Hausa Novels Complete Documents

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 45

Sponsored links

“Har me zaki iyayi akai bayan kingama lalatawa yaro rayuwa, yadena jin maganar kowa, kina nema ki mayar dashi mara mafadi kamarki, nonsense!!”….

“Dakata mallam! Karka kuskura ka gayamin maganar banza, in zakayi magana ka dinga tina a gaban wa kake, wallahi yanzu sai insa a dauremin kai kuma banga ubanda ya isa ya fitar dakai ba duk abinda kake takama dashi kuwa!!”….

Wata dariyar mugunta daddy ya sheka yace…

“Lallai wuyarki ta isa yanka! Banida lokacinki yanzu amma ki rubuta ki ajye we’ll come back to this!” Yanzu ta da’na nake!”….

“Kace danka mana tinda kai kayi naqudarsa ka haifesa! Kuma duk wani stubbornness na Deen ai a gurinka ya dauko kowa yasan wannan karatun kuma!!!……..

“Dake kikayi naqudarsa wani tarbiya kika basa banda gurbataciyyar rayuwa da kikasashi? Wallahi nayi danasanin saninki a rayuwa Fatima!!”….

“Ai nice da danasani da Allah ya hadani da munafuki azzalumi macuci irinka, above all maciyin amana wanda besan halacci ba,zakaga yanda zan wanke Deen tatas with the power of the law koda shi yayi kisan kuwa!”

Mami na fadin haka ta samu guri ta zauna bata kara kula dad ba……….

Driving yake zuciyarsa a dagule saboda tinda suka fito daga asibitin taki kulasa gashi ya rasa meya mata balle ya bata hakuri, maganar duniya yamata taki cewa komai……

Lumsassun idanunta ta bude kadan ta kallesa, so take ta tambayesa abubuwa dayawa amma ta kasa, ta dade a haka kafin tayi summoning courage tace….

“Are you responsible for the incident?”….

Zaro ido yayi sosai ya marairaice kamar karamin yaro yace…..

“Ni kuma love? How could you ever think zan iya cutar dake? Aiko wani ne ya tabaki sai inda karfina ya kare wallahi!”…..

“Who knows! Aibani kadaice ba, Tinda kace bakai kayi causing komai ba toh ina wanda mukayi accident din tare? I can recall vividly bani kadaice a motar ba!”…..

Ta fada rai a hade…..

“Sorry to say ya mutu, tin jiya aka binneshi”…..

“Karya kake wallahi! He’s not dead!!”…

Fatima zainab ta fada a zafaffe….

“Ni kike cewa karya nake?”….

“Angaya maka din, sai me? Just tell me where you take the damn guy to!”…….

“Naga alama kina nema kifi karfina! Ni kikema tsawa haka akan wani banza?”……

Ya fada mamaki fal ransa, wai ita ke maida masa magana haka yau? Yasani sarai bata ganin kan kowa da gashi amma fa duk iskancinta banda shi!

“An maka tsawar! Kafi karfin a maka ne toh? Mallam where’s is the man I had accident with?!”….

Cikin bacin rai yace

“Get out of my car!!”….

Itama cikin zafin rai tace……

“Wallahi bazan fita ba!, Tell me where the damn man is kaga in ban fitar maka daga useless car dinka yanzu ba!!”…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button