Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 60

Sponsored links

“Give me your parent address da address din hospital din da mamanka take”…

 

Da sauri ya fada mata komai…..

 

“Ok, I’m assure ya baka tips din da mutanen gurin bazasu gane ba, so keep on with it kafin mudawo, karka damu we’ll get you out of here soon!”…..

 

Bata jira amsarsa ba taja hannun mami suka fita dakin….

 

Cikin siyasa suka tamabayi masu gurin yau karfe nawa aka ba Deen waya domin sugane koya tafi dashi ne, bayani suka musu sosai har time din da aka karbo wayar, godiya suka musu suka tafi dan sun riga sun gane abinda suke san ganewa……….

 

Suna fita mami ta kalli Umm tace;

 

“Nasan inda zamu samesa, muje!!!”…..

 

Saida yayi nisa sosai sannan ya rage gudun daya keyi, tuki yakeyi cikin nitsuwa minti minti yana dagowa ya kalleta yana examining dinta, har lokacin karatun qur’ani na tashi a motar……

 

Daidai wani katon mansion ya tsaya, horn yayi akazo aka bude masa ya shiga da sauri……

 

Fadan irin kyawun gidan bata lokaci, duk yanda zaa siffanta gidan baze fadu ba, ba karamin achievement bane ace at his young age yanada mansion kamar haka dako government house albarka, wani in aka fadamasa gidan mallakin Deen ne baze yarda ba….

 

Parking yayi ya fito da ita a hankali yana dagawa me gadi hannun alamun ya dakata basai ya karaso sun gaisa ba……..

 

A kan three sitter ya kwantar da ita yana kallonta, so yake ya koma base gudun kar sameer yazo be gansa ba, sai ya masa karya yace be ganta ba toh amma gaskiya yana tsoron barinta ita kadai musamman idan ya tina encounter dinsu da wanchan mahaukacin, wannan wani kalan dilemma ne? Yanzu wanne zeyi a ciki?….

 

Ya dade yana sakawa da kwancewa be zabi wanda ya kamata yayi ba, karshe dai yaga gwara ya zauna da ita kar wani abu ya sameta kafin ya dawo ko wanchan dan iskan yazo ya dauketa, inyaso daga baya komai zasuyi da sameer saidai suyi……

 

Motar Deen na barin gurin sameer ya karaso, taba gate din gidan yayi ya jishi a rufe, mamaki ne ya kamasa amma be damuba da yake yanada extra key a hannu, be kawo komai ba ya bude gidan ya shiga…. Be bi takan neman Deen ba ya tafi dakin daya ajyeta straight, wayam yaga ba kowa, still be karaya ba ya shiga duba sauran dakunan gidan ko yamanta ya chanja mata daki saidai ko alamunta begani ba…

 

Ba karamin shiga tashin hankali yayi ba na rashin ganinta, gashi bega Deen ba, toh kodai Deen ya tafi da ita wajan daurin auren ne? Wai ko surprise ze masa ya dawo masa da ita a matsayin matarsa, tinanin hakan ne yasa hankalinsa ya kwanta sosai, duk wata damuwar dayazo da ita gidan yaji ta kau, ya kara samun kwarin gwiwar bijirewa mahaifinsa akan abinda yazo masa dashi, sam beji dadin haduwarsu ba dukda bawai yanajin dadin haduwarsu bane dama saidai wannan is worse, tinda yaje yake masa masifa ta inda yake shiga batanan yake fita ba, karshe kuma ya basa umarnin yin wani aiki me wahala da yake ganin ko duniya zasu taru akansa baze iyaba, Hakadai ya amsa masa zeyi badan zeyin ba……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button