Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 46

Sponsored links

Ajiyar zuciya ya sauke ganin idan be bita a hankali ba komai ze iya lalacewa,gwara ya lallabata su rabu lafiya, Afterall bashi ya dauki wanda sukayi accident din tare ba, kishine kawai yasasa fadin hakan, kuma koma wa take magana akai ze nemosa sannan ya tabbatar ya kashesa dagaske!…..

“Relax love, bari in fadamiki iya abinda nasani”..

Ya fada yana kallon lumsassun idanuwanta masu kaifi….     “Actually bansan ku biyu kukayi accident din ba saida nazo likitoci suke fadamin, dana tambayi ina dayan yake sukace iyayansa sun tafi dashi, wallahil azeem abinda nasani kenan”……

Gyada kai tayi har zuciyarta ta yarda da abinda ya fada dan mutum ce ita me saurin sensing in mutum karya yake ko gaskiya yake fadi, sannan hankalinta ya kwanta tinda iyayensa ne suka tafi dashi dole zasu basa kulawa me kyau……

Batareda tace komai ba ta masa nuni dayaja motar su tafi zuciyarta sake da kudirin dake ranta, sam bata manta da mama ba da abinda tayi niyar yiwa mama,kuma ya kamata a ce ta fara taking action tin yanzu……

“Kaini office din daddy”…..

Ta fada bayan tagama lissafin daddy na office a wannan lokacin, zatafi san haka kuma dan tasan mama ta sakankance by now, zuwanta gidan kuma zesa ta iya gane shirinta so gwara kawai ta samesa a office a sirrince…….

Daso samu ne ya tambayeta me zatayi a office din daddy, amma ina ya riga ya bata rawarsa da tsalle tinda ya bari sabani ya shiga tsakaninsu, sai yaji yana shakkarta yau…..

Daidai ‘Khaleel ventures and co’ yayi parking, ta fita batareda tabi ta kansa ba…..

Harta nufi hanyar shiga company din saita dawo da sauri, luckily ta sameshi a inda tabarsa ko motsawa beyi ba……

“Ai dama nasan zaki dawo”….

Ya fada yana smiling sannan ya miko mata niqab, batace komai ba ta karba ta daura sannan tashige ciki……

Direct office din daddy ta nufa, secretary dinsa tabita da kallo ganin ta nufa office din manager without permission, taso ta dakatar da ita sai taga ta mata kwarjini, tanaji tana gani tashige office din batareda ta hanata ba, addu’ar ta daya Allah yasa karta janyo mata matsala……

Da sallama ciki ciki ta murda handle din tashiga tana dage niqab dinta…..

Daddy dake zaune ya mike da sauri ganin wacce akace ta mutu tazo office dinsa, toh kodai fatalwa ce?…. A kidime cikin rawar jiki yace…..

“Wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahir rahmani raheem, ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba, Wayyo Allah ba ance kin mutu ba?”……

Wata muguwar dariya ta saki data kara ruda daddy yaji kamar ya saki fitsari tace…..

“Ban riga na mutu ba amma ina shirin mutuwa idan baka biyamin bukatar danazo dashi ba!”…..

Daddy dafe cikinsa dayaji ya murda yayi, cikin zaro ido yace….,

“Innalillahi wa inna ilahi raji’un,mutum ko aljan, dan Allah kiyi hakuri ki kyaleni, mekike so?”….

Daidaita nitsuwarta tayi tana tinanin wanda ya fadama daddy ta mutu? Gashi yanzu ya ganta ya dauka fatalwa ce, dole ta mishi bayani yanzu dan yasamu nitsuwar daze fahimci abunda tazo dashi sosai…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button