Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 82

Sponsored links

“Nikam na kasa fahimtar dalilin ka nayin hakan”.

 

Miran Arshaan ya faɗa bayan fitowarsu daga zauren tattaunawar. Wani shegen murmushi Miran Jasim ya saki cike da basarwa. Sai da sukai nisa da sashen Tajwar Eshaan gaba ɗaya sannan yay wata ƴar dariya batare daya kalla Miran Arshaan ɗin ba. Shimfiɗa kenan daga cikin plan b, harinmu na gaba shine ƙulla alaƙa da yarinyar nan, dan na san yanzu abinda zatai yinƙurin farawa shine bincike akan wanene shi”.

“Wai ya akai duk kake sanin hakan?”. Miran Arshaan ya tambaya cikin mamaki. Dariya Miran Jasim yayi sosai da faɗin, “Arshaan Akhi har yanzu kai ɗin yaro ne. Waya gaya maka mai nema yana zaman jiran tsammani. Tashi yake da ƙwanji da zuciya wajen samowa ai. Karka damu da inda na sani, kai dai kawai ka tabbatar littatafan nan da mukai magana kwanaki an kaisu books room an ajiye a daren yau, dan bana raba ɗayan biyu zuwa gobe zata iya bukatarsu”.

Cikin halin ko’in kula Miran Arshaan ya ɗage kafaɗu da tabe baki, sai dai acan ƙasan ransa dariya yake dan shima akwai nasa shirin akan hakan tun randa sukai maganar……

Duk da fuskarsa mai tsananin ɓoye sirrin zuciyace a yau ɓacin ransa sai da ya bayyana. Huci kawai yake faman furzarwa a kai-akai. Dan daga ɗakin meeting ɗin nasu da ba’a samu damar tattauna abinda ya dace ba kai tsaye sama yay can ƙarshen rufin ginin sashen nasa da aka gyara domin hutawa kawai. Ko gaisuwar hadiman dake tsare da ƙofar shiga wajen baiyi ba. Ya jima yana faman kai kawo hannayensa zube cikin aljihun farin wandonsa. Bakajin komai tattare da shi sai shaƙa da furzar da numfashi. Sai da ya ɗan samu nutsuwar da yake bukata ya zaro waya dake cikin aljihunsa. Kira yay, bugu ɗaya kuwa aka ɗaga, batare daya amsa gaisuwar da ake masa ba a kausashe ya furta. “A sakaya min shi, inda babu wani mahaluki da zai taɓa hasashe a kansa”. Yana gama faɗa ya yanke kiran cikin sake tsuke fuska da zuƙa ya fesar…

A ɓangaren Iffah tana tsaka da kai kawonta da ƙullawa da warwarewa itama wani tunani ya sata tsayawa cak. Miƙewa tai cikin gamsuwa, sai kuma ta koma ta zauna bisa wani tunanin da yazo a bayan wanda ya sata mikewar. A kallo ɗaya zaka fahimci tana cikin yanayin da duk wani ɗan ƙasar zaka iya ganin ya shiga sakamakon wannan baƙon al’amari daya shigo musu. Da farko bai lura da ita ba saboda idonsa rufe yake da ɓacin rai har lokacin, sai da ya kai zaune yay ƙoƙarin lumshe ido sai kuma ya buɗesu a kanta dai-dai itama ta kallesan mamakin yanayinsa na yanzun kuma fes a fuskarta. Ita ta fara janye nata shima sai ya furzar da huci mai zafi yana maida nasa ya lumshe kamar yanda yayi a farko.

 

Falon ya ɗauka shiru babu alamar wani zai tanka sai karar na’urorin ac dana tv da har yanzu ake cigaba da nuna al’amarin da yanda hankulan jama’a ke tashe. Kiran sallar la’asar ne ya katse zaman shirun nasu. Iffah ta fara yunƙurawa ta tashi batare da ta ko sake kallonsa ba dan da gaske har cikin rai haushinsa takeji yau. Da kallon ƙasan ido ya bita harta ɓacema ganinsa. Ya ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da maida idanunsa ya rufe. Sai da Iffah tai kusan mintuna huɗu da barin wajen sannan ya mike shima har yanzu da alamar ɓacin rai tattare da shi….

Bayan Iffah ta idar da salla kamar yanda ta tsara tai shirinta tsaf cikin wata doguwar riga mai tsananin ɗaukar idon duk wanda zai iya kallonta. Kamshin data gaje batare da umarnin mai shi ba ta baza tamkar tayi ɓarinsa a jikinta. A cikin dukkanin shirinta babu bijirema umarnin waɗan da tazo wannan matakin a dalilinsu, dan haka kai tsaye tai kiran number Daneen Ammarah. Ana ɗagawa tai sallama cikin sauƙaƙa murya mai nuna ladabi. Daga can Daneen Ammarah ta amsa cike da zumuɗi da nuna jin daɗinta da wannan kira.

“Shahrbano ce da kanta haka?”.

Murmushi Iffah tai mai bayyana haƙora jin sunan da Daneen Ammarah ta kirata da shi. Ta girgiza kai tamkar tana a gabanta. “Mamy zakisa a tsire ni a tsakkiyar daular ruman fa”.

Dariya sosai maganar ta bama Daneen Ammarah. Dan haka ta dara sosai kafin ta tsagaita. “Waya isa ya tsire Ibnati kuma Shahrbano duk faɗin ƙasar ruman. Babu mai wannan power ɗin Ibnati, ko maƙiya sun san kin gagara sai kallo daga nesa, dan kowa ya tabbatar a yanzu ke ɗin ce _Lady of the city_”.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button