Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 144

Sponsored links

Taji a jikinta kasancewar da gaske yunwar take ji,dan itama ruwan kawai tasha da dabino sai dan madara mai zafi da take matukar so a yanzu tunda akasha ruwan. Ta hakura ne tai salla dan tasan in har taci abu da yawa to tabbas bazatai sallar ba barci

zatai. Duk yanda take wani tuttura masa baki na shagwaba bai kulata ba, da taimakonsa sukai wanka a tare sannan suka fito daning room din. Sai da ta tabbatar ta gam harare-hararen kwanikan abincin tsaf duk da tasan bayan sun ajiye babu mahalukin da ya sake shigowa nan sai shi bata aminta ba kai tsaye. Komai a tare ta hada musu, hatta shayi a kofi daya ta zuba duk da kasancewar dan mitsitsin nanne na larabawa. A haka suka dinga cin abincin kowa na ciyar da dan uwansa har sukaje iya inda suke bukata. Falo suka dawo, yana kokarin kuna Laptop din tasa ta fama ta je ta haye cinyarsa tana tura baki.

“Wai nikam kodai computer din nan kishiyata ce?”.

A yanda tai maganar ma sai abin yaso bashi dariya. Amma dai ya gimtse bai yi ba ya dai tsareta da idanunsa kawai. Lumshewa yay ya dan bude tare da tallafo fuskarta cikin tafin hannunsa. A kasalance ya furta, “Ko dai ke ce ke kishi da ita”.

Murmushi kawai yay dan bashi da abin cewa kuma.Sai kawai ya dauka remote ya kunna musu television ya kamo babban gidan tvn kasar. Basu fara labarai ba, sai wani shiri mai suna * ZAUREN MUSULUNCI_*. sannin muhimmancin shirin yasa bai canja ba ya bar musu nan, itako harda gyara kwanciya a jikinsa ta lafe kamar wata mage. Shima sai ya gyara mata yanda zataji dadì sosai hannunsa saman cikinta da duk duniya a yanzu babu abinda yafi so da bukatar gani kamar girmansa da haihuwarsa. Koda wani takaici ya tuno a ransa daya tuna Iffah’r sa nada cikin gudan jininsa sai yaji nutsuwa ta saukar masa..

 

 

 

 

 

Washe garin aka tashi da fatan gain watan salla,Iffah na zaune tana karatun Alkur’ani bayan idar da sallar asuba Tajwar Eshaan ya dawo da ga massalaci. Komawa yay ya dan kwanta dan barcine a idonsa sosai. Ta idar itama tana shirin hawowa gadon yake sanar mata sakonta ya iso yanzu Sayeed Fayzul-haq ke sanar masa. Fasa kwanciyar tai cike da doki ta mike ta hau shiri, shi dai kallonta kawai yake dan ya santa da barcin tsiya amma da ga cewa sakonta ya iso ta fasa yi. Ganin sauri-saurin nata yay yawa a hankali ya furta, “Madam a hankali karki jamin asara abuna baiyi kwari ba fa”.

 

 

 

Ita kunya ma maganar ta bata, dan haka ta juya masa baya tana rufe fuska. Shima sai ya dan murmusa kawai ya lumshe idanunsa. Kirtsawa ta karasa yi ta zo gaban gadon ta manna masa sumba a goshi. Hannu ya kai zai damkota ta zille. Murmushi yayi da kara gyara kwanciya yana fadin (Fitinanniyar yarinya) a zuciyarsa…..

 

 

 

Duk da safiya ce sosai tuni kayan da aka shigo da su cikin manyan motoci kusan goma masarautar ta dauki dumi. Kowa jira yake ya ga da umarnin wa aka kawo kayan, dan abune dai sabo da ba’a san da shi ba, ga kuma wasu kayan da suka dan fitgito sun nuna suturu ne ma. Tuni fitowar Iffah da ga sashen Tajwar Eshaan Sayeed Fayzul-haq da amintaccensa biye da ita kallo ya koma sama, sal kuma ga tawagar matasan masarautar da ta saka suka mata aiki a wancan karon ma sun fito, a gabanta duk sukal rankwafawar gaisuwar girmamawa. Ta amsa musu itama da kulawa fuskarta da murmushi har da yar tsokanarsu wai kwanan nan zata fara saida form din aurar da samarin masarautar ta ga sun fara yawa. Dariya suka shigayi da barkwancin nata. Harda Sayeed Fayzul-haq da ke jin kaunar yarinyar, gata dai karama amma da halin manya, manyan ma sai an tona. Haka ma amintaccen hadimin Shahan-shan na jin kima da girmanta, dan yanda take kula da shugabansa kawai da sakasa farin ciki ma abin a jinjina mata ne. Shi baya ma ganin karancin shekarun sam sal wata kimarta da girma irin wadda yake kalion Shahan-shan da ita.

Ta musu bayani akan kayan suma da za’a rabasu kamar yanda aka raba kayan abincin azumi ne. Akwai kuma kaji da shanu suma zuwa yammaci zasu isa. Sai dai su baza’a kawosu nan ba a kowace jaha aka samar da masu kiwonsu aka siya idan kowane wakili yaje inda zai raba kayan da aka bashi zai amsa. Sai kuma wanda za’a rabama hadiman masarautar suma da nasu daban, sukam harda kudi wanna kuma Sayeed Fayzul-haq ne zai bada su sakone da ga Shahan-shan da kansa

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button