Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 18 Hausa Novel

Sponsored links

 

Har aka kare hutun wata biyu Nihad bata nufi hanyar gidan Kamila ba balle nasu gidan, kamar yanda Mumy ke kiranta kullum haka ma Abbanta, a ko da yaushe cikin demanding kudi take daga wajensa kuma ko sau daya bai ta6a hanata ba, da tayi magana xai tura mata fiye da yanda ta tambaya, Umma ma kusan kullum sai ta kirata, duk kuma wannan abun Abba da Mumy na xaton Nihad na Kebbi tare da Kamila, Umma ce kadai ta san Nihad na kano sai kamilar, gaba daya Kamila ta daina xuwa gida a zuwan tana can kebbi, idan da wani abu sai dai Umma ta shirya ita taje gidanta, A kullum Mumy bin Nihad take da addu’a, ta rasa dalilin da hankalinta ya ki kwanciya tun barin Nihad gidan, bata da rest of mind kwata kwata, gashi babu abinda xata iya yi game da hakan, ko me xata ce ma Abba baxai ta6a fahimtar ta ba sai dai ma ya juya xancen, a ko da yaushe ta kira Nihad sai ta mata nasiha a kan ta dai kula kuma banda rawan kai da yin kawaye, sai Nihad tace “Mumy ni da ba kowa na sani ba a garin sannan babu inda muke zuwa, kawai karatu nake ta yi against next semester” A haka dai kullum take gaya ma Mumy.

Ranan wata juma’ah Nihad da kawayenta duk suka shirya xa su je duba wata kawar Zully da tayi rashin lafiya, Naf ke driving din, Husnah tace “Amma fa ku kirata ko an sallameta asibiti kar mu je mu yi wahalar banza” Zully tace “Ai ko dai” wayarta ta dauka ta kira kawartata Yusra ta sa handsfree, tana dagawa Zully tace “Ya kuna asibitin har yanzu?” Yusrah tace “Wani asibiti da aka sallame mu tun jiya, ni kin gan ni a Bristol ina shan Ac, Saurayina Alhaji Muktar ne ya biya kudin kwana hudu sai gashi tafiyar gaggawa ya kamasa yau da safe kuma yace min xai kwana uku a Abuja, sai jibi kudin xai kare shine nace gwara in yi zamana a nan” Zully ta kyalkyale da dariya tace “Me ya fi ranki, to bari mu taho can din kawai” Yusrah tace “Ai ko ku zo, ga abinci ga enough drinks, sannan ga Ac 24/7” Zully tace “To sai mun iso” Tana katse wayar, Naf ta dau hanyar Bristol, Husnah tace “Mu ma muje mu sha Ac kawai” Dariya duk suka yi, Nihad tace “Amma yaushe xa mu fito, kunsan ni bana son xuwa irin wajajen nan in broad daylight” Husnah tace “Mu da xa mu shiga daki mu yi xaman mu meye na wani damuwa” Nihad bata ce komai ba ta ci gaba da danna wayarta, suna isa makeken hotel din Naf ta samu wajen parking, Dai dai nan wayar Nihad ya fara ringing, ganin Abba ne ta ɗan wara ido, Husnah ta kalleta tace “Waye?” Nihad ta nuna mata screen din wayar, Husnah tace “Ohk, bari kawai mu sauka mu tafi ciki, sai ki tsaya motar ku yi waya, idan kun gama ki fito ki kulle sannan ki kirani mu gaya maki room number” Nihad tace “Ohk” Duk suka sauka daga motar, Naf ta mika mata makulli suka wuce ciki, tuni wayar Nihad ya katse sai ga Abba ya kara kiranta, dagawa tayi hade da sallama tace “Abba ina yini?” Yace “Lafiya lau dear, how are you?” Tace “Alhamdulillah Abba ya aiki?” Abba yace “Mun gode Allah, yaushe xa ku yi resuming ne?” Nihad tace “In two weeks time Abba” Abba yace “Ohk, yaushe kamilar tace maki xa ku dawo?” Nihad tace “Ana saura 2 days mu koma school, tare da mijin xa mu dawo gaba daya” Abba yace “Ohk that’s good, take care dear” Nihad tace “Alright Abba, bye”

 

