Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 10

Sponsored links

Bayan ta kammala cin abunda azmee ta kawo mata kitchen ta mayar da kayan, sannan ta dawo ta shiga toilet ta daura Alwala, ta zura hija bi ta shiga jera salloli, bayan ta kammala ta rufe da zafafan addu’o’i tana nema ma rayuwarsu sauki, tasha kuka ayayin da ta daga hannunta sama tana rokon ubangiji, hawaye na gangarowa a idonta,

Ba ita ta kwanta ba sai cikin dare ya taba, sannan ta kwanta, tare da rungumo pillow a chest dinta kamar yadda ta saba, tabbas ranta na bata cewa Babban yaya bazai wuce gobe ba bai dawo ba, saboda taji wani sanyi aranta, amma bata da tabbacin hakan , sai in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai kuma in hafsat bature ta so hakan, dayake wuka da nama suna hannunta, 😜😜😜

Mutum biyu ne suka san da zuwan su Abba da junaid sbd sunyi receiving call dinsu in d midnight, a time din mu na nigeria jirginsu zaiyi landing around 9:00am,

 

A Wani irin haɗaɗɗen katafaren privet jet ne ya ɗauko su, wanda ya kasance mallakin Surgeon general RAFAYET, ya haɗu fiye da tunanin mai tunani, cikinsa bai da banbanci da hamshaqin parlour wanda yaji tsadaddun furnitures, saboda an ƙawata shi da jigunannun furnitures,

 

Wato Aljannar duniya ce, acikinsa ya ƙawatu, 👌

 

Wasu hamshaƙan leather seats ne acikinsa jigunannun gaske, wanda ko a ido ka kallesu kasan zasu yi tafshi da daɗin zama, masu numfashi irin waɗanda kana zama zasu lumbutse dakai ciki,

A jere suke biyu suna facing ɗin biyu zungura zungura, a tsakankaninsu wani ƙayataccen table ne haɗaɗɗen gaske, mai ɗauke da travel cups wanda abunsha ne acikinsu, tukunna ma shin su wanene acikin jirgin ? 😒

 

tunkan na fara zayyana su zan fara da faɗin tabarakallahu ahsanul khaliqin 😇

 

Haɗaɗɗiyar sura, dogaye ne masu cikakkiyar ƙira irin ta zakuna, irin ta mazan gaske sadaukai kuma jarumai, ƙerarrun gaske, duk inda namiji yakai to su sun zarce nan, komai nasu na kece raini ne ba wasa a tattare dasu babbar harka ne, duk iya haɗamar mace bazata wuce waɗannan handsome stylish guys ɗin ba, buri kowace ƴa mace nesu, a fage na kyau kuwa ba’a magana, ƙarshe ne su, a bangaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka ba, kana ganin su kasan cewa sun wanku da pawns da dollars, fatar jikinsu kaɗai abun kallo ce, su huɗu ne zaune kowa ya hakimce, jirginsu kawai suke jira yayi landing,

3 daga cikinsu suna sanye cikin expensive dress na suits, biyu launin nasu blue ne ɗayan kuma black ne,

 

Mutun ɗaya ne baya sanye cikin suits ɗin nan, shin wanene shi? Jikinsa na sanye cikin V-neck shirt , tayi tighting ɗinsa, white colour yayin da yake sanye da army trouser,

 

Yana da wata irin sura mai matukar rikiɗarwa mai razanarwa mai matukar jan hankali da ƙayatarwa, saboda a halitta dogo ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a buɗe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, ya cika vest ɗin kana ganin zanen ƙirjinsa ga breast ɗinsa sunyi 6ul-6ul ata ciki kana hangensu, daga gani yana gym (motsa jiki) sosai, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, kana gani kasan cewa yana da matuƙar ƙarfi kamar ɗan wrestling (dambe) haka surarsa take, mutun ne mai ji da ƙarfi,

 

Idan muka je wurin tommy dinsa kuwa a shafe yake ba alamar tumbi ko kaɗan, yayi flat, tamkar baya zuba abinci acikinsa saboda ɗamewarsa,

Launin fatarsa fari ne sol irin hasken fatar ƴan korea, natural white kasancewarsa half cast (ruwa biyu) mahaifinsa hausa fulani, mahaifiyarsa baturiya, ya kuke ganin abun zai kasance?

 

A wurin kyau kuwa sai dai muce tubarkallah, domin Allah yayi sa da wani irin ƙayataccen kyau mai matuƙar razanarwa, ko namiji jinsin sa ya kallesa sai ya ƙyasa balle mace, yadda kasan shi ya zana kansa, don duk mun haɗamar bil’ama aka basa damar ya tsara yadda kyansa zai kasance, bazai wuce nasa ba sai dai ma ƙasa da nasa 😯

Komai na halittar jikinsa dogo ne, kakkarfa domin Allah ya wadatasa da duk wani abu da mace zata buƙata ajikin ɗa Namiji!

 

Idan muka koma kan haɗaɗɗiyar suman kansa kuwa mai tsayin gaske wadda ta sauko masa har saman kafadarsa , tasha gyara na musamman ya ɗaure ta, dark brown ce Allah kaɗai yasan nawa ake kashe ma wannan suman wurin gyara,

 

Hatta gaban forehead ɗinsa sumarce a kwance, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haɗe da juna saboda yawaitar suma a wurin, idan muka koma kan idonsa kuwa yana eyelid (kwarin ido) wadatacce wanda ke lullu6e da eyeballs ɗinsa, yana da dogayen eye lashes masu cukowa da tsari, ga kyan gaske

Allah yabasa kyawawan idanuwa ga girma ga su so sexy, farare tass tass masu ɗauke da kwayar ido, blue colour masu shining masu ɗaukar ido,

 

daga ƙasa kuwa dogon hancinsa ne, ba wai irin ziƙau ɗinnan ba, a’a mai tsari dai dai wa daida, daga nan kuwa sai pink lips ɗinsa tamkar ya shafa jan baki, ga skin din la66ansa irin mai squeeze ɗinnan ce,

 

Cikin natsuwa yake daddana laptop ɗin dake gabansa saman table, ƙirar Luvaglio wadda price ɗinta yakai $1 million ne (dala miliyan ɗaya) a naira kuwa yakai 600millions, miliyan ɗari shidda, cikin natsuwa yake daddana ta da zira ziran yatsunsa, hannunsa na sanye da wrist watch kirar piaget emperador temple ce, farashin ta yayi $3.5 million a naira kuwa ba’a magana billions ne ke magana,

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button