Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 7

Sponsored links

Da sallama ya shiga part din mahaifinshi kanshi a kasa,fuskarsa a hade……… “Lale lale yaron hajiya,ashe kana tafe shine ba labari?” Ta fada tana mishi murmushi me kyau……. “Yes ina tafe dama,munsame ku lfy?” Ya fada yana dago kanshi….. “Alhamdulillah,wlh munyi missing dinka sosai, kamar wanda aka yiwa abu sai ka tafi kayi zamanka a abuja,haba Deen din hajiya?”…… “Zaa gyara Insha Allah” ya fada yana zama a kan kujera….. “Toh Allah yasa,Allah ya maka albarka son”ta fada tana fita daga parlourn,binta yayi da kallo harta fice,sai gata ta dawo da masu aikin gidan,aka ko cikamishi gabanshi da kayan ciye ciye da abinci….. Be taba komai ba a abubuwan da aka jera har tadawo tace mishi dad na kiranshi…… Tashi yayi yashiga main parlor din dad da sallama a bakinsa,ya hangoshi zaune yana karanta newspaper,sai ya karasa gabanshi ya zauna a kasa…

“Daka sani a gaba baka iya gaisuwa ba bayan sallama? Ai na dauka yau dinma bazaka zoba,you would have seen the very bad side of me tinda baka da mutunci,shashasha kawai wanda besan ciwon kansa ba”…. Shidai bece komai ba yaci gaba da sauraron mahaifin nashi….. “Da izininwa kuma kayi accepting invitation din university din chan?,meya hadaka da lecturing?,so kake kawai ka kaskantar dani kamar wanda ya rasa abunyi? Abunda ya kamata ka maida hankali kayi handling sai kamai dashi kamar wasan yara,ka tsaya kana shashancin da bai kamata ba ko?Toh wlh duk wanda ya mutu saboda gangancinka kaida Allah,kuma I’ll deal with you personally idan naji wani abunda bemin ba,stupid kawai!”………. “Bawai inata magana kamin shiru ba,ina maganarmu ta kwanaki da kullum kake cemin kana nazari kamar wani sa’an ka?”…… “Na amince!” Sai a lokacin Deen ya magantu….. “Good for you,lastly kar in karajin kaje university dinchan,out my friend!” Ya fada a tsawace…….. Tashi yayi yadaga kafada irin be damuba dinnan,ya fice daga parlourn,part dinshi ya nufa straightly,Mom na mishi magana ko kulata beyiba………

 

Yana shiga ya watsa ruwa sharp sharp kamar wanda ake jira,haka kawai yaji kamar akwai wani abu da yake ce mishi yayi sauri,gabadaya kuma sai yaji hankalinshi ya koma abuja duk da yanzu aka gama bashi warning,kunna data yayi yana duba available flight to abuja na ranar,luckily ko ya samu wani nan da 30mins,ai da sauri ya dau abunda ze dauka ya kuma fita………..

Tin dazu yake gaban hotel din a parking space,yana zaune a cikin mota kamar me jiran wani,kamar ance ya dago kawai ya hangota a tsaye jikin irin motar jiya cikin ire Iren shigarta,shi be mayi tinanin ita dince ko a’a ba,kawai gabadaya yaji zuciyarshi ta bushe yau,yaji dole sai ya tunkareta,ya kuma fincike niqab din munafurcin nan datake sawa dan bega amfanin lullubin ba in mutum yana zuwa hotel, toh meye na rufe rufe?, sannan yanaso ya tambayeta wacece ita a yau dinnan ? Sau biyu kawai ya taba haduwa da ita,amma shi kadai yasan irin tambayoyin da yake dashi a kanta,daga shekaranjiya zuwa yau har mamakin kanshi yake yanda ya damu da sanin wani mahaluki a duniya bayan shi be damu da ko kanshi ba bare wani……. Bude murfin motar yayi ya fito,kawai sai yaga wayam kuma,gadai motar nan amma bata a tsaye,kalle kalle ya farayi yana neman inda ze hangota,amma ko giftawar mutum be gani ba……. Dafe kirjinshi yayi yace”Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha,ya Allah idan ba mutum bace karka kara nunamin ita,idan kuma mutum ce ka taimakeni ka sanar dani WACECE ITA!”……….

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button