Hausa Novels and Stories

Sanadin Zane 15-16

Sponsored links

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

 

 

______________

 

Duk inda yaso ya Gama duk wasu al’amuran da ya kawosa kasar nan gagara yayi dan sai 6pm Suka fito meeting shima ba ayi concluding ba an bukaci ya jira har architect ya fidda *zanen* building din da za a Masa Dan company yake son budewa,Rai ba Dadi dukda ba Wanda ya Isa yayi masa Dole suggestion Suka kawo shima yayi reasoning da shawaransu Haka aka maidashi masaukinsa

 

 

 

Ana bude masa ya Fara kokarin fita sai idanunsa ya sauka Kan painting din da aka bashi d’azu

 

Alama yayiwa guide dinsa da ya kwaso Masa

Ciki yayi Yana shiga direct bathroom ya fad’a ya shiga yin uzurinsa sai da ya Gama ne yayi wanka ya fito d’aure da farar towel da wata karama a wuyansa Yana tsane jikinsa

 

 

 

Zama yayi a stool ya Fara tsane jikinsa bayan ya Gama ne ya shafa cream tare da saka wata farar jallabiya da yayi mugun Masa kyau da alamu dai sallah zai fita yi massalaci Dan an kusa magrib

 

 

 

Turarensa me mugun kamshi ya fesa tuni kamshin ya cika ko Ina sanan ya d’au wayarsa ya fita

 

 

 

Ya tarar dukkanin aid dinsa na jiransa dan baya bari ko wannesu yayi missing jam’in balle yanzu da sai sunje nisa da hotel din dole su fita da wuri kar suyi missing jam’in wani babban massalaci Suka je Basu fito ba Saida akayi isha’i sanan Suka bar wurin suka bar mutane da mamaki wanene shi

Yana komawa hotel d’aki ya shiga ya zauna a bakin gado yana bin missedcalls din wayarsa

 

 

 

Wanda yayi saving da first wife ita ya Fara Kira kamar ko jira take ta d’auka da sauri dan sanin kanta ne in har tayi missing calls dinsa ba zai sake Kira ba Kuma ko ta Kira bazai d’auka ba

 

 

 

Cikin wani irin shagwab’abiyar muryar da takeyi Dan ganin ta birgesa tace”assalamualaiku”dan akidarsa ne Dole a amsa me Kira da sallama in ba Haka ba zai yanke wayar

 

 

 

Da k’yar Kamar bazai amsa ba Dan ya d’au kusan minti daya kafin yace”wa’alaikum mussalam ya kuke”

 

Cikin Jin Dadi jikinta har rawa yake tace”fine honey when are you coming back munyi kewarka”

Cikin takaita zance yace”same here ”

 

 

 

Tace”Kana dai lafiya ko ka ci abinci?”

 

 

 

Yace”Zan ci a gajiye nike ne”

 

 

 

Tace”but why baby nasan yanzu 8pm tayi a can ka daina Zama da yunwa you might……”

 

 

 

Be Bari ta karasawa ba yace”ok I have to go please sai gobe”

 

 

 

Jiki a sanyaye tace”good night ”

 

 

 

Ba tare da ya amsa ba ya yanke wayar da ya so Kira sauran missedcalleds din Amma sai ya fasa

 

 

 

Kira yayi Wanda tea ne kawai dan baya jin zai iya cin abinci me nauyi a wanan lokaci

 

 

 

Jawo art work din yayi ya bude,zaro Ido yayi ganin shine a gidan abinci Yana cin abinci sai ya shafa Yana mamakin how perfect the work is

D’ayan Kuma ya bala’in tafiya dashi ya jingina da gado Yana kallo ya kasa d’auke idanunshi even for a minute sai ya gan an rubuta _fannah_ besan lokacin da ya anbaci sunan ba ya Kuma shafa aikin

 

 

 

Koda aka kawo tea din kin ajiyewa yayi yasa aka ajiye me a table

 

 

 

Kusan awa ya d’auka Yana kallon painting me birgewa a ransa sai cewa yake wow

 

 

 

A fili ya furta this is amazing

 

 

 

Sai da ya Fara gyangyandi ya ajiye board din ya dan kishingid’a a hankali bacci ya Fara fisgarsa hakan yasa ya kwanta

 

 

 

Yana kwantawa ya Fara sana’ar tasa watoh mafalkai mafalkai wanan karon kuwa yaki ake a kasarsa duk an Gama da mutanensa har ya fidda tsammani zasuyi nasara zaiyi saradan sai ga wata irin Guguwa a filin yaki…..sai ya Fara Jin takun doki kallon direction din yayi sai ya hango wani na zuwa da gudu

Tana fadin hakan ta turesa sanan ta bar wurin

 

 

 

Bude Ido yayi a firgice Yana numfashi sai ya mutsika Ido ya jingina da gado Yana tunanin matsalansa watoh rashin haihuwa,a ce Yana da Mata har uku Amma Babu wacce ta tab’a b’atar wata he don’t want to believe labarin da mahaifinsa ya basa na sirikar wanan muguwar matan da ya d’auketa tamkar uwa Amma tayi sanadin mutuwa mahaifiyarsa meyasa zata Masa haka’ and on top of that a ce sirikarta ta Zo har gida tayi amfani da maita wajen ganin ta hargitse masarautar Wanda da be yarda ba but gradually ya Fara yarda da maganar mutune Dan a cewar mutane tunda tayi musu Baki masarautar gaba daya ta rasa natsuwarta shi ya zaga asibitoci ana cewa lafiyarsa kalau Amma matansa ko b’atan wata Basu tab’ayi ba

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button