Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 86

Sponsored links

Ta dade tana shawagi akan titi kafin Allah yasa tayi shawarar zuwa school, school din da tafi sati nawa bata jeba, if she’s not mistaken ma kamar exam is starting on Monday gashi ko tests batayi, dage kafada tayi alamun ko oho idanma tayi failing……

Suna zaune suna dan hirarsu yanda suka saba duk dare idan suka dawo daga library kasancewarsu yan till day break duk inda 9 tayi sungama karatunsu sun dawo hostel, basa taba karatun dare……

“Nidai wannan unknown girl din ta tsayamin arai wallahi”…..

Cewar eesha dake zaune tana shan tea….

“Ni bansan yaushe kika zama so concerned about someone’s life ba, kina kulata tana wulakantaki amma kin kasa hakura”……

Cewar Umaima dake kwance tana game a waya….

Dariya tayi tace:

“And if you ask me why I can’t say, I think I just like her and she kinda looks like……”

Bata karasa ba sukaga an turo kofar dakin a hankali kamar ana tsoron taba kofar……

Wani tsalle eesha tayi saura kadan ta zubar da tea din hannunta cikin ihu tace;

“Yar halak, yanzu muka gama maganarki, where have you been zaa fara exam in the next three days, kinyi tests kuwa? Gosh you’re so beautiful wallahi, dan Allah ki dena rufe fuskarki”……

Lumshe idanunta da take jinsu kamar gaurashi tsabar yanda suke mata zafi tayi tana jingina da bango, all she need right now is to sleep, gashi wannan tazo tana mata surutun da ko word daya bata tsinta a ciki ba…..

Tun bayan datayi parking a gaban hostel ta balli usuals dinta tasha bata kara gane kanta ba, she’s got so high burinta kawai ta zube a ko ina ne tayi bacci…..

Taimaka mata eesha tayi har kan bed dinta ta kwanta sannan ta rufe mata spot dinta yanda taga tanayi har lokacin bata dena mamakin maganar data mata ba, ba ita kadai ba har sauran mutanen dakin mamaki suke ganin ta kulata yau, so suke suyi magana akan incidence din amma kowa ya kasa summoning courage, tsit kake ji kamar ba kowa a dakin…..

A hankali billy ta dawo kusa da eesha, kasa kasa tace;

“Dama haka take da kyau? Why is she always covered toh?”….

“If you ask me who I go ask? Yanda kika ganta haka nima naganta”….

Saida yayi tafiya me nisa kafin ya fita daga district din, cab ya tsaida ya fadamasa inda ze kaisa..

Tun bayan an saukesa a prison din yake tsaye yana tinanin yanda ze shiga ya dauki wayarsa ya fito sannan yaje yayi abinda zeyi ya dawo batareda sun sani ba…….

Yanke shawarar haura katanga kawai yayi hakan yasa ya nufi bayan building din, luckiky for him ginin bashida wani tsawo sosai, nan da nan ko ya haura sai gashi a compound din…..

Da sanda ya shiga har ya karasa section din da yake, kamar yanda ya zata haka ya gansu yanda ya tafi ya barsu kamar matattu…

Sadap sadap ya shiga duba wayarsa a inda yake tinanin suna ajyewa, saida ya dade yana dubawa kafin Allah yasa yaga wayar….

Daukan wayar yayi ze fita kenan yaga kamar wani ya motsa a cikinsu, da sauri ya matsa gefe yana boye wayar a aljihunsa…….

Sai daya tabbatar babu wanda yake motsi sannan ya sake fita ya kuma haurawa ta inda ya shigo yabar prison din gabadaya……

Saida ya bar area din sannan ya kunna wayar amma taki tashi saboda rashin charji…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button