Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 3

Sponsored links

Kamar yanada Malikat Haseenat ta faɗa an sake tsaurara tsaro a ɗakin da Iffah take, bana dakaru kawai ba harda tarin jami’an tsaron da Shahan-shan kawai suke bama tsaro tako ina yayinda ta kasance cikin masu iya bibiyar komai kai tsaye. Shi kansa abincin da ake kai mata a yanzu ya kasance na musamman dake samun saka ido, dan a rana ta biyar da yunwa ta nema mata illa sai dai likita ya shiga ya dubata. Dan dole ta koma cin abincin sai dai bata wuce lauma uku ko kurɓa uku na madara take ta ajiyewa..

A ɓangaren masu faɗa ajin masarauta ana ta cigaba da tattara bayanan da suka kamata ta hanyar bincike. Sai dai tsaiko na farko da aka fara samu shine rasa cctv footage na sashen Tajwar Eshaan da ga asubahin randa al’amarin zai faru har zuwa lokacin isar su Daneen Ammarah da su Miran Jasim sashen. Sai wayar Iffah da itama aka nema ƙasa da sama aka rasa da lap-top ɗinta. Wannan al’amari ma ya kawo ka-ce-na-ce bana wasa ba har takai jami’an tsaro cafke mai kula da ɗakin tsaron aka garƙame. Amma kuma juyin duniya yace bai san yanda akai ba. Hakama hadiman sashen Iffah kaf ɗinsu an tattare, suma kuma sun rantse sun kuma basu san yanda akai wayar Iffah da lap-top ɗin sukai ɓatan dabo ba. Ba kuma suga wani ya shigo sashen ba. Waɗan nan abubuwa na rashin makamar tabbatar da Iffah akan laifin da kowa keda yaƙinin ta aikata ya kawo rabuwar kai da rikici babban akan mata hukunci. Yayinda su Miran Jasim suka sha jinin jikinsu, dan haka suka zama ɓangaren masu nuna kawai a kashe Iffahn. Ɗayan sashen kuma da suka haɗa da zuri’ar Sayeed Khairul-Bashar suka bore akan bincike na har sai an tabbatar a kuma ji dalilinta dan in ma har ta aikata to dole akwai saka hannun wasu a masarautar.

Rikici ne bana wasa ba, dan har takai anyi wani zaman a karo na biyu amma sam babu masalaha daga kowane ɓangare. Ɓangaren kuma dake ganin kashe Iffahn shi yafi sauƙi sune ɓangare mafi ƙarfi dan da yawansu na jikin Tajwar Eshaan ɗin ne. Malikat Haseenat ce kawai ke nuna a dai cigaba da bincike kar a aikata aikin dana sani. Hakama Daneen Ammarah sam zuciyarta taƙi aminta Iffah zata aikata bisa raɗin kanta, idan ma har ita ta aikata ɗin kenan tunda har yanzu babu wata shaida dake nuna itace ɗin ta bashi madarar dan bayan ita suma masu dafa masa abinci da amintacen hadiminsa duk suna a rufe. Ƙulle-ƙullen su Miran Arshaan ne yasa dukan zargin yafi ƙarfi akan Iffah. A yanzu haka kuma sunyi kane-kane wajen sake rura al’amarin da nuna ɗaukar zafi fiye da kowa musamman Miran Jasim daya kasance mai riƙe da masarautar har zuwa samun lafiyar Tajwar Eshaan da ake fata…

Har cikar kwanakin mako babu wani cikakken masalaha akan al’amarin, sai ma ɗaukar zafi da kowane ɓangare suka sake yi. Iffah kuma taƙi taɓuwa bisa jajircewar Malikat Haseenat na sai fa anyi bincike. Wannan kafiya ta saka Miran Jasim da Miran Arshaan kasa zaune da tsaye. Barbushi kuma ya tabbatar musu in har fa Malikat Haseenat na numfashi bazasu taɓa samun yanda suke so cikin sauƙi ba. Dan haka ya basu zaɓi biyu. Kodai su gaggauta kasheta da hanunsu, ko kuma suyi ƙoƙarin tunzura Malikat Bushirat dayin amfani da ita kamar yanda sukayi da Iffah ta kawar musu da ita. Hankalinsu ya tashi, dan kashe Malikat Haseenat abu ne ba ƙarami ba musamman a wannan gaɓar da take taka wata rawa mai banbanci da tasu duk da tafisu kusanci da Tajwar Eshaan. Duk yanda suka tattauna da aunawa sun gafa wannan hanyar mai wahala ce a gare su, dan haka suka zaɓi nufar sashen Malikat Bushirat ɗin domin fuskantar ta kai tsaye. Fatansu zaman ya zame musu jifan tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, dan tunda aka fara rikicin nan Malikat Bushirat taƙi tofa komai ma, ta tattare hankalinta kacokan akan ganin lafiyar Tajwar Eshaan da aka hana kowa gani a masarautar sai ita da Malikat Haseenat har zuwa yau da ake cika kwanaki tara da faruwar komai…….

Yanda take magana cikin fitar ɗacin sauti tana kaikawo a fusace zai tabbatar maka ranta a ɓace yake ƙololuwa. Malikat Bushirat kenan da tun faruwar al’amarin nan babu wanda zaice yaji bakinta duk wannan sa toka sa ƙatsin da akeyi. A yanzu babban burinta bai wuce samun lafiyar tilon ɗan nata ba, batun hukunta wadda ta zama sanadin komai wato Iffah kuwa duk faɗi tashin da ake komai tana sane, sai dai bata shirya saka baki ba a yanzu acewarta akwai lokaci. A tsahon kwanakin nan dukkan wani motsin masarautar ruman a cikin kunenta yake fiye da masu kai kawon. Hauhawa da bunƙasar ɓacin ranta na yanzu kam yana da alaƙa ne da tattaunawar ta da su Miran Jasim, zaman nasu kuma kacokan ya alaƙantu ne ga hana hukunta Iffah da Malikat Haseenat tayi kai tsaye har sai anyi binciken da ta sharɗanta

Irin wannan fusatar ga Malikat Bushirat shine fatansu, dan haka suka dubi juna cikin son danne murmushin kan fuskokinsu. Zama suka gyara tare da sake buɗe sabon shafin abinda suka faro. Miran Arshaan ya sake marairaice fuska mai cike da tsantsar damuwa yana mai duban Malikat Bushirat..

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button