Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 17

Sponsored links

On this very faithful day, bayan ta gama shan fruit a part din daddy sai ya bata sako ta kaiwa momma, ba musu ta tafi part din momma, karban sakon momma da take jin haushin fatima zainab har lokacin tayi sannan tace ta tsaya, tsintsiya ta bata tace ta sharemata parlor dukda tasan bata iya ba so take kawai tagana mata azaba da ayyuka ranar…..

A ranar ne kuma khaleel yayi gamo da ita bayan ya dawo daga tafiyar da rabonsa da gidan kusan shekara hudu kenan, a lokacin dayayi tozali da ita ya kuma fada sonta a take wanda san da khaleel ke mata shine asalin samun yan’cinta a gidan…..

And when the table turns around she make sure kowa yayi reaping abinda ya shuka a gidan daga momma har mama, saida ta zame musu worse nightmare gashi a lokacin daddy ya ninka mata kulawar da yake bata, abun yaso ya bata mamaki ganin yanda yake fifitata akan kowa har matansa gashi har part dinta yamata daban a gidan dukda kankantar shekarunta amma sanin waye daddy tin farko saita watsar da zancen sannan kuma son da yake yiwa khaleel tasan ze iyasa ya mata komai, sai tayi using opportunity dinta wisely ta zame musu fitina da bala’i, take juya musu miji da da’ ba kuma yanda suka iya!!! Sai ta zama kamar dodo a gidan wanda har daddy dayake nuna mata baya rashin kunya take masa in abunta ya motsa, sai sangartarta ya kara yawa dalilin zuba mata masu aiki da khaleel yayi, shiyasa haryau babu abinda ta iya, shaye shaye ko har bunkasa yayi dan har abinda batasha da yanzu sha take saidai baya wani affecting dinta sosai yanzu saboda abin ya riga yabi jikinta, shiyasa batayi mamaki ba da akace kidney dinta is failing, zata yiwu karshenta ne yazo!, da abu daya kawai ta tsira a rayuwarta shine ibada da ilimin addini, duk rintsi duk wuya bata wasa da sallah!!!! Banda wannan she’s a very big zero!!!!

Hmmm

Kukan dayaci karfinta ne yasa takasa cigaba da labarin duk ta fada musu kusan komai gameda rayuwarta……

 

Tinda ta fara labarin Umm take kuka kasancewarta mutum me rauni da tausayi, rungumeta tayi suka hadu sukaita kukan, tashi mami da batasan tana hawaye ba tayi ta hadasu duka ta rungume tana lallashinsu bayan itama kukan take…….

Deen ko yana gefe yana kallonsu, zirgi zirga ya shigayi ya kasa zaune ya kasa tsaye, chan kuma sai ya zube a kasa yayi tagumi yana kallonsu with blank expression, a haka bazaka taba gane yanayin da yake ciki ba saidai shi kadai yasan me yakeji aransa, ashe dama abin tausayin ce ita shiyasa yakejin tausayinta sosai? And he has a lot of questions to ask her right now, sannan a labarinta tace daddy mutumin kirki ne amma bega alamun hakan ba, the fact is that koma menene zeyi finding out, wuyarta kawai ya fara bincike yasan da sannu ze gano komai……Sai ya sake daga kai yaga kuka suke har lokacin sai abun ya basa mamaki ya kuma rena karfin zuciyar mata, abu kadan sai su zauna suyita kuka?….

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button