Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 10

Sponsored links

Sake kallon mama tayi tace”Saifa kinci zanci,do quick yunwa nakeji”…… Hade rai mama tayi ta kuma cewa “Bangane sainaci ba ni nace miki inajin yunwa ne?”……. Kallon daddy tayi daya zama speechless tayi kwafa tace “Daddy ka fadawa matarka taci abincin nan in anason asamu zaman lfy a gidannan”…… Da sauri dan shima bayasan tashin hankali yace “Hafsa dauki abincinnan kici ko one spoon ne a wuce wajan,bansan ana jan magana”…… Kame kame ta farayi ta kafe akan ita fa bazata ciba,daga abin arziki sai a bita da rashin mutunci,Ita kuma fatima zainab ta kafe akan ko taci abincin ko duk abinda ya faru a gidan ita tajawo…… Daddy ganin abin na nema yazama babba yace”Ke husnah dauki kici,tinda uwarki taki ci” ya fada yana kallon daya daga cikin yanmata dake zaune a parlourn, tasowa tayi zata dauki abincin,mama ta daka mata tsawa tace “karki kuskura ki taba abincinnan” …… Haka yace duk sauran yaranta suzo suci,amma dukta hanasu….. Sosai ranshi ya baci da rainin hankalin mama,Itako Fatimah zainab bata kara cewa komai ba tin bayan ta bada warning dinta….. Wani idea ne ya fadowa daddy,sai yace “hafsah idan kika bari nayi bincike akan abincinnan nayi finding out wani abu zan dauki mummunan mataki akanki,gwara tin muna mu biyu kice”…… Sosai gabanta ya fadi amma ta dake zuciyarta na bata assurance din ba abinda ze faru…… Binsu da kallo daya bayan daya daddy yayi,sannan yace”zan kira Doctor yazo yayi taking sample din abincinnan yayi test a ganomin in akwai wani abun a ciki ko babu…….. Ya fada yana fito da wayarshi daga aljihu tareda dialing number Doctor din….. Wani dadi ne ya lullube mama tinda tasan family doctor dinsu ze kirawo,wannan kuma bata da case dashi tinda tare suke kulle kullensu,Infact shiya kawo mata injection dinma………… Katseta daddy yayi da maganar daya farayi bayan an daga wayar “Doctor kana abuja kuwa”? Basuji me akace ba sukaga yace “I have some urgent issues I want you to attend to,pls come to my house now”…….. “Thank you” sukaji ya sake fada….. Murmushi mama ta karayi aranta tana cewa “Allah ya taimakeni ya dawo shekaranjiya,da yanzu saidai a kira wani,haka kawai yazo ya tonamin asiri”…

Tafiya yake da niyar yaje barbing salon domin ya rage gashin kansa,kasancewarsa me tarin suma,shiyasa kusan duk sati sai yaje barbing salon,sai kawai ga kiran alhaji,batareda tinanin komai ba ya juya akalar motarshi zuwa gidan alhaji….. Horn yayi mai gadi ya taso da sauri ya budemishi gate,shiga yayi cikin gidan ya nemi guri yayi parking….. Kiran alhaji yayi a waya yasanar dashi zuwansa….. Fitowa yayi daga cikin mota ganin alhaji na nufoshi,karasowa alhaji yayi ya dafa kafadarshi yace “Welcome Dr Deen,my son”…… Murmushi yayi suka gaisa sosai da alhaji,sannan alhaji ya mishi jagora zuwa ciki……

Tinda suka tinkaro parlourn yaji gabanshi yayi wani mugun faduwa,kuma ya fara jin irin abunda yakeji a duk sanda ze ganta,toh ko ina yaje a abuja saita bishi ne?,to wai ‘WACECE ITA?’ Ya fada yana kalle kallen ta ina ze hangota….. ‘Tabbas haduwarmu bazaiyi kyau ba koma wacece ke!’ Ya fada suna shiga parlourn……………..

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button