Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 5

Sponsored links

Da sassarfa ya fito daga cikin motarshi,ya fara tafiya da sauri saboda flight dinshi 7:30am gashi haryaga 7 tayi,gashi in be bar garinnan yau ba toh akwai matsala,saura kadan suyi karo da ita,ta maza tayi gefe tana binshi da wani mugun kallo ta cikin niqab din……… Kallonta kawai yadingayi yana mamakin me tazoyi a hotel,dan shi Allah ya bashi baiwar gane mutum,be wani ganta jiyaba amma zai iya rantsewa itace,bama wannan ba ance in zaka sha giya kasha ta dubu,toh mena boye boye bayan kiri kiri mutum yazo hotel,kuma sai yayi shirin ustazai?…… “Hmmm green snake under the green grasses”…… Be gama tinani ba yaji an badeshi da kura,sai kuma ya nemeta ya rasa,a kidime yabi motar da kallo,if he was not mistaken motarnan achan karshe ya hangota,toh how comes ace hartaje tashige anja motar? Impossible!,kodai kuma bacewa tayi? Dan baze manta da encounter dinsu na jiya ba,kawai yaga wayam,”toh kodai aljana ce?” Ya fada yana kara bin hanyar da kallo…… Hanyar ya kuma bi da kallo yana karanto ayatul-kursiyyu a ranshi,sai kuma ya fara tambayar kanshi toh“WACECE ITA?”

 

Toh jamaa kubiyoni a sannu dan sanin WACECE ITA?…. Meanwhile bacewa tayi ko motar tashige?

A guje yake jan motar dan ya santa sarai jinta take kamar ta tashi sama,da kyar ta yarda ta dena driving ma,saboda yanda take driving recklessly,in anyi magana kuma tace ‘who cares?’… Ta riga ta kudurta aranta cewa third encounter dinsu bazaiyi kyau ba,dan sam bata yarda da kallon dayake binta dashi ba,taso tayi taking action tin a second encounter dinnan nasu,kawai sai taga takasa komai,shiyasa ta maza ta ware batare da ta ankarar dashi ba

Gunjin kuka taji yana tashi da dan shidewa daga cikin room din,sallama tayi a zuciya tashiga ciki,kwance ta hango wata a dukunkune kuma da alamu daga gurinta kukan ke tashi,tabe baki tayi ta karasa kan bed dinta ta shige ganin sauran yan room din sai bacci suke kamar matattu,kilama basuyi sallah ba,sai a lokacin ta kula ashe bata bar jakar a mota ba,fitowa tayi tana tinanin ta mishi text yazo ta mayar kota bar jakar kawai a gurinta? Karar shigowar kiran wayace ta katseta,taja karamin tsaki tana duba mai kiran,wani tsakin ta karaja ganin me kiran aranta tace “oh Allah wannan anacin ne Allah ya taimake shi be turo kudin ba yaga rashin mutunci”,tayi kwafa sannan ta bude message box,ai kuwa taci karo da alert din 5m din,ta wurga wayar ciki tana ce mishi dan wahala a ranta….. Katseta eesha dake kudindine tanata murkususu tayi da cewa “Dan Allah ki taimakeni ki dauko min magani na a cikin bag dinchan” ta fada da kyar tana nuna wurin da akayi hanging bags daga chan gefen dakin……

 

Yi tayi kamar bataji ba kuma sarai taji ta,amma ita sam ba ruwanta da abinda ya shafi wani,matsalar tace ba tata ba…… “Dan Allah,dan annabi ki taimakamin” ta sakejin eesha ta fada tana fashewa da kuka da muryarta daya dishe lokaci daya,tana kara dafe mararta dake ciwo………. Tsayuwa ta cigaba dayi,ita bata motsa ba,kuma bata juyoba,a hankali kuma ta fara takawa ta karasa gurin bags din,tashiga binsu da kallo ba tare data tambayeta wanne daga cikin bags din maganin ke ciki ba,a hankali ta gyara zaman hand gloves dinta sannan tasa hannu a wata ash bag,ta dauko maganin tana jujjuyashi a hannunta,ta gama karanta content din tsap sannan ta tabe baki tana ayyana yanda mata suke fama da ciwon mara,ita abunda bata tabayi kenan a rayuwarta,ita da girmanta ma bazata tina yaushe ta taba ciwo ba…………

 

A hankali ta karaso inda eesha take kwance,gabadaya ta gama fita hayyacin ta,for once,at that moment data tabajin wani ya bata tausayi a rayuwa,girgiza kai kawai tayi ta dauko ruwa,ta zuba a cup,ta hada da drugs din tana mika mata,sai kuma hannun eesha ya fara rawa ta kasa karba…….. Zare hand glove din right hand dinta tayi ta ballo drugs din ta tallafo ta,eesha ko najinta a jikinta sai jikinta ya fara rawa,ta fara kidimewa,chan kuma sai taga jikinta ya dawo normal………

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button