Hausa Novels and Stories

Idon Naira 30

Sponsored links

Aqeel ma kallo daya yayi Mata ya fahimci tsananin sanyi da sarewar datayi Dan haka shima ya kasa magana suka barwa Allah komai.

Haj maryamah daketa faman kiransa a waya bai dagaba sbd wayar ya Barta a mota da Haka take Hankalinta ya tashi itama sbd taji fitar motarsa da daddaren.

Takira Haj Kaka Amma ance baya can gidan Dan Haka Kai tsaye insha Allah Yana gurin Zainab.

Wurgi tayi da wayarta kan gado tareda Dan rufe ido Tana dafe goshinta qaramin tsoki na fitowa bakinta.

A asibiti kuwa komai ya lalacewa su Zainab da likitoci sukaita fada akan rashin kawosa asibiti da wuri yaga likita.

Zainab dai Bata iya cewa komaiba saidai AQEEL dinne kawai yake iya Basu hakuri Yana sanar musu da shima bai sani rashin lafiyar tasaba.

Tun suna saka ran Jin wani bayani daga likitoci bayan tarin magani da allurai da drips dasuka rubuta aka siyo Babu abinda suka sanar musu sbd malam din dai su kansu Basu samu ya farfadoba Amma dai suna saka ran farfadowar tasa Koda tsakiyar dare ne.

Anan suka cinye Daren zaune kofar dakin emergency babu Mai iya doguwar magana acikinsu…

Qarfe biyar na asuba Allah ya karbi ran malam Umar sanda Bayan ya bude idanuwansa akan Zainab Aqeel dake gefen.,

Kallonta kawai yayi tsawon sakanni kamarma baisan meyake kalloba sbd kwata kwata baya hayyacinsa na lafiya,

Akan Aqeel yakuma juyar da kwayar idanuwansa shima ya kafesa da kallo daga Hakan ya iya bude Baki daqyar yana kokarin Jan shahada ahankali ahakan Ransa ya fita.

Innalillahi wainna IlayhirRajiun

Innalillahi wainna IlayhirRajiun”

Shi kadaine kalmar da Aqeel yake iya kamowa bakinsa da zuciyarsa..

Zainab kuwa ahankali ta Isa garesa tareda zuba Masa idanuwanta dasuka Gama galabaituwa.

Ahankali Allah yabata ikon iya bude Baki tace”

Ya rasu ne Aqeel????

Sunkuyar dakai Aqeel yayi Yana kasa riqe jarumtarsa hawaye na kufce Masa masu yawan gaske.

Ganin Hakan yasata itama sauke kan ahankali tareda matsawa ta zauna bakin gadon takai hannunta na rawa ta Dora akan na malam din,

Sam idanuwanta bushewa sukayi suna Mata wani radadin yaji Amma kukan yakasa zuwa tsabar tashin hankali da duhun daya rufe zuciyarta.

AQEEL kuwa kuka yakeyi na hawaye sosai sbd rasuwar shikam tazo Masa ne Kai tsaye daga sama sbd baisan uban nasa Kuma malaminsa baida lafiyaba duk kwanakin.

Rufe gawar akai suka fito daga dakin suka zauna Babu Mai iya magana acikinsu Dan kuwa dukkansu sunyi nisa a fita hayyaci.

Ta bangaren Haj maryamah ma kuwa Bata daina kiransaba tsawon Daren sbd bai taba kwana ba a waje duk rayuwarsa

Idan dai baya gida to Yana gidan Haj Kaka Amma yau din tazo da sabon Al’amari.

Kiransa take Tana sakewa Amma baya dauka sbd wayar na mota…

Duk yanda takai ga danne zuciyarta saida ranta yakai maqura a baci tareda shiga tsoro da tashin hankalin idan ba wani abun ya samu Dan nataba,

Tanason Kiran Zainab taji idan gurinta yazo Amma zuciyarta taqi barinta Kiran dan Haka a tsakiyar Daren gaf da asuba takira umma ta sanar da ita sbd ita takira Zainab din.

Adaidai lokacinda ake fitowa sallar asuba alokacin Kiran umma yashigo wayar Zainab dake zaune kofar dakin da gawar mijinta yake, AQEEL kuwa yashiga masallacin asibitin sallah baidawoba.

Idanuwanta sunyi wani irin nauyi sosai,Babu abinda yake cikinsa sai radadin bushewa na kukan da suka gaza,

Daqyar ta iya gane sunan Mai Kiran ta daga ahankali takai kunnenta tareda Yar shaqaqqiyar sallama sbd makoshinta daya bushe tun tsakar dare har zuwa lokacinda mijinta ya karba Kiran ubangiji.

Umman na Jin Zainab ta dauki wayar Bata tsaya Jin komaiba Kai tsaye tace”

AQEEL na gurinki???

Daqyar Zainab taja numfashi tace,

“Eh….

Bayan Hakan umma Bata tsaya Jin komaiba ta rufe Zainab din da fada sosai akan bazata iya Bari maryamah ta Sabu da ‘danta ba harsai ya tafi Babu sabo da shakuwa tsakaninsu,

Meyasa bazata zama sanadi na alkhairi ba saina fitina,,???

Kuma ita Maryamah data haifi ‘dan batai qyashin bar Mata shi Yana yaroba sai itace zataji qyashin barin maryamah da ‘dan su samu nasu lokacin suma……

Dan batasan zafi da ciwon ciki da haihuwar ‘da bane shiyasa take saka son Kai a lamarin uwar data haifi ‘da…

Zainab zuciyarta takusa bugawa ta tarwatse tun lokacinda rai ya fita ajikin malam sai alokacin tasamu kuka Mai karfi yazo Mata Dama nemansa takeyi Amma zuciyarta ta mushe qyam sbd girman tashin hankalin data Shiga sai gashi masifar su umman tasa kukan yasamu zuwa.

Umma cikin waya dataji kukan sai ta tsaya da mamaki Tana cewa,

“Lallai Zainab kin samu sake,

Ina fara Miki fadan shine Zaki fashemun da wannan kukan kamar wadda na kashewa miji

Wato ke bakyason fada yanzu……

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button