Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 4

Sponsored links

Rasuwar samirah ya taba Annensu sosai fiyeda yanda suka saba hadiye kowane irin yanayi dazai riskesu

Qwaqwalwanta ya sake tabuwa sosai dan haka kusan koda yaushe tana daki a zaune zugum bata komai haka take wuni haka suke kwana da ita,

Sumayyah ma rasuwar ta girgizata tareda firgitata sosai itada safnah ta yanda a yanzu amon muryarsa kawai dukkaninsu fitar dasu hayyacinsu yake jikinsu ya shiga rawar tashin hankali.Biyayyarsu ta ninku fiyeda baya,soronsu ya qaru fiyeda baya,so da kaunar junansu ya karu a zukatansu fiyeda baya haka zalika tausayi da kulawan mahaifiyarsu da suka duqufa yiwa adduar samun sassaucin tabin kan nata sbd qarasa juyewar qwaqwalwanta na nufin Ababa zai iya miqata ga titi ta qarasa haukacewa acan wanda sukuma a yanda sukeji rabuwa da mahaifiyarsu kaman abu ne da mutuwace kawai zata rabasu.

Safnah a yanxu da komai yayi tsanani bata tinanin kowa da komai face kanta,

Mafita take nemarwa kanta koda ta mutuwar ce itama tabi samirah ta huta…

Lokacin rasuwar yaja sosai addua da kulawar dasukewa maihaifiyarsu yasa ta dan dawo daidai lokuta da dama a hankalinta take duk da hakan kusan gabaki daya Ababa yasa dokar karta fito ta ringa zama a daki sbd idan yana ganin yanayinta zai iya kaita gidan mahaukata idan akwai.

Jin hakan yasa suke killaceta a daki sam basa barinta fitowa idan ba bandaki ko alwala zatayiba,

Sauki na samuwarta sosai Hande tasa tadawo Ayyukan da aka saba da ita na wahalar.

Bai taba yarda da kowaba a rayuwarsa bayan kansa

Hande data haifesa bata taba sanin komai daya danganci samu ko dukiyarsaba,

A koda yaushe sune suke masa lissafi a gabansa tas sbd sunada kokari akan ilimin da suka dan samu daga karatun da sikai.

Sun rungumi kaddara sun rungumi rayuwar dasuke ciki sbd suna kiyaye komai girman doka da umarninsa da dukkanin imaninsu,

Abu daya ne yake girgiza jarumta da zuciyar Benazir shine duk lolacinda safnah ta furta kalmar barin gida sai taji zuciyar ta wani irin nauyi da faduwa,

Ba iya damuwa da tsoron abinda zai iya faruwa da safnah din bane idan Ababa ya kamata kaman yanda yakama samirah koma dai menene tasan ba lallai akwai alkhairi tattare da hakan bane.

Dukkanin halaye dake bayyanarda boyayyan son iya kai dake zuciya da jinin safnah yana bayyana ne tun data busar da zuciyarta ga son tserewa kota halin yaya tabar gidan.

********a shekaru yanzu bazasu wuce sha bakwai zuwa sha takwas ba sumayya ce mai sha tara zuwa ashirin,

 

Dukkaninsu kyawawa ne duk da kasancewarsu ba masu hasken fata ba sosai,

Mahaifiyarsu Anne marainiya ce da Ababa din yayi shaawar aurenta sbd batada kowa batada mai tsaya mata a duk rayuwar da yayi niyar yi da ita,

Batada uwa bata uba sai kakarta bara sukeyi ya aureta ko wata baa rufa da aurenba kakarta ta rasu ya tattara ya baro garinsu da ita da mahaifiyarsa ya dawo birni ya dasa sabuwar rayuwarsa anan inda yake sanaar dabbobi da kasuwancin babban shagon fata da kuma yawon kai manyan shanu da raguna garuruwa,

Bazaa kirasa mai kudi ba hakama bazaa kirasa talaka ba sbd cinsa da shansa da buqatunsa basufi karfinsaba,

Dukkanin masu aiki a karkashinsa basa jin dadinsa sbd mutum ne mara yarda da rashin daukar asara komai kankantarta baya dauka,

Baya shiga harkar kowa ba ruwansa da duk abinda zakayi koda mutum zaka kashe a gabansa zai iya wucewa bai shiga aikinka ba sbd duk duniya ya tsani a shiga nasa lamarin,

Tunda ya ware kansa daga anguwar dakeda mutane sosai ya dawo irin anguwannin karshe karshen gari inda babu mutane sosai ya kafa iyalansa da rayuwarsa harkokinsa kawai yakeyi,

Babu wanda yasan irin munanniyar rayuwar datake gudana acikin gidansa sbd basa zuwa gidan kowa kaman yanda bayason ana zuwa gidansa idan ba qaruwa yakeyi da kai ba,

Duk tsananim azaba da ukubar da yayansa suke ciki jikinsu baya nunawa sosai sbd kyan fatarsu dakuma fitar da basayi suna killace a gida kullum sai hakan yasa fatarsu take kaman a fresh haka zalika sunada jiki mai kyau,

Baida wanda ya tsana ya bude ido a duniya yagani kamar ‘yayan nan hudu mata da Allah ya basa,

Duk wani tinanin mafita akan yanda zaiyi dasu yayi sbd yanda ciyar dasu kawai kecin wani dan bangare na arzikinsa,

Idan baya qaruwa da kai sam bakada wani amfani ko darajar da zaiyi muaamala dakai,

Komai nasa akan lissafin qaruwa yake

Anne wadda asalin sunanta yake banazir ita nata amfanin dan yana biyan buqatunsa na aure ne akanta shiyasa baya neman yanda zaiyi da ita din amma a yanda hauka ke neman shigarta daga ranarda ta tabbata ta haukace bazai barta ta qara kwana daya ba a gidansa bakuma tareda ‘yayanta zata tafi ba dan su lissafinsa akansu mai girma ne saiya fanshe komai nasa dasukaci tsaf da yardar Allah.

Dukkaninsu bayan sumayyah datake ta farko babu wanda shine ya rada masa suna a cikinsu

Hande ce take rada musu suna

Benazir kuwa sbd tsanarta datafi ta kowa ita kanta Hande kasa saka mata sunan tayi shiyasa Annen ta mayarwa ‘yar da sunanta ta saka mata BENAZIR wadda acikinsu itace baa yankawa ragon sunan dayake yankawa sauranba wanda yana yankawa yake siyarda rabi rabin a soya masa yaci abinsa sauran a dan rarrabawa mayun makota masu nacin zuwa idan an haihu din shima hande ce take rabawar sbd itakuma duk wata barna da ‘danta yakeyi tsayawa takeyi ta boye shiyasa take faran faran da jamaar waje ta yanda babu wanda zai taba sanin halinda Anne da ‘yayanta suke ciki duk da shi rashin gata da rashin kulawar dasuke samu a bayyane yake amma babu me tankawa sbd zafi da tsananin rashin daukan hakuri a lamarinsa.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button