Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 34

Sponsored links

Mintuna da basu wuce huɗu da shigar tasa ba ya dawo ya zube a gabanta. “ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai amfani, shugaba ya bada damar shiga dake har ciki”. Shiru tai kamar bazata motsa ba, dan a duk sanda ta kama zasu gana anan sashensa yakan fito ne su haɗu a wannan falon ko ƙaramin falon hutawarsa dake a hawa na uku. Wannan kuwa a ƙa’ida ko matarsa bata shigarsa, dan haka jin wannan amasa yasata fahimtar akwai matsalar da gaske.

 

Bayan buɗe mata ƙofa Ghazi yaja da baya. Cikin takunta na ƙasaita da isa ta ƙarasa shiga cikin matsakaicin falon mai fidda wani irin ƙamshi da wadataccen sanyin na’urar ac. Rashin girman falon ba komai bane, haɗuwarsa da tsaruwarsa ce mafi ɗaukar hankalin mai kallo. Dan an ƙawatashine da wasu irin tausasan tumtum na ainahin sarakan asali, dardumar falon kanta abin kallo ce, komai ya tsaru dai-dai da tsaruwar manyan mutane. A hankali takai zaune tana mai sauke ajiyar zuciya, sosai takejin matuƙar kewar gudan jinin nata, sai dai tsarin masarautar tasu ya tilasta mata haƙura akan dole tamkar kowace uwa ta Tajwar irinta da akai a cikin wannan daula….

Motsin buɗe ƙofa da ƙamshin turarensa mai rige-rigen isowa hancinta da sautin takumsa ya sata ɗago ƙyawawan idanunta ta sauke a kansa. A hankali ya cigaba da takowa cikin ƙasaita da nutsuwa har ya ƙaraso gareta. Daga tsayen da yake ya ɗan risinar da kansa alamar girmamawa. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki *_Ammie!_*”. Nutsatstsiyar muryarsa mai zurfi da rashin hayaniya ta fita a fisge, dan yanda ya motsa lips ɗinsa a hankali zama ka iya ɗauka bashi yay maganar ba. A hankali ta sauke ajiyar zuciya mai haɗe da nannauyan numfashi ta jinjina kanta da lumshe idanunta ta buɗe a kansa alamar amsawa. A nutse ya kai zaune a gefenta, yay zama irin na ƙasaita da kame kai da kuma girmamawa a gareta matsayin mahaifiya. Hanunta ta ɗaura bisa tattausar sumar dake kansa kwance, tare da ɗan ranƙwafawa ta sumbaci goshinsa da yay zafi zau alamar baida lafiya. Lumsassun idanunsa da ƙanƙancewarsu ya hanata ganin hasken cikinsu ya buɗe, ya motsa lips ɗinsa kaɗan alamar murmushi a gareta. Murmushin ta saki itama a karo na farko da gyara zamanta na ƙasaita.

Ɗan luuu yay da idanunsa ya lumshesu tare da sake buɗewa a kanta da ɗan risinar da kai na girmamawa. Sai kuma ya kamo hanunta data janye a saman sumar kansa ya sumbata. Ajiyar zuciya ta sake saukewa mai kauri da jin ƙarin ƙaunar tilon gudan jinin nata da maƙiya suka sako a gaba. Tana matuƙar ƙishirwar rashin ganinsa a kusa da ita ko yaushe, sai dai babu yanda ta’iyane…..

“Ammie kina lafiya?”.

Ya katse mata tunanin da take neman yin nisa a ciki. Numfashi ta ɗan fisga ta fesar alamar dawowa. Sai kuma ta girgiza kanta da raunana fuskarta. “Kasancewarka lafiya itace tawa Saiful-mulk”.

A karo na biyu ya saki murmushi yana ɗan jinjina kansa shima, sai kuma ya ɗago ya ɗan kalleta ya kauda kai. “Ina lafiya Ammie”.

Baice komaiba kusan minti ɗaya, hakan ya fahintar da ita bazai ce ɗin ba, tai murmushi kawai tana kaɗa kanta. Ta yarda jinin mulki gaskiya ne, dan tana ganinsa yana yawo a cikin gudan jininta. Duk ƙasaita da miskilanci irin na Tajwar Haysam da ita kanta da ake faɗi Eshaan ɗinta ya takasu ya shanye. Irin miskalayen mutanen nan ne shi masu matukar ban mamaki da wuyar sha’ani, dan kai tsaye baka isa gane ainahinsu ba balle farin cikinsu ko damuwarsu kai tsaye, a matsayinta na mahaifiya a garesa da ake ganin yafi sakewa da ita fiye da kowa sukanyi zaman awa guda bai firta jimlar magana sau goma ba, murmushi kam ita da Malikat Haseenah kawai ke gani daga garesa sai mahaifinsa kafin yabar duniya……

 

Lurar da yay tayi nisa a tunani ya sashi kai hannunsa cikin ƙyaƙyƙyawan bowl ɗin da aka cuɗa dabino da zuba ya ɗakko tsagin dabino ɗaya daya naɗi zuma yay luntsum, ya tare da ɗayan hanunsa ya kai bakinta. A hankali taja numfashi ta sauke alamar dawowa. Babu musu ta matso tare da buɗe bakin ya saka mata. Sai da ta cinye a nutse tana mai kallonsa da murmushi sannan itama ta ɗauka kamar yanda ya bata ta bashi har sau uku. Tasan yunwa yake ji, amma yaƙi cin komai saboda damuwa. Tun yana yaro haka yake, a duk sanda sukaje dubashi a inda ya girma ita da Tajwar Haysam ta wannan hanyar take gane yanada damuwa, ko kuma yana fushi. Dan in har yana jin yunwa yaƙi cin abinci suka matsa masa akan yaci zai ɗiba abincin ya saka a bakinsu, sukuma hakan da yayi zai nusashesu zama su bashi da kansu har sai ya ƙoshi. Tissue tasa ta goge masa bakinsa idonta dake kansa na cika da ƙwalla.

Gajeren murmushisa ya sakar mata da kauda kansa gefe maimakon amsar data buƙaci ji daga garesa. Itama bata sake cewa komaiba, sai wayar landline dake gefensa ta ɗauka. (Inba akan Tajwar Eshaan ba waya isa ganin Malikat Bushirat a haka😑). Cikin ƙanƙanin lokaci aka iso da abinda ta buƙata. Shi dai kallonta yake a harɗe kamar yanda itama take zaune a harɗen. Abincine na musamman, wanda tasan shine mafi soyuwa a garesa…

“Idan kana zama da yunwa bazan yafema kaina ba”.

Idanunsa yay kamar zai rufe sai kuma ya buɗe a kanta. Ƙasaita jininsa ce, kamewa da tsumewa nagartarsa ce. Kwarjini da cikar haiba mutuncinsa ne. Miskilanci gadonsa ne. inba ita ɗin bama wake ganin murmushin kojin furucin bakinsa, dan babu abu mafi wahala da girma ga Tajwar Eshaan kamar magana. Dariya kam ko’ita a karan kanta zata iya rantsuwa bata taɓa gani ba tunda ba’a gabanta ya tashi ba, sai lokaci-lokaci suke zuwa su gansa.

Abincin ta haɗa masa a gabansa da kanta, babu musu kuwa ya amsa tausasan idanunsa na kallonta da jin ƙaunarta kamar kowane ɗa akan mahaifiyarsa. Tsahon mintuna yana tsakurar abincin cike da ƙasaita kamar wani magani, kafin ya ɗauka tissue ya goge bakinsa da janye jikinsa da ga kwanikan alamar ya ƙoshi..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button