagine an turo wani yazo ya kasheka, haka zaa kashe wanda bejiba be ganiba saboda yana talaka? Shikenan kun maida talakawa wa’yenda busan abinda sukeyi ba? Haryanzu kaki dena wannan I don’t care attitude din naka ko?”….

 

“Mami ba haka bane, I was just….”

 

Wasu lafiyayyun maruka ta sauke masa guda biyu masu rai da lafiya, tace;

 

“Ba haka bane a ina? Well I don’t blame you barewa bazatayi gudu danta yayi rarrafe ba, a gurin ubanka ka kwaso duk wannan banzan halin aka renamin hankali wai you have empathy issue medically, I’ll make sure I deal with you regardless of your so called issue, yanzu kuma zamuje ka karbi position dinka ayi freeing bawan Allah”…

 

“Mami please, ki barni koda na yau ne, I promise you gobe zan koma, idan ta tashi bananan you can’t handle her wallahi”….

 

Deen ya fada yana kokarin controlling kansa dan jijiyoyin kansa har sun fara fitowa alamun ze iya birkice musu anything soon, shi kuma bayasan hakan ya faru amidst wannan critcal situation din”…

 

“Kaji na rantse wallahi Deen sai ka koma a yau dinnan, shima kuma sameer zezo ya sameni, bani kuka hada baki kukayi fooling ba?”….

 

“Mami kona koma saina dawo, she’s in danger koyaya na matsa kusa da ita zasu cutar da ita?”

 

“A matsayinka na ubanwa a gurinta? Uba ko miji? Kasan Allah ka fita idona in rufe Deen, bansan yaushe ka zama fitsararre haka ba, imagine!”…

 

Mami ta fada tana dafe kai, mamaki take wai Deen ne yake gaya mata magana kai tsaye akan wacce yayi claiming bayaso, yes tasan shi da rashin ji amma duk wani abu daya danganci mace bayaso shiyasa take mamaki sosai yanda ya nuna damuwa akan wannan…..

 

“A muslim brother, mami kefa kike gayamin musulmi dan uwan musulmi, ina taimakon mutane, so please let me be with her”…

Mami zatayi magana kenan sujaji karar horn din mota da mugun karfi, wanda ko tantama basayi a bakin get din gidan ne!!!!!

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button