Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 19

Sponsored links

Deen bai farkaba sai washegari da safe around 9am,bude ido yayi ba kowa a dakin lokacin,bin dakin yayi da kallo,anan ya tabbatar da a hospital yake,sai a lokacin incident din daya faru ya dawo mishi,yanda accident din ya kasance da komai,fincike drip din da aka dauramasa yayi ya daki karfen gadon yace “It was intentional,yes it looks like a set up!,and I’m sure it’s from that demon,I must get her,dole ma insan ko WACECE ITA?,Today!”……

Tashi yayi da sauri ya fito daga amenity ward din,kasancewar mutane nata kai kawo a harabar asibitin yasa ba wanda ya kula dashi,gashi kuma ya maze kamar ba mara lafiya ba,fita yayi daga ospital din gabadaya……. Sai kuma ya fara tinanin ina zeyi tinda ba mota,gashi yaji ba wallet dinshi a jikinshi,infact ba komai ma a jikinshi,luckily ya hango wani branch din bank dinsa,da sauri ya nufi bank din,in ka kallesa bazaka taba tinanin bashida lfy ba dan shi haka Allah ya yishi,mutum ne me mugun dauriya,haka yake jarumi ne a komai nasa,kana kallonsa kaga kakkarfan namiji kuma,gashi ba abinda ya tsana irin zaman asibiti shiyasa kawai ya gudu inyaso ya cigaba da treating kansa,shi bama wannan bane a gabanshi,babban treatment din da yake bukata a yanzu shine sanin WACECE ITA?,tabbas ya yadda ta dalilinta wannan accident din ya sameshi,amma ba gudu ba ja da baya harsai yasan wacece ita,he’ll just get prepared for the worse,yasa a ransa ko ze rasa ransa sai yasan WACECE ITA?……..

 

Blocking wanchan card din yayi sannan yayi requesting sabo,within 15mins ko aka gama aka bashi,withdrawing enough cash yayi sannan ya fita daga bank din…… Bolt yayi ordering ya nufi inda ake siyar da motoci direct,wata mota kirar’Rolls Royce’ ya siya,duk da tarin motocinsa haka kawai yaji bazai iya jira har akawo masa mota abuja ba,clearance akayi da komai sannan aka bashi car key ya shiga ya ja….. Transcorp ya nufa straight hoping ko ze ganta achan….. Yafi 30mins a parking lot yana kalle kalle ko Allah zesa ya ganta,koda ze ganta ta bace shidai kawai ya ganta,amma ina ko alamunta be gani ba,gabadaya sai yaji ya damu,ranshi ya baci,shi haka yake in dai be samu abinda yake so ba sai ransa ya baci,yayi zuciya ya hakura,amma a kanta kamar wanda akayiwa baki ya kasa hakura ya dena bibiyarta,ko yayi zuciya yanzu anjima ze fara tambayar kansa toh WACECE ITA?,shiyasa kawai ya dauki hakan a matsayin kaddararsa……… Ya kuma chanja mata suna from ‘Demon’ to ‘My Fate’…….

Hakura da zama cikin motar yayi ya shiga cikin hotel din…

Wanka yayi ya shiga rama sallolin da ake binsa,yana godewa Allah sanin cewa dad is not aware,dan da sun sani sai dai kawai ya tashi ya gansu a hospital din,kuma yasan straight gida zasu wuce dashi,sai kuma yaji kamar fa yaga mom da dad jiya,girgiza kai yayi yace “No,hallucination ne amma basu nagani ba,in sune ina tashi yau zan gansu,nasan ma basu sani ba,and I’m glad”……….. Fitowa yayi ya fara lissafin ta ina ze fara nemanta………

Sai karfe daya ta farka,shima jin azahar tayi ne,sallah kawai tayi ta sake kwanciya,sai la’asar ta kuma tashi,sai a sannan ta jita garau…… Wanka tayi,tayi sallah,shiryawa cikin wata free abaya tayi,hangloves da socks ta saka as usual,sai nose mask da shades kamar yanda tayi sanda zata zo………

Ko bi takan khaleel batayi ba ta sauka kasa,ta nufi hanyar fita da niyar taje ta ci abinci sannan,tinani ta shigayi to ina ma zata fara,sai kawai ta yanke shawarar duba kitchen din khaleel ko zata samu abinda zataci,tana shiga ko ta tarar da abubuwa dayawa saidai duk basu mata ba,kawai saita fita daga kitchen din…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button