Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 32

Sponsored links

Banko kofar tayi ko sallama babu,husna da imaan ne zaune a hadadden parlourn mama suna kallo… Binta sukayi da kallo ganin irin shigar dake jikinta kamar zata club,matar da kullum a hijabi take,mamaki suka dingayi wai dama haka take? Tabdi jan! Lallai anyi halitta anan,sufa sun dauka wani abun take boyewa shiyasa takesa hijab ko yaushe,kullum sai sunyi da ita suna cewa kyawun fuska kawai gareta shiyasa take abunda taga dama… Imaan ce ta kasa shiru dan batasan lokacin da tace

“Kutumar uba! Anty dama haka kike,ya khaleel idan ya ganki a haka ai sai ya suma”…….

Wani wawan mari ta dauke imaan dashi tace

“Dan uwarki ni sa’ar kice da zaki tanka?,ina munafukar uwartaku take?”……..

Husna ce taji abun ya daketa ganin cin zarafin yayi yawa,ace a gaban idansu zata dinga zagar musu mahaifiyar su,kallon fatima zainab tayi tace

“Mudai mamanmu ba munafuka ba……

Bata karasaba taji saukar wani naushi a baki,take bakin ya fara zub da jini

“Dan kaza kazanku zaku gayamin inda mahaukaciyar uwarku take ko saina muku jinajina,yan iska kawai wa’yanda sukasha nonon mahaukaciya”…. Ta fada a hassale

Murya na rawa husna da tinda taji mari take ganin wasu stars na zagayeta tace

“Tatt tana dddaki”

Batace komai ba ta nufi bedroom din mama…

Da karfi ta daki kofar,mama dake baccin nishadi ta tashi a firgice dan ta dauka yan fashi ne….. Dirowa kasa tayi tana kokarin shigewa karkashin gado,ganin ta kasa shigewa dayake katuwace yasa ta futo tana rarrafe,a razane take fadin

 

“Dan Allah dan annabi kuyi hakuri,wallahi alhaji baya…..

 

Fatima zainab bata bari ta karasa ba ta dauketa da wani mugun mari….. A take wani mugun fitsari ya zubowa mama dan harga Allah tayi tinanin yan fashine,rufe ido tayi ta kuma cewa

 

“Wallahi kome kukeso zan baku amma dan Allah karku kasheni,ku tausayamin”…….

 

Wani wawan marin ta sake saukewa mama ganin kamar haryanzu bata hayyacinta….. ai saida jin mama ya dauke na wucin gadi jin saukar wani mahaukacin marin da tinda tazo duniya baataba mata irinsa ba,take ta fashe da wani irin kuka mara dadin sauraro,irin dai kukannan na gardawa…. Sai a lokacin ta dago tana kallan fatima zainab…. Sai kuma ta sake rikicewa dan dai a iya tinaninta tasan ta kone mururus,to kodai fatalwar tace dan dagajin wannan marin kasan bana mutum bane,a rikice baki na rawa ta nunata tana fadin

 

“Innalillahi ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,baki kone ba dama,kardai fatalwarki ce ta dawomin…..

 

Bata bari ta karasaba ta sake bata wasu lafiyayyun maruka guda hutu ji kake,tass tass tass tass…….

 

Wani irin ihu mama ta saki ta mike ta fita a guje,binta fatima zainab tayi itama,parlour mama ta nufa tana tafe tana sakin fitsari,imaan da husna na ganin mama ta fito a guje,suma suka mike,fita daga part din suka soyi gabadaya amma kafin su karasa fatima zainab ta rigasu,ta kuma sawa parlourn key,juyawa da sauri imaan da husna sukayi mama na biye dasu a baya suka nufi sama,binsu tayi a nitse har suka karasa bedroom din dake sama ita kuma ta rufe kofar parlourn sama,husna da imaan ne suka shiga bedroom din dake saman suka kulle,mama ko kafin ta karasa sun rufe kofar kasancewarta katuwa yasa bata iya gudu sosai,gashi dama bedroom daya ne a sama saitarasa inda zatayi… Bubbuga kofar dakin take tana fadin

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button