Hausa Novels and Stories

Idon Naira 7

Sponsored links

Maryamah da zainab ne suka fito kusan lokaci daya suma suna gaida su malam hamisun Wanda bai tsaya Jan lokaciba ko Jan ransu ya sanar dasu malam Adamu dai lokaci yayi rai yayi halinsa ya rasu qarfe hudun asubar yau..

Dan gyara tsayuwa umma tayi daqyar ta iya tattaro yawu ta hadiye a makoshinta tace”

Malam ya rasu????????

Gyada Kai isyaku yayi yana sauke kansa qasa sbd babu abinda zai iya cewa shima sbd mutuwar malam ta dakesa Dan mutumin arzikine mutumin jamaa.

Zubewa Maryamah tayi a qasa tana neman sumewa sukai kanta isyaku na zuma mata ruwa suna Basu hakuri sbd take kowannensu ya rikice da kukan tashin hankali da firgici mai tsanani.

Zainab kuka takeyi sosai mai sauti sbd asirinta yafi na kowa tonuwa rasuwar mahaifinsu.

Cikin qanqanin lokaci a yada rasuwar malam din cikin anguwa da Yan uwa da abokan hulda

 

Take aka fara shigowa ana rarrashinsu umma dake kuka kaman rayukansu zasu fita.

Ahakan akai janaizarsa aka kaisa makwancinsa.

Alh Barr Asad shine kusan jagoran zaman gaisuwar malam din tunda shine tamkar ‘dansa yanzu tunda baida ‘da namiji hakama ba wasu dangi sosai dazasu zauna.

Haka aka share zaman makokin tsayin kwanaki bakwai Zainab na cikin ƙunci da rashin walwala gaba ɗaya ta sake zama wata shiru shiru bata magana abinci ma sai an matsa mata ta ke iya cin kaɗan ta ce ta ƙoshi Bata da aiki sai na kuka duk idanunta sun zurma ta fita a hayyacinta gaba ɗaya, ga rashin me rarrashi ga rashin gata da ke kewaye da ita,

 

dama ƴan zaman makokin ne ke janta ajiki da bata baki yanzu an watse babu kowa daga ita sai su Umma da sam basa bi takan ta suma takansu sukeyi tunda rasuwar ta shafi kowannensu ba ita kadaiba,

Ahankali lokaci yaja har akai kusan wata biyu da rasuwar Dama bikin maryamah din an daga sai umma ta fita takaba Dan haka tuni kowa yaci gaba da rayuwarsa,

Bebar musu gadon komaiba saina gidan dasuke ciki Wanda bawani gida bane babba Dan madaidaicine Kuma bama ginin zamani bane.

Zainab taci gaba da zuwa makaranta dayake Daman ta gwamnati ce batada wata wahalar shaani kafin daga baya ko sati batai da komawa makarantarba Alhaji Asad ya sauya mata makaranta zuwa wata private school mai kyau da tsada.

 

 

 

rayuwarta ayanzu Takoma tamkar Mara komai da kowa tunda Dama Abbansu shine abokinta datake iya zaunawa suyi fira da dariya,yaji damuwarta da duk abinda take ciki,

 

Yanzu duk bame mata wannan Dan haka ahankali Dole tayi qawa daya Nabila a makaranta wadda da ita kawai taye Yar fira yanzu.

Anfara bikin maryamah gidan yacika da dangin umma dawasu tsirarraku daga dangin mahaifinsu dasukazo daga qauye Kuma ahakan har akai aka gama Babu ma Wanda yayi noticing dinta amatsayin qanwar amarya Koda yaushe tana cikin aiki da aike Dan haka har akai aka gama ko zanin sabuwar atampa Bata samu Wanda ya Bata ta daura ba saidai Bayan bikin umma tabata kala hudu acikin tsofin kayan Anty maryamah din Wanda sunyi mata yawa sosai saida umman ta Bata dari uku takai aka rage mata take sakawa dayake kayan Anty maryamah din duk masu kyau ne sbd umman dakuma Alhaji Asad daya tsaya mata.

An gama bikin ne cikin kwanciyar hankali da bushasha don harkar ta masu arziƙi ce sosai kuma ya sakar musu naira sun yi yadda suke so,

Dangin Umma ‘yan Cameron ne Dama Kuma duk wata riyar kudi sun iya Dan haka kudi suma suka hada sosai sukai mata wasu abubuwan na fita tsara duk da Babu abinda Alhaj Barr Asadullah din beyiba.

Amarya maryamah tabar gidansu ta tare a gidan mijinta aka bar daga umma sai Zainab wadda tun yanzu tafara hangowa kanta garari sbd rashin sanin saime Kuma Nan gaba.

Yanzu duk bame mata wannan Dan haka ahankali Dole tayi qawa daya Nabila a makaranta wadda da ita kawai taye Yar fira yanzu.

 

 

 

 

 

Dukkanin nau’in bauta na aikin gidan sai ya sake rataya a wuyarta musamman da bikin Anty maryamah ya gabato gashi dangin umma wasu tun rasuwar abban suna gidan,

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button