Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 62

Sponsored links

Cikin bacci me nauyin daya dauketa takejin wani bakon al’amari da bata gane kansa ba, sam ta kasa tantance wani yanayi take ciki hasalima bata gane meke faruwa ba, kamar dai lips dinta ake tabawa tadai rasa me takeji gashi ta kasa motsawa, haka ta daure tanaji tana gani aka cigaba da mata abinda akaga dama akan lips, jin kamar an shaketa dan har lokacin bata gane abunda yake faruwa ba yasa ta kasa jurewa ta fara mutsu mutsu tana kokarin farkawa amma kuma saita kasa……

 

Jin motsinta ne yasa Deen janyewa da sauri yana ayyana irin karfin jininta, wannan abun da sameer ya shaka mata sai mutum yayi 24hrs be farkaba inba allura aka masa ba shine ita take motsi within few hours? It’s surprising!, sai a lokacin kuma yagane aika aikan dayayi, meya hadashi da kissing yar mutane? Shida yakeso ya taimaketa ya fitar da ita daga gidan kafin wanchan dan iskan ya dawo shine ze bada kansa? dauke idonsa daga kan fuskarta yayi yana istigfari a ransa…..

Shafa lips dinsa daya jike yayi yanaji kamar har lokacin yana cikin bakinta, sai a lokacin yayi realizing ashe babu mask a fuskarsa, dube dube ya shigayi har ya gano mask din a kasan gado, mamaki ne ya kamasa dan ko zaa kashesa besan sanda ya cire mask din ba, he was lost indeed, shima kenan da ba ruwansa da mata couldn’t control himself, toh inaga in sameer ne mayan mata? Kai anya ma be tabata ba? Wani mugun bacin rai ne yazo masa dan haka kawai yaki yarda sameer betaba yarinyar ba, koma dai menene yayiwa kansa alkawari ba wanda ze kara tabata, inta farfado kuma ze tambayeta WACECE ITA? Sannan ya sadata da iyayenta ya kuma basu shawara su mata aure kar a lalata musu yarinya, dan sameer ba kyaleta zeyi ba inba gani yayi tayi aure ba, ze kuma gaya musu karsu bawa khaleel dan duk basu dace da yarinyar ba, gwara su nemi wani nitsattse su ba……

 

Zagaye dakin ya shigayi yana tinanin mafita dan gaskiya bayaso sameer yazo ya samesa be fitar da yarinyar daga gidan ba, toh amma ina ze kaita? “Ka kaita gidanka mana” wata zuciyar ta fada masa haka, gyada kai yayi kamar yana magana da wani, ya yarda da shawarar kaita gidansa dari bisa dari dan it’s the best solution for him tinda ba wanda yasan gidan a friends dinsa, wata zuciyar ce ta kuma ce masa “to amma mami ta sani ai, what if she come looking for you?”….. Girgiza kai yayi yana fadin “no zan fitar da ita daga gidan kafin mami tayi tinanin ina chan”….

 

Wani lissafi ya kumayi yaga alamun komai ze tafi masa daidai , abinda zeyi shine ya kai yarinyar gidansa ya ajye sai ya dawo ya renawa sameer hankali yace shi dayazo bega kowa ba…. “Yes” ya fada yana kokarin daukarta…..

 

 

Daukarta yayi kamar wata yar baby a zuciyarsa yana fadin gata dai a haka kamar a cike amma she’s weightless, kodai batacin abinci sosai ne?, tsaki yaja yana tamabayar kansa ina ruwansa?….

 

Carefully yake rike da ita gudin having body contact da ita amma duk da haka be tsiraba dan yanajin dumin jikinta sosai kamar wanda yake rungume da ita, haka ya daure ya karasa bakin mota da ita….

Bude gaban motar yayi ya zaunar da ita still tana nan a sumen da take, sannan ya kwantar mata da sit din sosai yanda zataji dadin kwanciyar ya kuma gyara mata zaman hijabinta…..

 

Bude gate yayi kasancewar babu me gadi a gidan tinda ba wani zama suke ba, ya fita da motar waje sannan ya kara dawowa ya rufe gate da gidan gabadaya ya nufi mota…..

 

Kamar a mafarki yaga mutum ya bude masa gaban mota harda zira hannu yana kokarin zaro ta…….

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button