Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 61

Sponsored links

Wayarsa ya fito da ita da niyar kiran Deen sai ya tina Deen be fito da waya ba, kishingida ya danyi yana jiran dawowar Deen da good news dan yasan ba shakka shiya tafi da yarinyar…….

Haka Deen ya zauna yana kallonta kamar wanda aka bawa ajiyarta, har lokacin mamaki yake wai shine haka akan mace, macen ma irin wannan da sai a hankali? Yanzu idan wani yaji ai sai y masa mummunan fahimta ya dauka sonta yake, shi ko me zeyi da wannan da daga gani zata basa ciwon kai, bama wannan ba meya hadashi da yarinyar da wa’yanchan mahaukatan ke hauka akanta tsabar rashin class, shi in soyayyar zeyi ai sai ya nemo yarinyar da shine ze zama first and last love dinta, bayasan mace me tarkacen masoya, sannan kuma bayasan reni so gwara ya dauko mace age mate dinsa atleast ta kai 30 ba irin wannan ba da daga gani she’s still a teenager (haba mallam deeni yada jumping into conclusion🙄) tazo tana basa wahala….

Ganin lokacin sallah yayi ya sasa tashi ya dauro alwala, a nan parlourn ya tada sallah a nitse…..

Samun kansa yayi dayi mata addu’a duk sujjadarsa kamar wanda aka bawa kwangilar mata addu’a, abun dariya kuma addu’a biyu yake maimaitawa, Allah ya shiryeta da Allah ya bata miji nagari yaketa fadi harya idar da sallah. Still be hakura ba ya cigaba da mata addu’ar ko bayan ya idar da sallah……

Yana cikin wannan hali yaji ‘tasssss tassss tasssss’ alamun fashewar abu me glass, mikewa yayi da sauri ganin ta dau center table ta buga akan tv, a take tv’n ya fashe kuwa, rasa abunyi yayi ya tsaya yana kallon ikon Allah, wurgi take da duk abinda ta samu a parlourn kamar mahaukaciya sabon kamu, tsabar shock ya kasa motsi bare ya hanata, toh yaushe ma ta farka? Wannan wace kalan yarinya ce haka?….

Ganin ta nufi dining ya daka mata wani mugun tsawa yace;

“Ke wata irin mahaukaciya haka? Daga taimakonki shine zaki zo ki illatamin gida, maza ki jiwa kanki ciwo mahaukaciya kawai”………

Fasa zuwa gurin dining din tayi ta tawo inda yake da gudu, chakumeshi tayi cikin masifa tace;

“Kaine babban mahaukaci for kidnapping me, akanme zaka sato ni ka kawoni nan, I’ll not spare you, saina kasheka!!!!”……

Dariya ya shigayi tsabar mamaki, wai ita wannan masifa takeyi a haka da bedroom voice, lallai ba kanta…….

Hannun data chakumeshi ya cire daga jikinsa yana bin hand gloves dinta da kallo……

 

Duka da naushi ta fara kai masa ta ko ina a jikinsa da karfi ko Allah zesa taji radadin da zuciyarta ke mata ya ragu dan tagama yarda mugune shi tinda harya saceta, ta kuma ci alwashin saita nuna masa he messed up with the wrong person…..

 

Ko gezau beyi ba saima gyara tsayuwarsa da yayi yanda zataji dadin dukansa da kyau, ya kuma gane ta dauka shiyayi kidnapping dinta ne…..

 

Ganin dukan baya mata yasata zura a guje ta tafi kitchen ta dauko wuka da niyar chaka masa ta wuta dan haka kawai takeji kamar ana zugata ta kashesa…..

 

Harta dauki wukar taga gwara ta fara yiwa kitchen din lahani tukunna, nan tashiga masa banna sosai a kitchen din, babu wani abu me glass a kitchen din dabe fashe ba…

 

Jin karar sabon fashe fashe ne ya kara tabbatar masa mahaukaciya ya dauko, bedroom dinsa ya shiga da sauri ya hado allurar barci me karfi ya zira a aljihu, gwara ya mata allura kawai ya huta da wannan masifa, haka kawai daga taimako ya kwasowa kansa masifa…..

 

Bayan ta gama da kitchen din ta fito hannunta rike da wukar tana nemansa a parlourn, ganin bata gansa bane yasata cigaba da fashe fashenta, har dining din daya hanata zuwa dazun saida ta masa lahani yanzu, saida ta tabbatar ta illata komai na parlourn sannan ta fara nemansa shima ta kasheshi ta wuce……..

Fitowarsa daga dakin yayi daidai da juyowarta daidai center dakin daya fito, kama haba yayi yana kallon millions din data masa asara kamar a kasa ake tsinto kudin….. Sai yaji batasu yake ba, he’s after her well-being karta jiwa kanta ciwo…..

Gadan gadan ta nufoshi da wuka boye a bayanta, tana zuwa ta chaka masa…

Saurin kaucewa yayi wukar ta dan yankeshi a hannu take hannu ya fara zub da jini….. Rasa abinyi yayi kawai ya rungumeta yana kokarin zare wukar a hannunta…..

Wani bakon lamari ne ya ziyarcesu duka kowa da abinda yakeji, ita ji tayi kamar an zare mata laka jikinta yayi sanyi sosai amma batadena mutsu mutsu ba, shikuma Deen laushin jikinta ne ya tafi da imaninsa dan Allah ya sani karfin hali yayi ya samu ya zare wukar daga hannunta, ya kankameta kam kamar wacce zaa kwaceta…..

 

Murya chan kasa kamar mejin bacci yace;

 

“Ki nutsu dan Allah, karki jiwa kanki ciwo plssss”

 

Bata kulashi ba ta cigaba da fizge fizge burinta kawai ta kwace kanta daga wannan tight hug din dolen….

 

Tana cikin wannan hali taji an dage mata hijab, bata gama ganewa ba kuma taji kamar an chaka mata abu, kuka ta fashe dashi sosai dan a rayuwarta in akwai abinda ta tsana toh be wuce allura ba, bare wannan allurar batasan ta mecece….

Jin kukanta yake har cikin ransa saidai shine best solution daze taimaki situation dinta, patting back dinta ya shigayi sai bata hakuri yake ba tareda yasan abinda yake fada ba, suna cikin wannan yanayi yaji ana taba kofar parlourn !!!!!!…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button