Katse wayar Abba yayi, ta bude motar ta sauka sannan ta kulle, tana rike da jakarta bayan ta kulle motar ta nufi entrance din hotel din tana kokarin dialing number Husnah, sunanta ta ji an kira, ta juya da sauri, wani tsohon saurayin Husnah ne, ya nufota da sauri yace “Hi Nihad” Ta ɗan yi murmushi tace “How are you Kabir” Yace “Alhamdulillah, ya kwana biyu?” Tace “Cool” Yayi er dariya yace “Kina da appointment yau a nan kenan?” Ta ɗan kallesa sai kuma tace “Tare da kawayena nake, suna ciki” Yace “Ohk maa sha Allah, ya school” tace “Fine” A tare suka jera xuwa cikin reception din hotel din yana jan ta da hira, zaune yake a haraban hotel din karkashin inuwa tare da wani da baxai wuce sa’ansa ba yana sauraron duk abinda yake ce masa, da ido ya bi ta da Kabir, at first he quickly imagined ba ita bace kamace kawai, but yanayin tafiyarta da kuma jakar hannunta wanda duk ya sani ya sa shi ajiye goran ruwan dake hannunsa ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Buga table din abokinsa yayi da mamaki yace “Heyy!!” Da sauri ya dauke idonsa daga kallonta ya kalli abokin nasa, abokin yace “Why are u staring at her that way, burge ka tayi ko me? Kaga yarinya da saurayinta sun zo holewarsu kayi ta kallonta?” Still bai ce komai ba sai kallon abokin nasa yake babu ko kiftawa, Abokin yace “Khalil” Sauke idonsa yayi daga kallonsa sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace “Yea mamaki abun ya bani shi yasa na bi su da kallo” Dariya Sultan yayi yace “Haba kai ma ai kasan wannan ba sabon abu bane, yan matan yanxu kam ai sun xama abinda suka zama sai addu’a, basa ma jin kunyan iskanci yanxu, ko wani hotels ka bi su ne, baka lura bane ko 10 mins ba ayi ba set of 3 girls suka wuce mu a nan, su ma kuma duk gun samarin suka zo na sani” Shi dai khalil bai ce komai ba, he was really shock, yarinyar da aka ce tana Kebbi ce ya gani a Bristol, Sultan yace “Kai dai tunda kana da Nadeeyah and upon her parents wealth she is decent sai ka gode ma Allah” Murmushi kawai khalil yayi, Sultan yace “Kuma kuna magana da ita all this while?” Khalil yace “Muna yi” Sultan yace “Tasan kana kano?” Girgiza masa kai kawai khalil yayi, Sultan yace “Ya batun turawa gidansu?” Khalil yace “Yana nan” Sultan yace “Toh Allah ya nuna mana, but ya kamata kayi nazarin duk abinda nace maka Khalil, pls do so Frnd” Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace “In sha Allah, and i appreciate u Sultan” Sultan yace “Nima nagode da ka bani lokacinka har ka saurareni” Murmushi kawai khalil yayi, Sultan ya mike yace “Toh ka koma can inda ka samar ma kanka aiki kar a fara nemanka ko” Khalil yace “Ina jiran wani ne still” Sultan yace “Wa kenan?”

