Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 128

Sponsored links

Kamar yanda labarin ya isa kunnen kowa kuwa yaje ga Malikat Bushirat din da take zaman tsara yanda zatai fitar da wanna abinci bisa tsarawar uwa kamar kowace shekara. Ba kuma a bada abincin ma sai bakwai da azumi, sai kuma gashi yau ana gobe saka ran daukar azumi za’a fara rabon. Kayan da aka fitar kuma sun ninka wanda ita take sakawa a fitar sau dari. Dan duk wani abinci dake shekara ta uku a cikin bital mali Iffah tasa an fito da shi ana da kasa a hannun wakilan. Su kuma kasancewar matasa masu zafin nama da son dama su nuna tasu baiwar amma basu da wanna damar sun bata goyon baya dari bisa dari, duk da kasancewarta karama a shekaru kuma sun bata girmanta matsayin Zawjata-almilk, to kwarjini da cikar kamalar ta da barazana ma bazai bari ko kaso kawo mata wargi ka iya aikata hakan ba.

Tsaf numfashin Malikat Bushirat ya dauke na wucin gadi lokacin da Jazaa tazo mata da mummunan labari. Ta wani zuba idanunta kamar mai son gano gaskiyar maganar a jikinta. Kafin ta yunkura ta mike cikin wani irin zafin rai ta shiga bedroom din ta. Cikin kankanin lokaci ta canja shiri, tana kokarin fitowa Jasrah ta shigo dakin da sallama, dan tunda aka sallamota da ga asibiti nan sashen ta dawo take zaune, a kallo daya datai mata ta fahimci bacin rai dake tattare da ita. Itama yanzu take jin labarin komai a bakin hadiman sashin, dan haka ta biyota daki sanin yanzu yayar tata zata birkice. Ita mamaki take da yanda gaba daya yanzu wasu halayenta ke neman canjawa. Tunda ta dawo sashen kokarin ganin ta fahimtar da ita wacece Iffah take amma taki fahimtarta, gashi kuma yanzu Iffahn ta sake dangwalo wani al’amarin.

“Akia Please kiyi hakuri, zuwanki wajen yarinyar nan a yanzu bashine mafita ba, sai dai maya zubar miki da mutuncinki. Ni a ganina nemanta ya kamata kiyi bayan tabar wajen sai muji dalilinta na zartar da hukuncin da kece ke zartar da shi, ko kuma ki tuntubi Abni kiji tunda dai bazatai komai bada saninsa ba”.

Ta fada a zafafe kamar ma bataji mi Jasrahn ta fada ba. Cikin dakewa itama Jasrah tace,”Bazan barki ki fitaba gaskiya Akia, kiyi tunani abinda kike son aikatawa. Akia na miya canjaki haka? Bayan kuma a baya ba hakan kike ba. Karfa ki manta shekaru kusan hudu muna kuka akan matsalar dake zagaye da mu ta mutuwar matan Abni, amma a yanzu UBANGIJI ya kawo mana iyakar komai, a kanta komai ya canja har mutane suka fahimci makarkashiya ake masa sabanin da da shi kai tsaye kowa ke zargi. Kamata yay mu rungumi yarinyar nan muyi farin ciki da kasancewarta mata ga danmu bawai bore ga duk yunkurinta ba. Matsalarmu da ita dama can akan abinda muke zargin ta aikata ne, amma yanzu mun fahimci ba haka bane ba, to mizaisa bazamu manta komai ba mu maidata komai dinmu kodan farin cikin da yaronmu ke samu da ga gareta.

Tassss! Kake jin saukar lafiyayyen mari a fuskar Jasrah, idanu kawai ta rumtse tana mai kauda kanta, yayinda Malikat Bushirat ke wani irin huci. Abune da bai taba faruwaba, dan ko sanda Jasrah a karama bata taba dukanta ba, shagwabata tai kamar yar data haifa ba kanwa ba, ta kyautata rayuwarta tai mata raino kamar Kwai a cikin cokali. Idanunta da sukai jazur ta bude, ta dan girgiza kai tana murmushi mai ciwo. “Zan iya amsar duk hukuncin da zakimun Akia dan ke uwa ce a gareni ba yar uwa kawai ba. Amma why bazan taba barinki ki zubar da mutuncinki ba”. Tana gama fada ta zare key din kofar ta fice da sauri ta maida kofar ta kulle

gaba daya. Duk kiran sunanta da Malikat Bushirat keyi cikin karaji batako kulata ba tai shigewarta dakin dake matsayin nata a yanzun tana hawaye. Ita kam ta fara shiga rudani akan canjin halayen yar uwar tata, ta sara mike damunta a yanzu. Anya ba masu son cutar da Eshaan bane suka dawo kanta suka saka kiyayya a tsakaninta da yarinyar nan. Ita kam yanzu ta fahimci Iffah, tanajin kaunar yarinyar a ranta kamar tun a da can farko, matsalar data biyo baya ma a dalilin abinda suke tunanin ita ta aikatane. Amma yanzu kunyar haduwarsuma take ji. Dan bata san da bakin da zata fara rokonta gafara ba. Amma koba komai ALLAH ya sakama yarinyar tun ba’aje ko’ina ba, tunda gashi wanda ta yarda da shi fiye da kowa da komai yau shine kecin amanarta da matar dan uwansa, wannan wace irin mummunar kaddara ce. Hawaye masu zafi suka silalo mata, dan abune dake mata matukar kuna da zafi a zuciya tunda ya faru, ga kunyar fitama da takeyi dan ko hadimai shune suke mata akaikaice matsayin matar mai neman tsohuwar matar Shahan-shan…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button