Hausa Novels and Stories

Hamrah Complete Hausa Novel

Sponsored links

Kwance take akan makeken royal bed d’inta tana latse latse a wayar ta kirar iphone 11 sanye take cikin Arabian gown me shegen kyau ta yana gyalenshi a kanta, d’an banzan hill ne a kafanta, kyakyawa ce ta karshe sossai take da kyau……

 

 

 

“Hamrah plz ki tashi kin san kin ajiye mutane kusan 20mins kenan amma ke kina kwance anan bayan kin shirya ba kyau fa wulakanci” wacce take kwancen ta d’ago idonta a hankali ta sauke akan me maganan…..

 

 

 

Cikin sanyin murya tace “simra plz spare me, Ina ruwanki ni ce fa CEO na company d’in nan so duk abunda nake so shi za’ayi kuma don an jira ni a meeting ba wani abu bane” simra tayi saurin katse ta “to hell with the CEO ko ke wacece a duniyar nan baki da right d’in wulakanta d’an Adam I see no reason..

Cikin sanyin murya tace “simra plz spare me, Ina ruwanki ni ce fa CEO na company d’in nan so duk abunda nake so shi za’ayi kuma don an jira ni a meeting ba wani abu bane” simra tayi saurin katse ta “to hell with the CEO ko ke wacece a duniyar nan baki da right d’in wulakanta d’an Adam I see no reason…..

 

 

 

Wai ke kina tausayin mahaifinki kuwa? Ya d’auki ragamar company d’inshi gabad’aya ya sakar miki amma be huta ba, zan iya rantsewa kin kai 3weeks rabonki da office, baki san me ke tafiya ba……”

 

 

 

Katse ta hamrah tayi tana cewa “ya ishe ni plz, zaki iya zuwa mosque kiyi preaching d’inki bye” ta mike ta d’auki hand bag d’inta da wayanta a hannu ta fice tana zuba mahaukacin kamshi, tana fita ta samu mota biyu a dai dai kofan parlor d’insu da securities d’inta a tsaitsaye, da sauri suka bud’e mata mota ta shige suka fad’a d’ayan drivern yaja da gudu suka fice daga mansion d’in……

 

 

 

Fareed tower suka shiga babban building da ya amsa sunan shi me hawa 25, har gaban entrance na building d’in suka yi parking da sauri suka fito suka bud’e mata fita tayi cikin tafiyanta na kasaita ta shige building d’in…..

Hamrah fareed kenan the great CEO/heir of fareed company, the only daughter to mr. Fareed Ahmad da Barr. Suhailah aryan, ‘yar shekara 22 me ji da kyau da kud’i, mr. Fareed su biyu iyayensu suka haifa da sister d’inshi ummul-khiram sun taso cikin kud’i da ilimi iyayensu ‘yan boko ne na karshe…..

 

 

 

A Harvard university fareed yayi degree d’inshi akan business inda ya koma oxford university yayi masters d’inshi duk akan business anan oxford d’in yayi doctoring degree d’inshi tukun ya dawo nigeria ya fara juya business d’in mahaifinshi, sister d’inshi ummul-khiram ita ma a Harvard tayi karatu zuwa matakin degree……

 

 

 

Sossai suka yi daga da mahaifinta da tace karatun ya ishe ta haka ita aure zatayi, har ta tsayar da wadda zata aura da kyar mahaifinsu ya yadda akan hakan suka shirya tafiya dubai yi mata sayayyan kayan d’akintan daga chan suka wuce Saudi sukayi umura tukun suka d’auko hanyar nigeria inda suka samu mummunar plane crash da ba wadda ya tsira a cikinsu…..