Khalil yayi kasa da murya yace “Another caring frnd like you” Sultan ya sauke ajiyar xuciya yace “All this shall come to pass in sha Allah Khalil” khalil ya ɗan yi murmushi ya mike tsaye ya mika masa hannu sannan yace “I truly appreciate ur care Sultan, nagode kwarai” Sultan yace “Mention not abokina” Har mota Khalil ya rakasa sannan ya dawo ya zauna inda yake zaune har sannan yana cike da mamaki, har karfe shidda na yamma yana xaune wajen bai ga fitowar Nihad ba balle shi mutumin da ta shiga ciki da, kiran Aminu ne ya shigo wayarsa ya ciro ya daga ya kai kunne, Aminu yace “Toh na ji ka shiru daga cewa xaka bakin titi ka dawo” Khalil yace “Ina nan dawowa yanxu” Aminu yace “Toh ga manyan mangwaro ma Hajiya Inna ta zo ta bada a ajiye maka” Khalil yayi murmushi yace “Toh nagode, sai na dawo” daga haka ya katse wayar. Har aka yi magrib Khalil bai ga fitowar Nihad ba, babu warce ta fado masa a rai sai Mahaifiyarta, ya ji tausayinta sosai, mata me kirki da mutunta ɗan Adam, and such a nyc woman didn’t deserve Nihad as a child… Wayarsa ya dauka yayi dialing number Nihal ya kai kunne, tana dagawa tayi masa sallama, ya amsa yace “Ya kike?” Tace “Alhmdlh, ina yini?” Yace “Lafiya lau, ya lectures?” Tace “Ya shirin jarabawa dai” Yace “Ohh haka ne, ya shirin jarabawa?” Tace “Alhmdlh” yace “Tare xa ku dawo da er uwarki kenan?” Nihal tace “Noo, ai ita tana kebbi” Yace “Ko?” Tace “Eh” Yace “Ita da wa suka tafi kebbi?” Nihal tace “Wannan yayar tawa da ka kai ni gidanta kwanaki” yace “Ohk, yaushe xa su dawo?” Tace “Jiya da na tambayi Umma tace min nan da sati biyu” Khalil ya ma rasa abinda xai ce, jin shiru tace “Hello” Yace “Eh ina jin ki, to shkkn, dama tambayarki xan yi ya jarabawa” Tace “Toh Nagode” Yace “Sai anjima” Daga haka ya katse wayar, kallon cikin hotel din yayi, yana ta xaune har kusan Isha’i ganin Nihad ba fitowa xata yi ba ya mike ya tafi can inda yayi parking motar gidansu Nihad ya shiga ya bar hotel din, direct gidan Kamila ya nufa, bayan sun gaisa da mai gadin yace “Matar gidan na nan?” Mai gadin yace Tace “Eh” Yace “Ita da wa suka tafi kebbi?” Nihal tace “Wannan yayar tawa da ka kai ni gidanta kwanaki” yace “Ohk, yaushe xa su dawo?” Tace “Jiya da na tambayi Umma tace min nan da sati biyu” Khalil ya ma rasa abinda xai ce, jin shiru tace “Hello” Yace “Eh ina jin ki, to shkkn, dama tambayarki xan yi ya jarabawa” Tace “Toh Nagode” Yace “Sai anjima” Daga haka ya katse wayar, kallon cikin hotel din yayi, yana ta xaune har kusan Isha’i ganin Nihad ba fitowa xata yi ba ya mike ya tafi can inda yayi parking motar gidansu Nihad ya shiga ya bar hotel din, direct gidan Kamila ya nufa, bayan sun gaisa da mai gadin yace “Matar gidan na nan?” Mai gadin yace “Ehh tana ciki” Khalil yayi shiru, sai kuma yace “Ohk an aiko ni wajenta ne” Mai gadin yace “Toh bari ayi mata magana” Yana shiga gate khalil ya juya ya shiga motar ya bar layin. Direct gida khalil ya nufa erasing everything off his mind kamar ba ayi ba, after all it’s none of his business and will neva be any of his business. Bayan sati biyun da Umma tace ma Abba su Nihad xa su dawo kano, sai ga Nihad tare da kamila a gidan da yamma, babu irin rokon da Umma bata yi ma Kamila akan su xo gida tare da kyar dai daga karshe ta yarda suka taho gidan da Nihad, akwatin kayanta daya kawai ta dawo gida da, tun da suka shigo gate Khalil ke kallon Nihad, ita kuwa shaff ta mance da wani batunsa a gidan sai yanxu da ta gansa, tana ganinsa kuwa mood dinta ya canxa, shkkn kuma ta dawo miserable house din nan da driver din nan a ciki, noo gaskiya ita dai baxata iya ba, xata roki Umma ta yi come up with another plan da xai sa ta sake barin gidan, Kamila ce kawai ta amsa gaisuwan mai gadi da khalil da ke gaisheta, Nihad kuwa tafiya take cike da isa ta nufi entrance din parlor, tayi wani kyau ta kara haske, kana ganinta kasan bata da damuwar komai, ba komai ya haddasa mata kara haske ba sai cream me shegen tsada irin nasu Husnah da take shafawa yanxu, ga sabulu ga shower gel, Khalil ya bi ta da kallo, suna shiga parlor Aminu yayi kasa da murya yace “Kaga yanda tayi wani haske tayi kyau uwa warce ta tafi duniyanci?” Khalil bai ce komai ba, but he really felt sorry for Abba and Mumy, ya jima bai hadu da mutane masu kirki da karamci irin tasu ba, a watanninsa kusan shidda a gidan Abba ya ja sa jiki kamar nasa, ya kai ya kawo yanxu hatta Atm card Abba na basa ya ciro masa kudi wanda ko Habibu baya ba Atm card dinsa, shi ko Abba ya ya6a da hankali nutsuwa da girmamawa irin ta Khalil, ya sha gwadasa ya aikesa ya siyo masa abu sai ya linka kudin sau uku ya basa yace haka ake siyarwa amma in sha Allah sai Khalil ya kawo masa canjinsa, ya gwadasa ta fanni daban daban wanda shi khalil bai ma san yana yi ba, duk gidan babu wanda yake da matsala da warce ta zama second Nihad sai Umma, gaba daya ta dau karan tsana ta daura masa tun da Nihad ta fesa mata yana waya da Nihal, to uban me Nihal dinta xata yi da shi, duk abinda take yi kuma baya damun khalil, Usman ma dai in ya zo basa wani gaisawa, amma Farooq idan yana gari mayar da bakin gate wajen zamansa yake yi sbda Khalil, xaka yi tunanin ya ta6a saninsa, kawai he enjoys gisting with him sbda yana magana kamar wanda yayi ilimi me zurfi, gashi he knows almost everything that’s happening in the world wato he is current, suna dadewa sosai suna hira…

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button