Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 81

Sponsored links

A nitse suke tafiya motar Deen a gaba sai tasu Mami dake biye dashi a baya, musamman mami tace ya shiga gaba dan suna ganinsa kar suce ya biyosu a baya yayi wata hanyar yanda ya nuna musu bayasan komawa dama…..

 

Minti minti Deen yake juyowa ya kalleta gabadaya zuciyarsa a dagule, shi bawai bayasan komawa prison din bane a’a so yake ta farfado ta fadamasa WACECE ITA? sannan ya kaita gidansu ya musu kashedi akan rashin kula da ita gashi ana so a cutar da ita….

 

 

Haka ya cigaba da sake sake har suka karaso prison, parking yayi yaki fitowa daga motar saima juyawa da yayi yana kallonta, nan wani tinani yashiga ransa kan meyasa koda yaushe take kunshe cikin hijabi? Kodai akwai wani abun da take boyewa ne? Shifa yanzu baze iya yarda da yarinyar nan ba, sai ya fara dana sani da be cire hijab din gabadaya ba ranar da ya mata allura, sai kuma yaga ai yana cikin tashin hankalin haukar data dingayi ranar, shi ko kallonta beyiba daya dage hijab dinta, amma zeyi maganinta dan sai ya gano me take boyewa, hardasu hand gloves da socks tsabar munafurci?…

Umm ce ta katsesa da fadin

“Ya kayi zamanka a ciki kuma, fito mana”….

Fitowa yayi yana addu’ar Allah ya dorasa akan Umm ta tayasa bawa mami hakuri a barsa ko zuwa gobe ne.. Cikin fuskar tausayi da damuwa yace;

“Umm na yanzu dawo dani kukayi da gaske?”…

Ba yabo ba fallasa tace;

“Ga zahiri ka gani”…

Harara mami tashiga aika masa batareda tace komai ba, Umm ce ta zaro ido itace;

“Ikon Allah wato fata kake mata su dawo kenan? Anya saif wannan taimakon na tsakani da Allah ne?”…

“Wallahi tsakani da Allah ne, ni nasan basu gama tafiya bane, ina ganewa idan aljanu na jikin mutum”.

“Yaushe ka zama sheikh bamu sani ba? Kafa ji tsoron Allah saif!”…..

“Ke kika tsaya kina kulasa ma yanata zuba miki shashanci, mu zaka maida wanda basu san abinda sukeyi ba, yaushe ka fara harka da aljanu bamu da labari?”…..

Sai a lokacin mami tayi magana….

Shiru yayi yana shafa gemu kamar wani ustaz, ya rasa meyasa yake sakin layi akan yarinyar, idan yayi kokarin billewa wani gurin sai yaga ashe kama kansa da kansa yayi, in banda haka shi meya hadashi da gane masu aljanu? Bema taba yiwa wata karatu ba sai a kanta…..

Gyaran murya mami tayi tace;

“Ka bude kunnuwanka da kyau ka saurareni sannan ka gayamin iya gaskiyarka, hakan ze iyasa na maka sassauci, sannan inaso ka sani maganar nan daga gurinnan ba zaa kara tadota ba, ya rage naka ka fadi gaskiya”…..

“Ina ji”….

“Are you in love with her? Dan wannan rawar kafar da kakeyi akanta ba kalau ba, so tell me kana sonta ne?”…..

“Mami wani kalan tambaya ne wannan?”…

“Bansan dogon surutu, just tell me yes or no?”….

“NO!”….

“Good, Umm ki zama witness even though kema kin masa same question, we’re not coming back to this, that no will be forever!! Wallahi wallahi baza a sake tada maganarnan ba!!”……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button