 

 

 

Sossai rashin ya girgiza fareed ya zamana shi kad’ai dama family d’insu ba wani yawa ne da su ba Asalinsu ‘yan kano ne yayinda mahaifiyarsu shuwa Arab ce kuma family d’inta are against auren shiyasa suka yi nisa da ita ba wani sanin su fareed yayi ba………

 

 

Sossai rashin ya girgiza fareed ya zamana shi kad’ai dama family d’insu ba wani yawa ne da su ba Asalinsu ‘yan kano ne yayinda mahaifiyarsu shuwa Arab ce kuma family d’inta are against auren shiyasa suka yi nisa da ita ba wani sanin su fareed yayi ba………

 

 

 

Brr. Suhailah aryan ficecciyar barrister da ake ji da ita a nigeria asalin mahaifinta balarabe ne yayin da mahaifiyarta take ‘yar asalin nigeria jihar kano, tun tana karama Allah yayi wa mahaifinta rasuwa mahaifiyarta hajja nana ta d’auko ta suka dawo nigeria anan tayi krt daga nursary d’inta har secondary tukun ta tafi india anan ta karanci law…….

 

 

 

Sun had’u ne ta sanadin wani problem daya taso ma fareed a company d’inshi wadda yake bukatar lawyer asalin lawyer d’in mahaifinshi wadda ya zama nashi be kasa shine ya had’a shi da suhailah, anan tazo tayi iya kokarinta har suka shawo kan problem daga nan ya fara sonta be yi nauyin baki ba ya fad’a mata, dayake bata da wani wulakanci da ji da kai duk da kyaun da Allah ya mata sbd mahaifinta ta d’auko, duk da fareed d’inma ba baya ba duk kyaun mahaifiyarshi ya kwaso bata wani ja lokaci ba ta amince……

Ansha buki sossai duk da ‘yan uwan angon kad’an kawai suka zo daga chad, zaman lafiya sukeyi kowa na aikinshi, har aurensu ya shekara 7 suhailah bata ta’ba ko ‘batan wata ba, abun ya fara damunta amma se fareed ya kwantar mata da hankali da “haihuwa ai na Allah ne, in da rabon haihuwan se kiga kin haihun karki cire rai ga rahamar ubangiji”……

 

 

 

Kullum nasiharshi kenan a gareta, kwatsam se ga ciki, soyayyar duniyar nan gabad’aya suka d’aura akan cikin nan, ba karamin gata aka tanada ma babyn da be ma san sunayi ba, bayan wata tara ta santalo ‘yarta kyakyawa wacce tayi karo karo na kyau se tazo tafi iyayen nata da suka tsammata kyaun, anyi shagali sossai inda yarinya taci sunan mahaifiyar fareed “HAMRAH” sam ya ki a boye mata suna……..

 

 

 

Anan Abuja tayi daga nursary d’inta har secondary daga nan ta wuce India tayi first degree d’inta anan ta gamu da simra ‘yar india ce ba musulma bace lokacin da suka had’u ita ma ba baya ba wajen kyau haka mahaifinta ana ji da shi a india kuma yana tashen kud’i, bayan ta gama ta koma gida se simra tayi mata maganan masters da farko tace baza tayi ba se kuma ta chanza ra’ayi zama sukayi suka za’bi university da suke so…..

 

 

 

Oxford suka za’ba ba’a b’ata lokaci ba aka sama musu suka wuce duk department d’insu d’aya inda suke karantar business, tana dawowa nigeria ne mahaifinta ya sakar mata ragamar company d’inshi tana son mahaifinta kaman ranta, a lokacin ne kuma kawarta simra ta musulunta, sam bata samu matsala da iyayenta ba sbd sunga takai ta zabi addinin da take so…….

 

 

 

Nigeria tazo ta musulunta tana zaune gidansu hamrah d’in, dr. Fareed ya kawo mata babban malami tana d’aukar karatu a gurinshi sossai ta mai da hankali akan addini wani lokacin hamrah d’in ke daura ta kan hanya don hamrah ba baya ba wajen ilimin addini sossai take da ibada sede tana da dan banzan wulakanci mussaman akan samari ita har yanzu bata ga wadda ya dace da aurenta ba kowa low class ne in kuwa kayi gigin furta mata se ta tsiga maka abunda har ka mutu baza ka manta ba……..

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button