Hausa Novels and Stories

Hamrah Hausa Novel Page 3

Sponsored links

Nigeria tazo ta musulunta tana zaune gidansu hamrah d’in, dr. Fareed ya kawo mata babban malami tana d’aukar karatu a gurinshi sossai ta mai da hankali akan addini wani lokacin hamrah d’in ke daura ta kan hanya don hamrah ba baya ba wajen ilimin addini sossai take da ibada sede tana da dan banzan wulakanci mussaman akan samari ita har yanzu bata ga wadda ya dace da aurenta ba kowa low class ne in kuwa kayi gigin furta mata se ta tsiga maka abunda har ka mutu baza ka manta ba……..

Private elevator ta shige a take ranta ya baci ganin wani saurayi tsaye ciki dama kaman ta ga shigan mutum Allah ya taimake shi da ya danna kafin ta karaso da se ta jira kenan don taimakonshi zata ce sbd be isa ya sa ta jira bata wulakanta shi ba…….

tsaki taja a fili ko dago kai saurayin be yi ya kalle ta ba abunda ya kara bata mata rai kenan dogo ne sossai ga alamun karfi sun bayyana a jikinshi daga gani ya saba daga karfe kuma kyakyawa ne a zuciyarta take maganan wani tsaki ta kara ja a ranta ta sake cewa ko me damuwa na da kyaunshi? Mtseww……….

Tabbas ranshi ya soma baci ya tsani tsaki a rayuwarshi in har kuwa ta kara ja ba abunda ze hana shi tsinka mata mari be gama tunaninshi ba elevator din yayi wani jijjiga da alamu an dan samu matsala ne bottle water dake hannunshi da ya bude da niyyar sha ya fallatsa se fuskarta a take ya jike mata fuska zuwa gyale………

Wani irin numfashi tajaa cikin tashin hankali da matukar tsoro ta daga hannu ta tsinka mishi mari shi kuwa ya dago da niyyar bata hakuri sbd ya san be kyauta ba kuma ruwan da sanyi se Jin saukar mari yayi muryanta a sama tace “in banda hauka da dakikanci taya zaka watsa min ruwa ruwan ma me sanyi kasheni kakeson yi ne?………..

Kallonta kawai saurayin ke yi tabbas ba wadda ya san farin cikinshi haka ba wadda ya san bacin ranshi amma da ba don haka ba tsayuwa a gurin ma se ya gagare ta wani irin turiri ranshi ke yi amma baza ka taba ganewa ba a daidai lokacin da elevator din ya tsaya ta furta “bloody fool” tare da ficewa tana mamakin wa ya bashi izinin shiga private elevator…………

Office dinta ta nufa seda ta shafe wasu 30mins din wurin gyara fuskanta da jikinta tukun ta nufi meeting hall d’in da zasuyi meeting d’in tana shiga ba hi ba hello kawai tace “shall we start the meeting?” A sanyaye suka amsa mata da “yes” kafin su rufe baki sukaji an ce “to hell with the meeting” kowa bayan kujeranshi ya zuba ma ido a hankali ya juyo da kujeran ya fara fiskantan ta shanyayyun idanunshi ya zuba mata na kusan 2min……..

 

 

 

Bud’e baki yayi da niyyar yin magana se kuma ya fasa mikewa yayi ya fice daga company d’in cikin haddad’un motocinshi ranshi na wani irin suya kenan itace CEO na companyn kenan?lallai se tayi dana sanin marin da ta mishi a duniya baze iya tuna randa aka taba marinshi ba balle duka se ta gwammaci kida da karatu batun ta ya share ya shiga wasu harkoki don yana da tabbacin se ta neme shi shi kuma anan ne zeyi maganinta anan ne ze gasa mata aya a hannu smirk yayi tare da jan kwafa……….

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button