Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 31

Sponsored links

Ta share tsahon awa guda tana abu ɗaya babu uwa babu alamar ta. Sai ranta ya ƙara sosuwa, ta dunƙule kanta waje ɗaya tana mai jin hawaye nason zubo mata. Amma ta hana hakan saboda taurin zuciya. Har karfe biyu na dare da masarautar ta nitsa bakajin motsin komai alamar anyi barci, in ma da wanda bai barcinba ya kasance a killace ƙarƙashin inuwar karamin motsi. Waya ta ɗauka tai danne-danne ta kai kunne, a bugu ɗaya aka amsa mata. Kafin ace komai da ga can cikin bada umarni ta furta, “Ki sashi ya jirani a garden”. Daga haka ta yanke kiran. A gurguje tai shiri cikin ɓadda kama ta fice, bazaka taɓa ɗauka mace bace, ta canja kammani cikin kayan jami’an dake aiki bada tsaro a masarautar. Dan haka babu wanda ya maida hankali kanta harta isa babban garden ɗin masarautar dake a ɓangaren kudanci. Wajen nada ƙarancin haske, sai kukan tsuntsaye da ake kiwo jefi-jefi. Da sauri ya fito da ga maboyarsa, ya zube a gabanta yana miƙa gaisuwa. Nuni tai masa ya miƙe batare da ta amsa masa ba. Mikewar yay, kansa a rissine, dan haramunne a garesa kallonta.

 

Sai da ta gama ƙare masa kallo sama da ƙasa ta mika masa anvelope ɗin hannunta. “Daga daren yau zuwa safiyar gobe ina buƙatar jin kuka, ina buƙatar naji kukan mutuwar Zawjata-almilk. Idan aka samu kuskure kuwa kukan mutuwarka ahalinka zasuyi. A jefata a babban ruwan swimming pool na garden ɗin gabashi”.

 

“Umarninki shine abin jirana da cikawa”. Ya faɗa da sauri cikin matuƙar girmamawa. Bata sake tankawa ba ta juya tabar wajen. Sai da ta ɓacema ganinsa ya iya ɗago kansa dake a risine yana sakin nannauyar ajiyar zuciya. Ba yau ya fara mata aiki ba, sai dai a shi kansa har yanzu bazai iya sanin ainahin wacece ba. Dan a koda yaushe cikin ɓadda kama take bashi umarni ko ta saka amintacciyar ta ta bashi, sai dai a duk lokacin da ita ta bashi da kanta ya san ba aiki bane ƙarami. Anvelope ɗin ya buɗe, ya wani zaro idanu da ganin makudan kuɗin da ke ciki miƙaƙƙu sababbi ƙal sai ƙamshin sabunta suke. Fuskarsa washe da murmushi ya sumbaci kuɗin, ransa fes da samunsu. Duk da dai yasan bazai cisu a banza ba, dan wannan aikin bazai taɓa zama mai sauƙi ba a garesa kasancewar matsanancin tsaron da kurkukun da Zawjata-almilk ke ciki, amma kodan waɗan nan taurarin dolene ya cika umarni…….

Ya kai mintuna goma yana kallon yanda masu tsaron kurkukun ke kaiwa da komowa, kowanne kuma da makami tare da shi. Ga haske ƙal tamkar rana dan ko allura ka yar ka duka ka ɗauka abinka batare da ka nema ba. Bugawar ƙaton agogon masarautar da ake iya gani tako wace kusurwar daular ta ruman ya sashi jan numfashi a sarƙe. Karfe uku dai-dai kenan, awa ɗaya garesa kacal na kammala wannan aikin. Dan huɗu nayi zaka fara jin motsin hadimai na tashi domin fara ayyukansu, musamman masu share-share da goge-goge. Zaman ɗammarar ƙugunsa ya gyara da ƙyau, hakama hular kansa kalar kayan jikinsa na ainahin amintattun jami’an dake cikin sashen Tajwar Eshaan. Ya ƙara saita kansa da ƙyau cikin dakewa ya tunkaresu hannunsa ɗauke da babbar jaka. Duk da sanin matsayin masu waɗan nan kayan a gidan gaba ɗaya sukai masa ca. Bai nuna razana ba duk da zuciyarsa na faman dukan dari-ɗari ne. Cikin sake matse kansa ya sara musu alamar girmamawa yana mai miƙa musu I’d card ɗinsa.

 

“Umarnine da ga shugaba, zan sada kayan nan ga Zawjata-almilk domin sakasu a gobe idan zata fita, na kwashe na dattin dake tare da ita”.

 

 

Kallonsa suke kawai suna sake kallon katin domin tantance shi ɗinne a hoton kokuwa. Sai dai hoton ya ɗanyi duhu, duk da kuma hasken wajen dai rana bazata taɓa zama ɗaya da hasken lantarki ba. A dake ya sake faɗin, “Ba tantancewar kaɗai ake buƙata ba. Ya kamata ku kira sashen shugaba domin tabbatarwa, wannan shine cikar aikin masu tsaro”.

 

Kalamansa sun ɗanyi tasiri garesu, sai dai duk da haka wani ya tubure akan sai ya fara zuwa ya tabbatar bawai kiran waya ba. Dan ko ƙuda an tabbatar musu su kasance masu himma wajen hanashi gittawa zuwa inda Iffah take sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Tsabar ƙarfin hali na hadimin nan, babu ko nuna gezau ya bada goyon baya. Hakan ya ƙara saka sauran jin sun yarda da shi, sai dai wancan ɗin babu alamar hakan. Sai ma tabbatar musu da yay su cigaba da tsaresa zaije ya dawo”.

 

Tsahon mintuna goma da tafiyarsa sai gashi ya dawo, batare da yace komai ba yay masa nuni da ya shiga. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ya saki da ɗan kashe ido wa jami’in da a yanzu yake ta faman sinne kai kamar wani munafuki. Sauran basu damuba dan su dama sun aminta tun dazun, dan haka ya wuce hankali kwance.

 

 

 

Tana tsaka da ɓarawon barcin da ya sace ta bayan ta idar da sallar da take tsaiwar yi duk dare domin miƙa kukanta ga UBANGIJI taji kamar numfashinta na fita a fisge, firgigit ta farka da ƙoƙarin kai hannunta saman hancinta, sai dai aikin gama ya gama dan ya riga ya shaƙa mata abinda ke cikin handkherciff ɗin. Duk yanda taso sake yunƙurawa hakan ya gagara sai ma jikinta dake saki baki ɗaya. Daga haka bata sake sanin inda kanta yake ba.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button